Page 23

2K 122 25
                                    

BWA

{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}

👄 °°° °°°👄
°°
°

🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
{the love saga}

#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and more

SIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim

23

Sai wuraren 8:40pm suka iso gida already sun tsaya a Nature Reserve sun gabatar da sallar zuhur da asir dan haka da dawowar su kowa ɗakin sa ya nufa ya yi freshen up suka gabatar da sallar magrib da isha'i daga haka suka fito falon cikin shigar kayan barci nata coffee colour mai ƙyalli na sa red colour mai laushi duk da takalman su ita ta saka gyale ta yane kan ta shi kuma ya fito da wayar sa a hannu yana latsawa kamar dai waya yake son yi da wani ko wata.
Kusan a tare suka fito dan jubilation ɗin da suka yi yau ya saka su deciding cin abincin dinner tare a falon shi yasa ma suka bar abincin a falon.
Saman centre carpet da ke shimfiɗe a falon suka zauna yayin da ya ajiye wayar sa a gefen su.
Shi ya buɗe well packaged pack ɗin ya yi unwrapping foil papers da ke lulluɓe da wasu abin ciye ciye,a gaban ta ya baje mata nata haɗe da miƙo mata spoons da ke nanaɗe a cikin toiletry yana mai ce da ita
"Bismillah"!ɗan murmushi tayi sannan ta amshi spoons ɗin ta buɗe bata wani tsaya jiran sa ba tayi bismillah ta fara cin abincin,shima sai ya fara ci.
Sun yi maintaining good table manner babu magana har sai da suka kammala sannan tayi clearing wurin shi kuma yana zaune ya ɗau remote yayi booting plasma dake falon.
Kafin ta dawo daga disposing dirt ɗin already ya hakimce saman kujerar yana kallon wani program na shirin doctors suna surgery an kai tsakiyar shirin dan bai ƙunna da wuri ba.
Har zata wuce ta ma buɗe baki da niyar ce mai sai da safe sai ta ga abin da yake kallo,abu nasu maganin a kwaɓe su sai ta dawo da baya ta zauna kan ɗaya kujerar dake fuskantar nasa dama a tsakiya plasma ɗin yake sai kujerun a gefe da gefe.
Ko da ya ga ta dawo ta zauna sai ya kalle ta ya ce
"Ba zaki yi bacci bane?aren't you tired"??kallon sa tayi kamar ba tare suka yi yawon ba after all shi ke buƙatar hutun ba ita ba dan shine marar lafiya kuma gobe suna da zuwa asibiti wun doctor saboda zai fara checkup ɗin sa.
Da murmushi shimfiɗe kan fuskar ta ta ce
"No..not at all...in fact,kai ya kamata a ce mawa ya huta,dan gobe zamu fara zuwa checkup"!!sai a nan ya haɗa ido da ita dan she speak to him so nicely ga tausaya a muryar ta yayin da tale maganar.
Glance yayi sai ya gyaɗa kai ya cigaba da kallon kamar yadda itama ta mayar da hankalin ta kan plasma ɗin suka cigaba da kallon.

Basu bar falon ba sai da suka ga abin da ya turewa buzu naɗi dan a idon su aka yi suturing komai aka gyare patient ɗin kafin a tafi short break wanda yayi daidai da ƙarfe goma shaɗaya da mintuna hamsin da biyar.
Kashe tv yayi ya juyo gare ta ya ce da ita
"Sai da safe"itama ta ce mai sai da safen,kowa yayi ɗakin sa dan barci ne cunkushe a idanun su kawai son ganin ƙarshen theater ɗin suke son yi shi yasa basu kwanta ba.
Da baya ta kwanta a kan gadon tana mai lumshe idanun ta sai hamma take ta yi akai akai tana son tambayar sa hotunan da suka yi ɗazu but barci ya hana ta sai kawai ta bari akan washegari zata tambaye sa kafin su tafi asibitin.
Babu jimawa bacci yayi gaba da ita ai kuwa a yadda ta kwantan nan a haka tayi baccin hankali kwance ta ke baccin ko ƙofar ɗakin bata ƙulle ba iya turawa tayi ta bar shi a hakan..

A nasa ɓangaren ma kusan hakan ne ya kasance dan bayan ya shiga ya kwanta sai ya janyo wayar sa da nufin saka alarm dan so yake ya riga ta tashi dan tun da aka yi hospitalizing na sa bai dawo daidai ko ba sallar dare ba kasafai yake tashi yin ta ba hakan kuwa ya samo asali ne a sakamakon effect na maganin yamma da yake sha a kullum again ear device ɗin da ke sagale a kunnen sa ya taimaka wun saka shi yin bacci har fiye da misali dan sosai device ɗin ke taimaka mai wun rage jin sauti sai ya ke saminbacci sosai wanda hakan ke shagalar da shi.

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now