⚜BWA
{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}
👄 °°° °°°👄
°°
°🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
{the love saga}#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
#Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and moreSIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim
27
Rage
"Bilkisu idon ki biyu"?cikin gajiya ta amsa mai da
"Uhmmm"!!shafo suman ta yayi cikin son kwantar mata da hankali sai ya kuma cewa
"Kin gaji ne"?a zuciyar ta ta ce..
"Ikon Allah wani irin tambaya ne wannan"amma a zahiri sai ta gyaɗa mai kai kawai dan ita ta san irin gajiyar da ya sauke mata amma bata son nuna gazawar ta a gaban sa dan nuna gazawar mace a fannin zamantakewar aure musamman abin da ya shafi shimfiɗar miji,baya ba ma mijin wani impression da ya wuce ita ɗin raguwa ce,.shi yasa ta jure duk azababben raɗaɗin da ta ji a sa'ilin da ya ke tarawa da ita sannan take ƙoƙarin kawar da gajiyar ta a yanzu da suke kwance tare dan kar ya ga gazawar ta
Bata bashi amsar tambayar sa ba sai ta ɗago ta ɗora haɓar ta saman ƙirjin sa tana kallon sa cikin magagain son sa da yake fizgar ta ta ce
"Nima ban sani ba"ɗan smirking yayi haɗe da jan hancin ta kaɗan ya matso da fuskar sa kusa da nasa ya haɗe hancin su wuri ɗaya yana rubbing da nasa hancin,lumshe idanun ta tayi tana ƙara manna ƙirjin ta a jikin sa.
"Kamar ban ga alamun gajiya tattare da ke ba"ɗago kan ta tayi for the second time ta kalle sa sai ta kai mai bugu a ƙirjin sa da hannun ta haɗe da kwantar da kanta again ta share sa sai ya riƙo hannun nata cikin nasa hannun yana ɗan murmushi kaɗan dan ya san ko ba'a faɗa ba Bilkisu mace ce kuma jaruma mai juriya da ba kowace mace bace zata iya ɗaukar sa ba kai tsaye haka ba tare da ta yi gardama ba ko janjani ba haƙiƙa wannan ita ce mace da ta amsa sunan ta mace..
Cikin sanyim murya ta ce mai
"Gobe zamu koma gida and...."sai tayi shiru cikin son ƙure ta ya ce
"And what.."??abin sai ya bata kunya sai ta ƙyale sa tana nan kwance har sai da ya leƙo fuskar ta dan ya ɗauka bacci tayi sai ya ji tana wasa da hannun ta saman ƙirjin sa alamun dai ba baccin take ba.
Shiru yayi yana observing nata har tsawon lokaci babu abin da ke fita a ɗakin shiru kamar babu leaving creatures sai ya kuma shafo suman ta ya ce
"Kina tsoron kar su Ammi su gane wani abin ya shiga tsakanin mu ne"??shiru tayi tana jin ran ta na kuma yi mata sanyi dan yana nuna mata damuwar sa akan ta"Kana ganin su Ammi ba zasu fahimci komai ba kuwa"?ɗan murmushi yayi kafin ya ce
"Ina ga kawai mu fasa komawa gobe har sai kin dawo normal self ɗin ki what did you think"?ɗan murmushi tayi kafin ta girgiza kai ta ce
"Bad idea...in har bamu koma gobe ba tsaf su Ammi zasu gane dan for the past few days ina ta hide and seek da su ba Umma ba ba Ammi ba duk sun saka ni ka san ma wani abu"?sai ya girgiza mata kai yana murmushi
"A duk lokacin da muka yi waya da su..."sai ta dakata tana murmushi kafin ta cigaba har ya riga ta tambayr ko menene
"Me ke faruwa in kun yi wayar"??ɗan girgiza kai tayi tana mamakin hali irin na iyayen su kafin ta ce
"A kullum in muka yi waya da su sai su rinƙa min tambayoyi,last time da muka yi waya da Umma ka san me ta ce min"??sai ya girgiza kai yana murmushi dan ya san taɓarar iyayen su.
Murmushi tayi kafin ta ce
"Ce min tayi wai tsakanina da Allah in gaya mata anya ba ciki bane da ni wai dan ta ga mood ɗi na na saurin switching at least sau uku nake possessing mood swing ɗin da nake exhibiting kwanannan in muna waya da ita"..wani irin shaƙiyin dariya ne ya kuɓuce masa mai tsanani dan yi yake har sai da ya saka ta dariyar ita ma sai can suka tsagaita sai ya ce
"Humm su Umma kenan"wani dariyar ne ya zo masu a tare suka kuma ƙyaƙyatawa sai ya ce
"Toh ke kuma me kike ce masu a matsayin amsar tambayar su"?kamar da gayya ya mata tambayar sai ta ce
"Me kuwa zan gaya masu"dariya suka kuma yi a karo na uku sai ya ce
"Toh yanzu fah"?duka ta kai mai sau ya riƙo hannun ta yana mata dariyar shaƙiyanci
"Shall i get you your phone dan ki gaya masu mun ɗauko hanyar samar masu da abin da suke so"?ɗaga kan ta tayi daga kan ƙirjin sa ta mayar kan pillow tana nuna mai fushin ta sai kawai ya bi ta da dariya ya ƙara mata abin takaicin da ya mata wai
"Toh shikenan tunda ba zaki kira ba ni bara na kira su dan kin san iyayen mu are modernized they are civilized zasu taya ki tanadin abin kula da ke ne instead,so let me call them"!!ai a 360 ta dawo kusa da shi tana faɗin
"You can't do this o bet you"ɓata fuska yayi yana faɗin
"Kenan mun saba haka da ke a rayuwar mu ko"?itama ɓata fuska tayi tana faɗin
"Ka daina irin wannan wasar Zaid bai kamata ba,i am the one that got cheated and ni zaka yi reporting again"?sai yayi shiru yana sauraron ta kafin ya ce
"I wanted asking you something important Bilkisu"sai ta zamo serious ta dawo da hankalin ta gabaɗaya kan sa ta ce da shi
"Me kake son tambaya na"?ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce da ita cikin son ɓoye damuwar sa akan lamarin ya ce
"Ina jin wani irin strong attachment game da outreach ɗin mu"sai ta ji gaban ta ya faɗi cikin tsoro ta ce.
"Me kake ji game da ƙauyen Zaid"??sauke ajiyar zuciya yayi kafin ya ce
"Am disturbed...i am concern..about that girl,ko wani hali take ciki"??dumm ta ji ƙirjin ta ya amsa sai ta ji hankalin ta ya fara tashi ta fara kasa controlling kan ta amma an ce mahaƙurci shi ke cin moriyar zance dan haka sai ta haɗiye wani abin da ya taso mata ta ce cikin shaking voice
"Which girl is that"??ɗaga kan sa yayi sama yana kallon mounted ceiling decoration ɗin ɗakin kafin ya furzar da iska mai ɗumi daga bakin sa ya ce
"Asma'u"!!wuf ta tashi daga kwancen da take saman ƙirjin sa ta ji faɗuwar gaban ta na tsananta kamar ana saukar mata da duwatsu daga ƙirjin ta wanda ke penetrating har cikin zuciyar ta hakan ke haifar mata da tsantsar tsoro,abin da take tsoron ji shi kunnuwar ta ke son kawo mata,me Zaid ke son yi mata ne haka,sai yau,yanzu,a wannan moment ɗin da tayi cherishing sama da ko wani moment na rayuwar ta,a daren da take darajawa take ganin ƙimar sa fiye da ko wani dare na rayuwar ta,she thought after what happened between them shikenan zasu zama ɗaya and he will forget that culprit,amma sai gashi tun basu bar nan ba suna maintaining posture ɗin su na ɗazu yana shigo mata da maganar yarinyar da ta fi tsana a rayuwar ta sama da komai,why will he do this to her,me ta yi mai da tayi deserving wannan abin farat ɗaya haka,why Zaid whyy..abin nan ya sosa mata zuciya ba kaɗan ba dan ta tsani jin sunan yarinyar a rayuwar ta.
"Kina jina Bilkisu"!?haɗiye yawu tayi kafin ta ce
"Uhmm"!..sai ya cigaba da cewa
"I couldn't reach Dr Hussain,na so in nemi alfarmar sa da ya haɗa ni da Asma'u dan ina son sanin halin da take ciki because i can vividly remember that...she was in that hectic scene da yaron nan ya kawo mana attack and i heard her voice saying no that i should go,that i should fight that beast...but i failed,,na kasa cika mata umarnin ta Bilkisu,i feel so ashamed,when i waked up i saw myself in that hospital i wanted asking about her but...sai na rasa wanda zan tambaya,na so tambayar ki but wani anu na hana ni dan ban san amsar da zan samu ba ko tana raye ko a mace,i know that Mudan is a dangerous person and he can do anything for his personal gain ciki har da son mallakar Asma'u which i won't allow that to happened never sai dai in bana raye"dan dakatawa yayi kafin ya cigaba
"Na yi iya ƙoƙari na amma ban sami damar yin magana da ita ba a duk lokacin da zan kira Dr Hussain sai ya ce min ai baya nan shima yana bakin aiki kuma in na nemi sanin abin da ya faru sai ya ce min bai da masaniya but i get so confused in ba shi ya fitar da mu daga cikin forest ɗin nan ba then who could that be?sometimes sai in ga kamar Asma'u ce ta taimaka mana and this thought always makes me feel like i am indebted to her sai in rinƙa ganin kamar haƙƙin ta na hunting ɗi na bana jin na mata adalci and i promised her that zata yi karatu mai zurfi na mata alƙawarin zan fitar da ita daga wannan lunatic dajin na su in kawo ta birni,she gave me this name 'Ɗan birni' and i promised her that ita ma zan sa jama'ar ƙauyen su su fara addressing nata da ƴar birni,but duk waɗannan analysis ɗin nawa are almost diminishing na bar ta tare da yaron nan what if he marries her?ya zata yi?me zata ɗauke ni?cewa zata yi ban san muhimmancin alƙawari ba zata ce ban da amana dan na mata alƙawari but na kasa cikawa i am blaming my self i feel so ashamed and that is why i decide that in mun koma gobe after two days zan yi tafi,zan tafi ƙauyen koma dan sanin halin da take ciki and i will seek for her forgiveness dan ina jin nauyin alƙawarin da na kasa cika mata na bibiya ta what did you think"?

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...