⚜BWA
{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}
👄 °°° °°°👄
°°
°🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
{the love saga}#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
#Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and moreSIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim
32
Wacce suka gani a bakin ƙofar ne ya saka su baki ɗayan su sauke ajiyar zuciya cikin tsoro da fargabar ta shigo a ƙurarren lokaci lokacin da bai dace ba ta yi saurin duƙar da kan ta ƙasa tana faɗin
"Ki gafarce ni Hajiya wallahi ban san komai ba kawai shigowa nayi na ɗauka ke kaɗai ce a ɗakin shi yasa na shigo kai tsaye ki min afuwa ranka ya daɗe ka min haƙuri ba da niya ko manufa na shigo maku haka nan ba"sauke numfashi Bilkisu tayi tana kallon matar nan sai ta ce da ita
"Ba komai ajiye abincin ki tafi"jiki na ɓari ta ajiye kamar ana tsungulin tatayi gaba har da tuntuɓi dan ganin laifin kan ta ta shiga gani da ta nace da yin sallama da bata shigar masu ɗaki haka ba..
Tana saukowa Hajiya Zeenat dake zaune saman two seaters hannun ta riƙe da tablet tana yin transaction ta hango Alawiyya dake saukowa suƙuƙui kamar mai cuta sai ta ɗan karance ta kaɗan tana nazarin me kuma ya kai ta ɗakin Bilkisu dan ta direction ɗin ɗakin ta fito sai dai yanayin ta na nuni da wani abin ba daidai bane.
Har ta gifta zata tafi kitchen Hajiya Zeenat ta kira sunan ta
"Alawiyya zo nan"a firgice ta juyo duk tunanin ta baby doctor zata balbale ta ne dan ta kutsa mata kai cikin ɗaki ba tare da ta bata izini ba but luckily enough for her tana juyowa ta ga uwar gidan ta ne sai ta sauke ajiyar zuciya ta dawo da baya tana faɗin
"Wallahi hajiya har kin saka ni jin tsinkewar gaba,duk tunani na hajiya ƙarama ce"jin haka sai Hajiya Zeenat ta gane zargin ta ya zamo gaskiya kenan sai ta gyara zama tana mai kallon Alawiyya da kyau
"Ke ban son shirme gaya min,me ya faru da hajiya ƙaramar"??ta tsare ta da ido dan kar ma ta sami damar lauya maganar sai ta shiga inda inda kamar marar gaskiya sai da Hajiya Zeenat ta tsawatar mata sannan ta natsu tayi mata bayani
"Hajiya,abincin Hajiya ƙarama na kai mata ɗakin ta na duba ta can balcony bata nan sai na yi sallama ban ji amshi ba sai kawai na shige kai tsaye dan nayi tsammanin baccin ta koma yi saboda lokacin da ta kira ni tace in zo in kawo mata abinci daga bacci ta tashi,toh Hajiya in gaya maki ina tura ƙofar ban fah lura ba na saka kai na shige da niyar in ma baccin take sai in zo in maki magana a tashe ta baccin yayi yawa haka nan amma abin kunyar da na janyowa kaina ya sa na kasa faɗin komai Hajiya"sai kuma tayi shiru alhalin Hajiya Zeenat ta kasa kunne tana jiran jin zance amma Alawiyya tayi shiru.
Ɓata fuska Hajiya Zeenat tayi dan tasan halin Alawiyya ita ɗin yarinya ce mai kawaici da rashin son gulmace gulmace shi ya sa nasu yazo ɗaya da Hajiya Zeenat ɗin.
"Kina ƙarasa gaya min ne ko kuma in bar ki har Hajiya ƙaramar ta zo ta isko ki da bala'in ta"?ai jin wannan sai ta ce
"Haba Hajiya a yi haka,a'ah bari dai in gaya maki,,kin ga da na shiga ɗakin sai na gan ta tare da shi mai gidan nata a tsaye kamar dai ma magana mai muhimmanci suke yi da juna shiga ta ce ta katse masu maganar da suke yi,wallahi Hajiya duk kunya na ji ga tsoro na hana su ƙarasa maganar su sam ba da wata manufa nayi hakan ba wallahi abinc...."nata bar ta ta kai ayar zancen ba dan ta sami abin da take son ji dan haka ta dakatar da ita ta hanyar ce mata
"Is okey ya isa haka nan tafi abin ki zan yiwa Bilkisun magana dan kar tayi fushi"har ƙasa ta duƙa tana ma Hajiya Zeenat godiya kafin ta tashi ta bar wurin.
Bin ta da kallo Hajiya Zeenat tayi kamar ita ce Bilkisun har ta ɓace sannan ta dawo da idanun ta saman tablet dake hannun ta tana girgiza kai at the same time tana murmushi ita kaɗai...
Dama sai da Hajiya Madina ta yi maganar nan ta ce mata da miji duk borin da zasu yi ba lallai bane mu san lokacin da zasu shirya ba hakan kuwa gaskiya ne dan gashi tun ba'a kai ko ina ba da tigimar har an fara siɗaɗewa ana zuwa ganin juna a ɓoye.
Murmushi mai ƙayatarwa tayi tana jijjiga ƙafar ta dan abin nasu yanzu dariya yake bata kamar dama wani ne ya ce da su suyi faɗar da suka yi..
"Allah ka ƙara haɗa mana kawunan ƴaƴan nan namu ka basu zaman lafiya da fahimtar juna dan suna lacking fahimta a zaman nasu..
Gyara ƙafar ta tayi bisa kujerar tayi positioning tablet ɗin tana murmushi sai ga fuskar Hajiya Madina yayi appearing a screen.
"Kai aminiya ya naga annuri ne bisa fuskar ki ko dai yarinyar nan ciki ne da ita"??dariya cikin ƙasaita Hajiya Zeenat tayi tana faɗin
"Ko ɗaya wallahi ai mu da ganin ranar ɗaukar cikin nan sai dai mun gani"da amusement Hajiya Madina ta ce
"Kina nufin me kenan"cikin halin ko oho ta ce
"Ai shekaranjiya yaran nan suka haɗe humm"abin ita kanta da take faɗa ya bata mamaki bare Hajiya Madina da ke sauraron ta sai ta ce
"Bilkisun ce ta sanar da ke"?girgiza kai tayi ta ce
"Ina fah zata faɗi gaskiya,ai ta san bata da gaskiyar ne tsabar hauka ne da rashin tunani ya sa ta yi abin da tayi"saurin katse ta Hajiya Madina tayi tana jujjuya mata yatsa ta ce.
"ia mu ne marasa gaskiya Hajiya Zeenat"da mamaki ta ce
"Mu kuma"?gyaɗa mata kai tayi kafin ta ce
"Can you imagine,bamu fah tsaya mun saurari ainihin dalilin yarinyar nan ba fah kawai muka ɗau mataki kenan in har a daren washegarin dawowar su ne suka sami matsalar nan kamar yadda ta faɗa to lallai akwai ɓoyayyen lamari dan ban ga alamar rashin jituwa ba a tsakanin su saman fuskar Zaid da safen nan ba dan ya shigo gaida ni har ya so yayi min maganar matsalar amma na kauce mai ban bari yayi ba,dole zalintar yarinyar nan yayi i just pray ba fin ƙarfin ta yayi ba ta ga ba zata iya zama da shi ba again ya kuma ƙara mata takaicin maganar wata ba a daren farkon su ba dan har in dai wannan ne dalili then i must say Zaid bai da hankali"ran ta a ɗan ɓace ta ida maganar sai Hajiya Zeenat ta ce mata
"Ni kam duk ba blame games ɗin nan ba wannan damuwar su ne amma ki sani yanzu da haka right now,,Zaid na gidan nan chan ɗakin ita Bilkisun"!!mamaki ƙarara saman fuskar Hajiya Madina ta ce
"Ban gane ba aminiya"darawa Hajiya Zeenat tayi kafin ta amsa mata
"Yanzu kuwa zaki gane"nan ta sanar da ita exactly abin da Alawiyya ta sanar da ita.
Wani shewa suka yi sai Hajiya Madina ta ce
"Bana kusa da ke da mun tafa,ai dama na gaya maki duk borin da zasu yi mata da miji ne matsalar sai in har basu san junan su ba amma matuƙar suka sani toh fah ba faɗa ba ko yaƙi suka yi zasu dawo su liƙe ne yanzu ke da ke gidan kin ma san lokacin da Zaid ɗin ya shigo maki gida"!?girgiza kai Hajiya Zeenat tayi tana mamakin ƴaƴan nasu
"Kin gani,dan haka ƙala kar ki ce da su su gama sulhunta kan su su gyara babu ruwan mu ciki but kafin nan ya aka yi kika san abin da ya faru wa ya sanar da ke"?murmushi tayi ta ce mata
"Zainab matar Jamil"cikin son jin labari ta ce
"Gaya min mana"tas ta mayar mata da zancen ta ɗora da
"Sam ni ban yi tsammanin kishin Bilkisu ya kai har haka ba duk fah ta haukace da yawa"..gyaɗa kai Hajiya Madina tayi ta ce
"Manta su kishi ai haƙƙun ne dan tayi kishin sa ba laifi bane but mu dai zuba masu ido what goes around comes around"murmushi Hajiya Zeenat tayi sai ta ce
"Wai fah tare suke ni abin ma har yanzu dariya yake bani ki ga fah yadda yarinyar ta ta zaƙe ita fah sam babu ita ba u shi but ko me ya canza ta"da dariya ta gama maganar wanda har sai da Hajiya Madina ta taya ta dariyar
"Ai bar su kawai zasu gane kuren su mu suke son rainawa hankali su mai da mu ƙananan mutani"dariya suka kuma yi kafin daga bisani suka yi sallama.har suka gama wayar nan mamakin Bilkisu da Zaid bai bar ta ba...
YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...