Page 5

1.9K 157 4
                                    

*⚜BWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

*5*

"Sunan ta Asma'u kuma ƴar nan yankin ce again bai kamata ki tsare ta kina mata ihu ba kawai dan ta zo ƙarƙashin ki neman abu a gare ki ba"daga haka yayi shiru yarinyar ta kada baki ta ce
  "Ɗan birni baka faɗa mata ɗayar sunan ba"sai ta juya ga Bilkisu ta kalle ta cikin fitsara ta ce
"Ma'ulle"inkiya ta kenan kuma bana ɗaukar raini ban ma san abin da ya sa na kyale ki kika gasa min magana har haka ba ba tare da na nuna miki ko ni ɗin waye ba"ta juya kai tana rakaɗi

Tsyawa kallon ta tayi cike da alhinin wannan fitsararriyar yarinya marar tarbiya ta juya ta kalle shi ta ce da shi

"What ever her name is ba business ɗi na bane dan bata gaba na iya abin da na sani ba zan ɗauki rashin kunya daga wun ƴar ƙanƙanuwar yarinya ba kai da ka san ta sai ka nuna mata muhimmancin zuwa na dan bata isa in zauna orienting ɗin ta ba"a zafafe ta karasa maganar wanda hakan ya bashi mamaki dama ta na da masifa har haka?shi kam bai taɓa gani ba sai dai ji a hospital a ce ta masife su a asibitin but shi bai taɓa witnessing ba

"Me ya sa ba zaki iya mata magana da kanki ba alhalin kin san ke ce da laifi"ƴar ƙaramar scoff tayi ta ce

"Are you for real"? Ɗage mata gira ɗaya yayi daga haka ta mai banza ta cigaba da abin da take da niyar yi

"Ku yi haƙuri fah kun san a wuri dole mutum ya haɗu da masu tarbiya da marasa shi in kuma mutum ya haɗu da marasa sanin ina ke masu ciwo dole ya daidaita su domin samin kyakyawar sakamako a wun aiki ko ba haka bane"?cikon chorus suka amsa da
"Haka ne likita"ta yi murmushin gamsuwa ta ce da su

"Toh yanzu dai zamu fara abin da ya kamata saboda yanayi na gari tunda ruwa ake yi yanzu gashi akwai ayyukan gida da za'a yi in an bar nan dan haka ba tare da ɓata lokaci ba zaku gaya min sunayen ku ne da shekarun ku haka ma da ayyukan da kuke yi"murna suka yi sosai dan she tried as much as possible ta wurin bringing kan ta so low wanda ya saka su jin kamar ta saka kan ta a shoe ɗin su ne dan haka babu ɓata lokaci suka fara gabatar da kan su ɗaya bayan ɗaya yayin da ita kuma yarinyar mai suna Asma'u ta haɗe rai tana ta faman kumbure kumbure yayin da shi kuma ya ke ta bata haƙuri,sam ta manta da su a wurin ma kwata kwata sai da aka yi rabi da introduction ɗin ta fara duba shi,chan wani bakin bishiya ta hango su zaune abin ya firgitata dan haka ta juya ga ɗaya daga cikin matan da suka yi introducing kan ta ta ce mata
  "Wai ni kuwa baba waccan yarinyar wacece ita"?ajiyar zuciya ta sauke ta ce cikin jimami

"Kin ga waccan yarinyar"? ta girgiza mata kai sai ta cigaba
"Sunan ta dai kamar yadda bokan turai ya sanar da ke Asma'u ɗiya ce ga mamman mai rasuwa dattijon kirki da kamala mutum mai haƙuri duk faɗin yankin nan ana daraja shi ba kaɗan ba dan bayan sarki da mai gari sai shi halin dattako irin tasa yasa ko matsala aka samu wun shi ake zuwa dan ana mutunta shi ba kaɗan ba..ita kaɗai ce ƴar shi mace yayyen ta biyu maza duk yaran kirki ne su ita kaɗai ce ta fito bare babu hali dan uwar ta ta yi ƙoƙarin tarbiyartar da ita haka mahaifin ta ma yayi ƙoƙarin sa sai dai albasa bata yi halin ruwa ba dan daɗin taɓarɓarewar tarbiyar ta wannan tsagerin saurayin nata mai suna Mudan yaron nan babu hankali gashi dai a fuska kamili daga shi har ita sai dai babu halin arziƙi toh a faɗin ƙauyen nan ko wani lungu da saƙo an san su dan tare suke zaga garin kuma duk wanda ya san Mudan ya san shi da jarabar tsiya da fitina toh haka duk wanda ya taɓa Asma'u ya taɓo jaraba dan kusan kowa tsoron sa yake ji ba kaɗan ba shi yasa ƙarfe shida na yamma na bugawa zaki ga yaran gari sun koma gidajen su amma a lokacin Asma'u take cancaɗa kwaliya ta fita ita da Mudan su zaga garin nan sai karfe tara na dare suke dawowa an daka har an gaji amma bata daina ba dan haka aka zuba mata idanu kawai toh kamar dai yadda muka ji shi wannan bokan turai shine yayo dare a hanyar sa ta dawowa daga cikin gari tsageran garin suka tare shi a hanya itakuma sun rabu da Mudan kenan zata dawo gida ta ci karo da su a hanya ai kuwa shine ta masu kaca kaca kuma sun san ko ita ɗin wacece sai suka gudu ba dan haka ba da sun mai kisan gilla dan ba su son harkar asibiti a cewar su duk ma'aikatan asibiti bankaɗo sirrikan su na shaye shaye suke yi daga haka gwamnati sai ta saka masu ido har a tono asirin su a hukunta su wanda hakan ba daɗi ke masu ba,toh kin fah ji labarin wannan botsararriyar ƴar wacce ta fi ƙarfin jama'an gari...

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now