Page 18

1.3K 111 9
                                    

*⚜BWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

   *18*
     *_promise_*

  Abin mamaki me ke damin ta ne wai haka,ta yiwa kanta tambayar sannan ta ba ma kanta amsa "what else if not love"!!hakan ya sa ta shiga murmusawa ita kaɗai ba tare da ta san tana hakan ba mayar da idanun ta tayi zuwa kan suman kan sa da yayi yawa fiye da da sai ta ji kamar ta masife Hakim da ke kula da shi akan menene ba zai gyara mai fuska da kai ba gashi nan suman kan sa da na fuskar sa sun wuce misali ai hakan sai ya ƙara mai rashin lafiya,
  Zancen zuci take ta yi ita kaɗai daga bisani ta miƙe ta tofa mai addu'a sannan ta fara tafiya dan komawa ɗakin ta tana tafe tana juyowa tana kallon sa har dai ta kai bakin ƙofar kamar kar ta fita ta zuba mai idanun nan nata tana kallon sa cikin sigar da bata san yanda zata alaƙanta sa ba.
  Firgigit kamar an tsungule ta sai ta ga kamar baccin da take yi har yanzu bata farka ba haba in ba a mafarkin ta ba dama ta yaya Zaid zai yin yunƙurin yin wani abin ai sai dai a mafarkin dan haka ta saka kan ta zata fita ta kuma jin alamar faɗuwar abu wani juyin bori tayi a zafaffe ta buɗe idanun ta gaban ta na tsananta bugawa tana fargaban abin da zai biyo baya in har bai yi alama ba toh gaskiya ba zata taɓa yafewa zuciyar ta ba for making her imagination go beyond her limits.

Sharewa tayi ta yi kamar zata fita sai dai hakan bai yiwu ba sakamakon jin numfashin mutum kamar yana gasping sai ta juya a rikice tana baza idanun ta dan ganin daga inda numfashin ke fitowa bata san lokacin da ta dira a gaban sa ba sakamakon ganin ɓarin flower verse a gefen gadon sa,saurin yaye comforter ta yi hannun ta na ɓari tana gama yaye comforter ɗin sai ta ga shi ke numfashin kuma taimakon gaggawa yake buƙata dan haka ta fita cikin gaggawa bata tsaya ko ina ba sai a ofishin likita da ƙarfin ta ta shiga office ɗin tana ta kwala mai kira a rikice ya fito daga cikin bathroom da shigar sa kenan yana tambayar ta ko lafiya ta rasa me zata sanar da shi sai kawai ta shiga kirawo mai room number tana faɗin
  "405...405..405."ganin ta ruɗe sai ya ce da ita
"Is okey let's go"da gudun ta ta fita shima ya biyo ta suka ranƙaya zuwa ɗakin da shigan su ya riga ta zuwa kan gadon.ganin Zaid yayi yana jacking yana gasping da sauri da sauri sai ya cire mai mask ɗin ya yi regulating device da zai rinƙa bashi iska,fita yayi cikin hanzari ya nufi office ɗin sa babu jimawa ya dawo shi da wasu doctors biyu a nan ne aka buƙaci baby doctor da ta fita girgiza masu kai ta shiga yi tana kuka tana faɗin ba zata iya fita ba,hayaniyar da ke fitowa daga ɗakin ne ya janyo hankalin Hajiya Madina da Hajiya Zeenat da ke kwance a ɗakin masu kula da majinyata fita suka yi gabaɗayan su zuwa hanyar da hayaniyar ke fitowa,ko da suka tafi sai suka ga abin tashin hankali wato Bilkisu ce ke faman risgar kuka while ga doctors nan uku a ɗakin da Zaid yake kamar dai so suke su yi stabilizing nasa sai Hajiya Madina ta ɗan janyo Bilkisu tana tambayar ta me ya faru.
In banda kuka babu abin da take yi hakan ya sa Hajiya Madina jan ta suka bar wurin a inda Hajiya Zeenat ta tsaya tana hango abin da ke gudana a ɗakin duk hankalin ta a tashe yake ko me ya sami Zaid ɗin sai Allah dan haka zirga zirga ta shiga yi a bakin ƙofar Hajiya Madina dai bata dawo ba dan bata jin zata iya cigaba da witnessing abin da ke faru sai ta tsaya tana rarrashin Bilkisu kawai.

  An hour + kafin doctors ɗin su sami damar saisaita Zaid dan sun fahimci cewa ya farfaɗo ne kuma da ƙarfin sa ya farfaɗo dan kuwa so yake ya farka gabaɗay sai dai ciwon da ke kansa wanda ya janyo masa surgery bai warke ba dan haka dole komai sai a hankali zai saba da shi they were able to seduce him dan ya koma bacci kuma he is calm shi yasa suka fito a nan Hajiya Zeenat ta tare su tana tambayar su ko me ya faru shi babban likitan ne ya yi inviting ɗin ta zuwa office ta bi sa cikin hanzari.bayan sun zazzauna ne ya kalle ta at first moon face ya saka sai daga baya ya murmusa da smiling face ɗin ya ce da ita 
  "I must say,congratulations your son just regain consciousness and he is in good state of mind he will wake up in not less than an hour or more with full strength and ability what a surprise i guess"!!faɗaɗa murmushin sa yayi yayin da Hajiya Zeenat ta tafi ƙasa tayi sujjada bata ce da likitan komai ba sai da ta ɗago sannan ta kalle sa fuskar ta jiƙe da hawaye idanun ta sun yi ja ja zir tana dariya tana fidda hawaye ta ce da shi
"Thank you,thank you doctor,thank you"!!shima murmushin ya mayar mata da shi yana girgiza mata kai ya san tana cikin farinciki dan haka bai ga laifin ta ba dan ta zage tuƙuru tana kuka.daga office ɗin ɗakin zaman su ta nufa inda ta ga Hajiya Madina na rungume da Bilkisu tana rarrashin ta ita kanta mai rarrashin ta take nema dan haka ta ƙarasa shiga ɗakin ta ce cikin muryar kuka
  "Hajiya tashi ki ma Allah godiya our Zaid is back"ba ita kaɗai ba hatta da Bilkisun sai da ta razana dan maganar a matsayin abin almara ya zo masu da mamaki da al'ajabi sai suka tashi tsaye baki ɗayan su hawayen Bilkisu ya ƙafe yayin da Hajiya Zeenat ta buɗe baki cikin mamaki tana son yin magana amma ta kasa Hajiya Zeenat ta gane state of shock da ta shiga dan haka ta matso kusa da ita ta riƙe kafaɗun ta ta shiga girgiza ta tana cewa
  "Yes yess Hajiya Zaid is back for good yanzu na fito daga ofishin Dr kuma ya sanar da ni cewa Zaid ya farfaɗo kuma any moment from now yana iya farfaɗowa cikin ƙoshin lafiya abin godiya ne ga Ubangiji"!!sai ga hawaye sharr na fitowa daga idanun Hajiya Madina cikin farinciki da jin daɗi ta rungume Hajiya Zeenat ta saki kukan farinciki petting bayan ta Hajiya Zeenat ta shiga yi tana ƙara tabbatar mata da cewa eh Zaid ya dawo masu irin farinciki da suka tsinci kan su a ciki understatement ne sun manta da Bilkisu a ɗakin wacce ta yi suman tsaye sakamakon jin an ce Zaid ya farka a nan ta bar su ita kuma ta nufi hanyar ɗakin da Zaid yake.
   An saka dokar kar wanda ya shiga ɗakin har sai ya farka amma ita kam kai tsaye ta shige ta rinƙa bin sa da kallo tana jin wani abu a ran ta game da farfaɗowar Zaid a haka ta zauna gwiwa a sage ta kafa mai dara daran idanun ta waɗanda suka chanza launi zuwa jajjaye saboda kukan da ta yi saƙe saƙe kala kala take yi a zuciyar ta mafi akasarin saƙe saƙen sun ta'alaƙa ne ga mafitar rayuwar ta in Zaid ya farfaɗo ya kuma gane cewa shi da ita sun zama ma'aurata wanɗanda zasu rinƙa zama inuwa ɗaya tun farfaɗowat sa har izuwa ƙarshen rayuwar su ya zai karɓi maganar?shin da wani siga zai fahimci maganar?zai amince da ita kokuma a'a?zai ma yarda ya ɗauke ta a matsayin abokiyar rayuwa ta har abada?waɗannan tanbayoyi sun tsaya mata a rai she knows that tomorrow will be her wedding day ranar da ba zata taɓa mantawa da shi ba a rayuwar ta saboda tambari ne that will signifies a new life,a new beginning and a new world to her.but is she well prepared and ready to accept it?sai ta kuma kallo sa ta ga yadda yake fidda numfashi a hankali har yanzu bata san me take ji game da shi ba it's somehow mix the chemistry is over reactive reaction ɗin na boiling ko wani ɓangare da saƙo na jikin ta,kanta ne ya fara ɗebar chaji sai ta tsagaita da tunane tunanen ta cigaba da kallon sa.

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDOnde histórias criam vida. Descubra agora