Page 21

1.7K 125 8
                                    

BWA

{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
     {the love saga}

#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and more

  SIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim

  *21*

  Fincike hannun sa yayi daga nata da suka shiga ɗakin ya na mazurai maganar dai bai yi ba ita kuma bata fasa haɗe fuskar da ta ke yi ba.zama yayi yana nazarin ta but me yasa take mai haka?ɗazu da safen nan ta zo ta hau nurse da faɗa ta kirawo wata kafin su fita dan ta bashi magani amma ta hau matar da faɗa and now....this nice woman Ms Mcsantos again tana gaya mata and she is comfortably saying basu buƙatar compliments ɗin ta again she claims to be he spouse why is she doing all these?babu wata wata ya shiga buɗe mata wuta

  "Bilkisu wacece ke da har zan rinƙa mu'ammala da mutani kina son datsewa?wacece ke da har zaki rinƙa underestimating min dignity a gaban jama'a kai tsaye?ko dan kin ga na sake miki fuska ina maki shiru ne ya sa kike ɗauk na for granted?saboda kin ga ina binki da kallo bana maki magana ya sa kike kallo na kamar wawa?ko dan kin ga am hospitalized shi yasa kike mim kallon rascal?tell me me dalilin ki na min shishigi"?da ɓacin rai ya ƙarasa maganar dan shi bai ga dalilin da zai sa ta raina sa ba ko da kuwa saboda disability ɗin sa ne na rashin lafiyar da ya ke ciki.

  Cikin halin ko in kula cikin halin damuwar ka ne wannan ta kalle sa ido cikin ido ta ce
  "Ni ban hanaka mu'ammala da mutani ba da mata na hanaka matan ma matan turawa da baka san su ba baka haɗa wata alaƙar jini da su da su nake hanaka mu'ammala dan ubangiji ma bai lamunce maka da yin mu'ammala da wanda ba muharramin ka ba ciki kuwa har da waɗannan masu fuskar shanun dan ita ɗin ai ba muharramar ka bace arniya ce tana iya jan ra'ayin ka you mever can tell ka ga ka aikata laifi babba dan sai da aka ce 'La taƙrabul zina' kar ku kusanci zina and that woman...that os exactly what she is trying to induce you to do using her child as her entry point ni kuma ba zan so Allah yayi fushi da kai ba ka ga ai ban da laifi dan na taya ka kuɓutar da kanka daga shiga kaifin arniyar baturiya.sannan ni bana underestimating maka dignity ina ma rising maka dignity ne dan duk responsible man in ya kalle ka ya san kai ɗin ɗan gidan masu hankali ne zai ji takaicin ganin ka kana zubda mutuncin ka a bainar jama'a shi yasa na hanaka cigaba da hirar da kake yi da matar kuma ni bana ɗaukar ka for granted kawai dan ina tausaya maka ne shi yasa nake hana ka mu'ammala da matan turawa haka zalika ni bama ɗaukan ka a wawa dan kai ɗin miji nane akan me zan maka kallon wawa,kuma ni ma nan ai i was hospitalized kuma har yanzu ban gama warwarewa ba dan haka in saboda in har dan baka da lafiya ne ya sa kaje ganin kamar ina ɗaukar ka a rascal then nima maybe haka kake kallo na dan nima ai patient ce finally ba shishigi nake maka ba as a responsible wife haƙƙi nane kare ka daga faɗawa a cikin ko wani irin sharri ko halaka dan haka you owe me no explanation"...

  Kamar an dasa sa a wun haka ya koma bai yi tsammanin zata bashi amsoshi daki daki kamar yadda ta bashi yanzu ba dama ta iya gasa magana haka ne ko dai dan shi ne da ta raina??. 

  Ko a jikin ta ta yi kamar zata durƙusa ta cire mai takalmin sa sai kuma ta fasa ta tashi tana mai kallon ƙur idanun ta na nuna alamun wani gagarumin magana
"You know what??just undress yourself i guess you are now physical and mentally fit....goodbye Dr Zaid Maher"...daga haka ta juya a zuciye tayi tafiyar ta lo waigo sa bata yi ba ita fah danne zuciyar ta take yi da attitude ɗin da yake bata haka kawai tana kan nemawa kan ta lafiya kawai dan tana tausaya mai sai ya rinƙa mata wani gani gani dan ma ya gode su Ammi da Umma sun yi convincing nata kan ta aure sa if not me ma zata yi da shi...

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now