*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more**SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*6*
Yana cikin duniyar tunanin sa bai san lokacin da ya ce da ita
"You look cute"ba,kawai sai ta dakata da dariyar ta natsu amma da ragowar murmushi a kan fuskar ta wanda hakan ya saka shi gano cewa abin na yawo a kan ta still.
Toh amma menene na dariyar?koh dan ya kira Asma'u da budurwar sa shi yasa take ta mai dariya?but ai Asma'u kyakyawar yarinya ce bata da aibu.shi fah ba sani yayi cewa Asma'u na da saurayi mai siffar ƴan daba ba shi yasa ya fara dulmiyawa but nevertheless zai tsawatar wa baby doctor akan me za ta na yi wa budurwar sa dariya dan haka ya ce"In kin gama dariyar ki zo mu tafi yamma na yi kuma yanayin ruwa ne".kaiwa nan ya fara tafiya yayin da ita kuma ta biyo shi a baya suna tafiya yana riƙe da kayan da suka raba ya rage wanda yawan jama'an yau har ya ɗare na jiya dan haka sun ɗau lokaci sama da na jiya.
Suna tsaka da tafiyar su ta kurame kawai sai ta kuma sakin dariya sai yi take kamar ta sami abin arziƙi abin harzuƙa shi yayi dan haka ya tsaya ka kalle ta kafin ya mata wata muguwar tsawa.
"What the heck are you laughing at huh"?shiru ta yi ta haɗe rai kafin ta ce
"Excuse me Dr Zaid Maher baka da right din ɗaga min murya dan na yi dariyar abin da bai fice min a kai na ba laifin waye?kai fah ka faɗa min cewa wannan ballagazar ita ce budurwar ka yarinyar da babu tsari babu tarbiya a tattare da ita kai ka sani haka kuma kana gani da idanun ka bata da tsarin da za'a ce ta kai standard ɗin zama budurwar doctor ba doctorn ma kamar kai mai girman kan tsiya da iyayi,iya nan jijji da kan ka ya dakata ashe?dan haka ni ba laifi na bane dan na yi dariya dan abin na dariya ne mana ta yaya zaka ce da yarinyar nan wai budurwar ka kai tsaye,ai kowa ma dole yayi dariyar wannan abin". Tana isa nan ta yi gaba ta wuce shi shi kuma ya tsaya nazarin kalaman ta dan akwai ƙamshin gaskiya a ciki shi kan shi ya kasa ganewa da tantance dalili ƙwara guda da yasa ya ke jin kamar akwai wani al'amari da ke son faruwa da shi game da yarinyar wato Asma'u kenan but ko ma dai menene he don't think Bilkisu should give that bad impression to Asma'u dan ba dan ita ba da an shafe tarihin sa a doron ƙasa ƙila dan bata san da haka bane shi yasa but zai gyara mata tunanin ta akan Asma'u.
Shi kaɗan shi yake wannana analysis ɗin har dai ya kamo ta dan dama ba wani sauri take yi ba har suka shiga taxi suka kai madakatar su babu wanda ya kuma cewa kanzil da suka fito ta riga shi shiga cikin gidan yana maganar zuci ya ƙarasa ciki shima a inda yake cewa
"Ƙarfin halin yarinyar nan yawa gare shi ita ce da laifi kuma ita ce da fushi"ya cigaba da tafiyar sa har ya kai masaukin sa inda ya yi wanka ya chanzo zuwa ƙananan kaya zuwa lokacin an kawo mai abinci ya ci ya fita abin shi ko ina zai tafi.Ita kuwa da ta shiga ciki dariya ta tuntsire da dan abin gaskiya ya shammace ta ace mutum da izza da iyayi amma ya ɓige da son wannan fanɗararriyar yarinya kuma yana mafarkin mahaifiyar sa zata lamunci wannan shirmen tasa.
Har ta gama cin abinci tana alhinin wannan abin yayin da zulfa'u ke tambayar ta dalili sai ta ɓoye mata saboda yadda suke respecting Dr Zaid ba zai kyautu ta faɗi abin kunyar da ya ke yi ba dan mutuncin sa ne zai zube wanda hakan ba zai kyautu ba sai ta ce da ita wata mata ce ta ke sanar da ita wai akan mijin ta zai ƙara aure ita kuma ji take kamar ta yi hauka dan haka wai baby doctor ta taimaka mata su je gidan su yarinyar ta sanar da su cewa ta gwada mijin kuma ta tabbatar da cewa yana ɗauke da cutar zamani,kuma a zahirin an yi hakan but sai ta lauya wa zulfa'u instead ta sanar da ita ainihin maganar sai ta chanza,
Itama dariyar abin ta yi dan matan su akwai duhun kai haka halayyar su take duk baƙon da ya zo sai an gwada mai ƴar hali..

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...