Page 40

1.6K 108 19
                                    

BWA

{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
     {the love saga}

#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and more

  SIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim

  40

Tana zaune a wurin kamar statue tana kallon sa kamar bata san sa ba brain ɗin ta ya tsaya wuri ɗaya ya daina aiki ya tsaya cak,.ihun da ta yi ne yayi sanadiyar zuwan receptionist ɗin, buga ƙofar ɗakin suka shiga yi amma gam a rufe dan haka suka koma ɗaya daga ciki ya zo da spare room key ɗin suka gwada sai ya buɗu da sauri suka ƙarasa ciki sai suka shiga cikin bedroom ɗin dan ba su ga kowa a falon ba.
  Abin ya rikita su ganin ga Bilkisu chan kanannaɗe a ƙurya ga ƙarfen nan a ƙasa ga Zaid kwance kamar marar rai sai suka raba jiki wasu suka nufi Zaid wasu suka nufe ta ganin ko ƙyafta idanu bata yi sai suka yi tunanin shock ta shiga dan haka aka ɗauko bottle water aka yayyafa mata kamar ba zata yi responding ba sai gashi ta ja numfashi tayi blinking idanun ta..
  Cak ta saukar da idanun ta kan dead alive husband ɗin ta,da rarrafe ta iso inda yake kwance ana son tabbatar da yanayin da yake ciki ko da rai ko babu aka duba pulsating regions wuyan sa carotid artery da radial artery ɗin sa sai aka tabbatar da eh akwai gudanar jini aka duba bugun zuciyar sa nan ma aka tabbatar da cewa yana da rai sai suka yi saurin kiran hospital  emergency number babu jimawa aka zo daga asibiti mafi kusa da hotel ɗin dan ɗaukan sa..
  Tun da ta kai hannun ta saman nasa hannun ta ƙura mai idanu hawaye ne ke ta bin fuskar ta suna tsiyaya wasu na korar wasu da ta ji an ce he is still alive sai ta kalle su dan tun da suke ta examinations ɗin su bata motsa ba sai da suka zo ɗaga sa aka raba hannun ta da nasa dan fitar da shi..
  Kiran hukuma aka yi dan a zo a yi tracing incidence ɗin da ya faru a wurin saboda sanin wanda ya shigo ya aikata hakan dama ga CCTV cameras nan da za'a yi tracing ta cikin shi...
  Ba daɗewa suka iso sai suka fara gudanar da aikin su suna ƴar tambayoyi as for Bilkisu babu abin da suka samu daga gare ta dan kamar kurma haka ta zamo masu dole suka bar ta akan zasu dawo su kuma neman evidence daga gare ta dan ita ce ta fi kusanci da victim ɗin sun ɗau hotuna daban daban na incident site ɗin...

  Da taga da gaske tafiya da shi zasu yi sai ta miƙe zata bi su amma wata mace cikin masu kula da hotel ɗin ta dakatar da ita dan babu sutura a jikin ta sai rigar wanka gwara shi yana da T-shirt da wandon bacci a jikin sa..
Fincikewa take yi akan a bar ta tana son bin su amma aka hana ta matar ce ta nemo mata suturar sakawa ta miƙo mata cikin sauri ta saka kayan suka fito ƙala dai bata ce ba har suka zo wurin motar tana kuka ta shiga cikin inda aka saka sa ta ɗago kan sa ta ɗora bisa laps ɗin ta ta ɗora hannun ta saman fuskar sa da haka aka ja motar aka bar hotel ɗin aka nufi hanyar asibiti..
  Kuka take yi sosai tana shafa kyakyawar fuskar sa tana kai mai kisses time to time tana jan hanci duk ta hargitse ta fita hayyacin ta kamar zararriya haka ta dawo kamannin ta gabaɗaya ya canza kamar ba Bilkisu ba...
  A haka suka isa asibitin inda aka yi E&A da shi cikin sauri jikin ta kaf ya ɓaci da jinin da ke fitowa daga kan sa kuka take kamar wace ta yi asara a rayuwar ta lallai ba dan ita ta aikata wannan aikar ba da babu abin da zai hana ta yin sanadin wanda ya aikata hakan visiting hell a yau ɗin nan..
  Zarya take ta yi a bakin ɗakin tana hango yadda ake masa dressing external bleeding ɗin ko da aka gama sai aka gano akwai concealed bleeding dan ga wurin nan yayi bulky ya hauro sosai seducing nasa aka yi aka mai allurar kashe raɗaɗin zafi dan kar abin ya saka sa a shock..
Da suka yi stabilizing nasa sai suka fito suna tambayar waɗanda suka taho tare da patient ɗin,saurin tashi tayi ta nufe su sai dai duk tambayar da aka mata sam kasa bada amsa tayi sai kuka da suka fuskanci cewa shock ta shiga sai suka nemo paper da pen suka miƙo mata..
  Da sauri tayi grabbing ta fara rubutu rubutu mai tsayi tayi har sun fara tsammanin hala mahaukaciya ce dan yadda jikin ta ke ɓari ga zufar dake tsatsafo mata ta ko ina kuma kusan rabin hour bata kammala ba sai suka yi concluding bata da hankali.
  Juyawa suka yi dan su koma ciki sai ta taɓo wanda ya bata paper da pen ɗin,juyowa yayi ya ƙura mata ido sai ta miƙo mai papern ya karɓa yana nazarin ta kafin ya maida idanun sa kan papern ya karanta loudly ta yadda sauran zasu ji..
Jinjina kai suka yi sakamakon ganin abin da ke rubuce cikin papern dan komai da ya faru da shi ta zayyane masu cikin papern har da dalilin ta na buge sa da tayi ta nuna masu ita ta aikata hakan har da papers dake ɗakin su na 5 star hotel wanda cikakken medical history papers ɗin Zaid ne a ƙarshe ta roƙe su da su yi saurin ceto mata ran mijin ta dan yana nan yana battling da rayuwar sa kar su ga kamar sun yi seducing nasa yana iya rasa ran sa a haka dan daga ita har shi doctors ne...

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now