Page 17

1.5K 115 17
                                    

*⚜BWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

*Explore*

   *17*

  At first da ta shiga ɗakin zuba mai idanu tayi sai daga baya ta zauna ta cigaba da kallon sa azimun babu shakka so take ta fitar da wani abu daga fuskar sa sai dai hakan bai samu ba dan ɓata lokaci tayi tana kallon sa bata san time ya tafi ba sai da ta ji gyaran murya sai tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta faɗa,.
  Ammi ce ta shigo ɗakin dan tuntuni take kallon ta ta transparent glass door dake ɗakin nazarin ta take yi shi yasa bata yi interrupting mata analysis ba har sai da ta ga kamar kan ta zai buga dan dagewa tayi tana kallon sa tana ta wasu abubuwa masu kama da analysis.
Kunya ne ya kama ta Ammi caught her again oh no sai ta fara inda inda tun ma kafin Ammin tayi magana wanda ya saka Ammi fitar da dariyar ta fili dan kasa riƙe sa tayi,
  "Wait Bilkisu,wa ya saka ki a gaba akan sai kin yi explaining dalilin ki na shigowa ganin Zaid?i guess babu right?common dear is a natural feeling feel free and express your feelings is not a crime rather is it a sin,open your eyes and heart,learn to accommodate the stranger in your heart,ki daina ɓoye abin da kike ji game da Zaid,Bilkisu da a ce ban hango wannan abin ba,da a ce ban ga tsantsar so da kike yiwa Zaid ba wallahi tallahi ko da shi Zaid ɗin ne ke son ki amma ke baki son sa toh wallahi ba zan taɓa yarda ya aure ki ba ko da hakan na nufin threat ne ma rayuwar sa dan haka baby,ki amince da abin da zuciyar ki ke faɗa maki"ta ƙarasa maganar tana mai daga kafaɗun ta.
  Ko uhum bata ce ba sai ta fita abin ta dan waɗannan maganganu da Ammi ta mata kamar watsa mata garwashi tayi saboda yadda take rera kalaman ta sai suka rinƙa taso mata da tunanin Asma'u dan ita kaɗai ta san ya take ji a ran ta a duk sanda ta tuna da Asma'u ta kuma tuna da abin da ya faru da su abin ba ƙaramin rura mata wutar ƙiyayyar yarinyar yake ba shi wanda ya aikata abin ma bata jin haushin sa kamar yadda take jin haushin yarinyar  kuma all she can see and say shine Zaid is blindly in love with that villager what if he regain consciousness and decided not to make her his Mrs?what if he develops love for that strange girl and not her?what if he hates her after knowing that she is his wife and life partner?ya salam sai ta zauna  tana tunanin mafita gashi su Hajiya Zeenat basu riga sun yi landing ba bare ta kira ta ta sanar da ita abin da ke gudana.
  Throughout ranar babu wani kuzari ko walwala a tattare da ita iya tayi sallah ta ci abinci ta sha magani sai kwanciya amma baccin ma ba zuwa yake yi ba saboda tsananin damuwa da ta sakawa kan ta duk brain ɗin ta ya ɗau chaji ta rasa menene abin nan da ya ke mata ƙatutu a ƙirjin ta babu damar ta ji sunan Zaid sai gaban ta ya faɗi hatta ita kanta in zata yi yunƙurin kirab sunan sa sai ta yi da gaske if nit kasa furtawa take,toh me hakan ke nufi?wannan tambayar ta tsaya mata a rai sosai duk ta kasa shikir but she knows that damuwar ta zai ƙare da zarar ta yi magana da Umman ta.
  A haka Bahajjatu ta same ta sai ta kira sunan ta yayin da take ƙoƙarin zama
"Beelove"amsa mata tayi ta ce
   "Na'am Baha"sai ta tashi ta zauna tana son gaya mata wani abin but bata san yadda zata fahimci maganar ba but she have to say it
"Baha ni ko na ce me zai hana a yiwa Zaid gyaran fuska he is going out of his usual appearance kuma kamar ba wanda ya shirya gyara shi haka za'a cigaba da kallon sa dan baya cikin hayyacin sa"?tsayawa kallon ta Bahajjatu tayi dan ta bata mamaki wato har lura take da yanayin fuskar sa tsabagen so da ya matu mahaukacin kamu but she doesn't wanna admit it sai ta ce
  "Toh ke in banda abin ki beelove ai ina ga since babu wanda ya lura da hakan sai ke why not ki tafi ki mai gyaran fuskar coz na ga yanzu ba lafiya kike nema ba dan kin ji sauƙi already sai dai ki yi jinyar marar lafiya and i guess babu zunubi dan mata ta gyara mijin ta for her own satisfactory purpose right"??da teasing tune ta kammala maganar wanda ya sa Bilkisu jefar ta da ƙaramar pillow da aka yi beautifying gadon da shi,gudu tayi tana dariya ita kuma ta ɓata fuska a dole an laƙaba mata abin da bata lamunta da shi ba sai ta ce
"Amma dai kin san ban son wannan abin ko Baha?zamu fah ɓata ta yaya zaki rinƙa kiran min matsayin da ban kai ba a ina na zamo matar Zaid stop it please before some could hear you so annoying"!!ta ƙarasa kamar wata ƙaramar yarinyar da ke shirin sakin kuka sai kawai Bahajjatu ta cigaba da dariyar ta kafin ta dawo kusa da ita ta zauna ta ce
  "Babes,ba fah laifi bane dan kin yarda da abin da kike ji game da yaya na,wallahi kin ji rantsuwar musulm,yau da ace wata ce ba ke ba ta ke ƙaryata feelings ɗin ta akan yaya na toh Allah ban bin ta kanta sai dai ma in daɗa dulmiya ta ta amince akan bata son sa but ke Bilkisu both our parents have agreed to this wedding dan sun san alkhairi ne cike a cikin ta abin da suka hango mu bamu hango ba kuma baki san wani abu ba,kin ga yaya na da kike gani wallahi bai da matsala bai da damuwa ko kaɗan hasalima he is a free person very gentile and kind kawai borin fuskar sa kike gani har kike ɗaukar hakan a matsayin halin sa ne but i will tell you a little secret about my brother"sai ta zama serious haɗe da chanza fuskar alamun maganar da zata faɗa ɗin babba ce mai muhimmanci sai itama Bilkisun ta maida hankalin ta gabaɗaya kan aminiyar tata dan jin me zata sanar da ita
  "My brother happens to be the most quit caring and gentile out of all my brothers shi kaɗai ne mai hanƙuri da juriyar duk wasu abubuwan da ke tasowa,bai taɓa son wata ba kuma babu macen da ta taɓa gigin kusanto sa da sunan so ko da kuwa tana son sa ne he is committed to his duties abu ɗaya da ya tsaya mai a rai kuma yake damun sa shine akwai wata yarinya da ya taɓa gaya min cewa yana da wani feelings akan ta wanda bai sani ba so ne kokuma shaƙuwa ce bai sani ba amma ya san in har ya ga yarinyar yakan ji wani abu game da ita is somehow mix bai iya tantance menene kuma ya kasa sanar da kowa ya barwa kansa shi kaɗai sai ni da yayi min bayanin kaɗan i guess that girl is the Asma'u girl in that village,wani abin da ya sa na ƙara yarda cewa ba son yarinyar yake ba illah shaƙuwa da tausaya mata da yake yi shine sai da ya gargaɗe ni akan maganar kar ta wuce tsakanin mu mu biyu saboda ya san in har Ammi ta ji toh Allah ne kawai zai taimake shi daga hannun ta dan fushi zata yi da shi and yiu know what?ko da wasa bai taɓa yin maganar da Ammi ba kenan ba son yarinyar yake ba dan da son ta yake toh babu wani abin da zai saka shi jin shakkar nunawa duniya ma budurwar sa har Ammi zai nuna mata but no he is not comfortable with that decision so you see in har yaya bai san matsayin yarinyar nan a rayuwar sa ba i don't think you should play with this opportunity for making him yours kin fah san a family ɗin mu namiji mace ɗaya ya ke rayuwar sa da,which is equivalent to having a single life partner in kuwa ya auri yarinyar nan shikenan ya rasa damar auren ki and our parents dream is for the two of you to get married and leave a happy life wanda nake fatan kafin ya farka ki zamo matar sa because i don't want him to marry that village girl dan bai san abin da yake so ba har yanzu bai san menene taste ɗin sa ba marrying that girl will shatter all his dreams away saboda yaya na ɗan soyayya ne yana son yin rayuwar soyayya ba kaɗan ba da matar da zai aure wanda ko da na duba sai na ga kuna a page ɗaya da juna dan kema ƴar son soyayya ce but kin rasa da wa zaki yi rayuwar soyayyar yadda kika daɗe kina mafarki,Aslam was never your dream guy ni na san ba kya son sa kuma in har kika zuba mai ido yana iya tura iyayen sa su tafi gida a yi maganar auren ku because yadda yake yin abu is like irin kin amince mai ɗin nan ne dan haka Abba might not think twice sai ya amimce though na san shima yana son auren ku da yaya na but he won't force you in ya tambaye ki kika ce mai a'a ba ki son yaya na yana iya barin ki ki zaɓi wanda kike so wanda a gare ni hakan babban asara ne dan i want our friendship to go beyond this so please Bilkisu ki natsu ki duba wannan maganar da na gaya maki ki kuma yi la'akari da future ɗin ki kafin ki zaɓi life partner ba wai kamun ƙafa nake yiwa yaya na ba a'a am here acting like a sister to you saboda na san Umma zaki faɗawa damuwar ki but ba lallai bane ta feɗe maki komai akan rayuwar ki ba kamar yadda ni zan sanar da ke ba just think about our conversation before you make the decision humm"?girgiza mata kai ta yi dan bata sani ba sai yanzu da aka sanar da ita,a yanzu take jin kamar tana da wani abu a ran ta wanda bata tsammanin zata iya sharing nasa da kowa sai mutum ɗaya who could he be?is it Zaid?did she love him kamar yadda ake faɗa?yin wannan tunani na ƙarshe ya sa ta ɗago idanun ta ta ɗora su kan Bahajjatu sai ta kasa furta komai illah kallon da take bin ta da shi daga bisani ta numfasa ta ce
  "Nagode Baha nagode da shawarwarin da kika bani nagode da kulawar ki gare ni indeed you are a friend and a sister to me a da na yi yunƙurin sanar da Umma danuwa ta saboda Ammi 48hours ta bani dan yanke shawarar maganar da muka yi da ita but you coming at the appropriate time da nake cikin buƙatar shawarar wani ya saka ni jin kai na as the most luckiest kuma inshaAllah i will follow my heart because i was a witness akan maganar Zaid da Asma'u,ko ba komai i don't think i will allow her to marry him koda ban aure sa ba bana jin zan iya zuba ido in kalle sa yana auren yarinyar da ta so ganin bayan sa dan da ita aka mai wannan abin Baha ita ta nuna wa Mudan hanyar da muka bi har suka biyo mu suka mai wannan abin sannan kina tsammani zan kyale ta ta aure sa??i can't i just can't bear to see him leaving with that hippocrate chameleon she is a deceiver he trusted and believe in her but she went right behind his back and stabbed him kina ganin wannan ta cancanci zama abokiyar rayuwar Zaid?ko ba'a faɗa ba yarinyar da bata da tsarin nan za'a bar sa ya aura"?kukan da ya taso mata ne ta fito da shi dan abin na ƙona mata rai sosai.

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDDonde viven las historias. Descúbrelo ahora