⚜BWA
{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}
👄 °°° °°°👄
°°
°🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
{the love saga}#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and moreSIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim
42
Triumph Bliss
Da asubahin fari suka farka almost the same time sai ta riga sa dirowa daga kan gadon ta nufi hanyar toilet ta fara haɗa mai ruwan wanka dan so take su kammala abin da zasu yi da wuri su tafi asibiti dan so take ko da da kaɗan kaɗan ne ta sabar mai da zagawa ganin gari than yayi ta zama haka nan indoor..
Dawowa ɗakin tayi ta fara tayar da shi sai ya buɗe mata idon sa ya zuba mata su yana kallon ta irin wannan kallon da ya ɗorawa kan sa a tsakankanin jiya da yau sam bata son shi haka nan ta ji she is not comfortably da kallon shirun da yake mata...
Kawar da fuskar ta tayi gefe a hankali ta yadda zai ji ta ce
"Zo mu je ka yi wanka lokacin sallah ya kusa"shiru ya mata kamar bai jin ta sa da ta kai hannun ta ta saka cikin nasa ta shiga ɗaga sa sai ya biye mata ya tashi a hankaki cikin tsan tsan ta ɗaga sa suka nufi toilet ɗin a hankali ta wanke mai bakin sa sannan ta kai sa gaban shower ta bar sa a tsaye dan ta ga ko an sami improvement daga jiya zuwa yau a ability ɗin sa na tsayuwa da ƙafafun sa..
Sai ta ga bai yi shaking sosai ba compared to na jiya sai ta sami ƙwarin gwiwa da fara'a ta ta mai wankan hankalin ta kwance dan a tsaye ma ta mai da ta gama ta miƙo mai wani cup mai cike da ruwa dan ya yi alwala..
Dawo da shi ɗakin tayi ta shimfida masa darduma ya fara sallar sai ta koma ciki tayi wanka ta yi alwala sannam ta fito cikin sauri ta shirya cikin shirin fita ta saka hijabi ta tayar da sallah a lokacin shi kuma ya idar sai ya jira ta har ta kammala nata sallar tayi addu'aoin ta sannan ta juyo tana facing nasa cikin girmamawa ta ce
"Ina kwana hero"bin ta da ido yayi kamar bai ji ba sai ta ɗago kan ta ta kalle sa ta ga ita yake kallo shima sai ta kuma nanata mai gaisuwar..
Cikin dishewar murya ya amsa mata da
"Lafiya ƙalau"sanyi ne ta ji a ran ta daga haka bai kuma ce mata komai ba sai ita ce tayi ƙarfin halin tambayar sa
"Ya jikin ka"??bayan wasu seconds ya amsa mata da
"Alhamdulillah"daɗi ta ji jin bai share ta ba kamar yadda tayi tsammani kuma bai canza mata fuska ba....Cikin jin daɗi ta ce da shi tana mai matsowa kusa da shi
"Are you sure babu inda yake maka ciwo"?da ƴar murmushin ta ta faɗi hakan sai ya juyo da kan sa yana kallon ta kafin daga bisani ya ce
"Akwai"!!!cikin faɗuwar gaba ta ce
"Ina ne kuma"?idon ta na ciccikowa da hawaye yayin da ta mai tambayar sai ya mata shiru ita kuma ta tsani wannan shirun dan kashe ta yake yi a hankali...
Hannun ta na rawa ta kawo kan nasa hannun ta haɗe wuri ɗaya ta fara murzawa a hankali ta kuma maimaita mai tambayar
"Ina ke maka ciwo hero"??hannun sa na hagu ya ɗaga a hankali ya yi amfani da index finger nasa yayi pointing mata direction na zuciyar sa..
A wani irin haukace ta raba hannun ta da nasa ta ja baya tana mai rufe bakin ta sakamakon jin wani ihu da ke son kufce mata...
Kallon ta yayi ya rasa me ya razana ta da ta firgita haka sai dai bai iya ce da ita ƙala ba..
Faɗuwar gaban ta ya tsananta ta ji ko ina na jikin ta yana mata wani iri sai ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya..
For a while yayi shiru yana kallon ta har dai ya magantu
"Lafiya"??muryar sa chan ciki yayi tambayar sai dai ita da ke a ruɗe ta kasa gane cewa tambayar ta yake sai ta kuma fashewa da wani kukan har dai ya gaji ya matso kusa da ita...
Bata sani ba sai dai jin ta tayi a jikin sa yana mai rubbing hannun sa a bayan ta..
Ai kamar ya kuma ingiza ta ta kuma fashewa da wani sabon kukan sai yi take yi shi kuma yana rarrashin ta..
Tsagaitawa tayi daga kukan da take yi ta natsu sai ta ji kamar daga sama muryar sa na mata amshi a kunnen ta
"Me yasa kika min haka"??ɗif ta ji ta ɗauke wuta sakamakon tambayar da Zaid ya mata dan out of the blue ta ji tambayar...
Ɗagowa tayi niyar yi sai ya ƙi barin ta ta ɗagon ya kuma mayar da ita ya rungume ta..
A ƙarƙarshin zuciyar sa shi ya san sam bata da mummunar nufi a bisa ga abin da ta aikata mai sai dai ta saka sa duhu son sanin dalilin ta na yin hakan kawai yake...
Silent tears ne ke biyo mata fuskar ta a hankali suna sauka saman rigar jikin sa bata iya ce mai komai ba haka shima bai iya furta mata komai ba yana sauraron ta...
Share hawayen tayi da hannun ta ta ja hanci tana mai jin zafi da raɗaɗin abin da ta mai a zuciyar ta...
Kaf abin da ya faru ranar a dajin ƙauyen koma ta mayar mai sannan ta dawo ta sanar da shi rayuwar sa a asibitin germany ta ɗora da bayanin da Dr Gabby ya mata da ɓoyewar da ta ma family ɗin su har kawo ga bayyana mai dalilin ta na aikata mai abin da ta aikata ta ɗora da sanar da shi kyakyawar labarin ya warke kenan har abada babu shi babu wani matsala mai firgitarwa
"You can now leave a normal life just as everyone does"..hawaye duk ya gama wanke mata fuska dan tsakanin ta da Allah ta ke jin tausayin sa na bin duk wasu sassa na jikin ta sai dai itama bata da yadda zata yi shi yasa ta kasa fidda abin a ran ta but yanzu da ya nemi sanin dalilin hakan ta mai bayani sai ta ji sauƙi a ran ta at least ko ba zai cigaba da son ta ba ko nuna damuwar sa da kulawar sa a kan ta ba ta san zai iya yafe mata wataran...

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...