*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more**SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*4*
A ranar kasa rintsawa ta yi sakamakon zullumi da fargaban ko me zai wakana washegari kiran Bahajjatu ta yi a waya bata ɗauka ba an saka mata number busy kuma kira ta yi har sai da ta ɗauka"Haba Beelove wani irin fitina ne da daddaren nan kin kira kin ga am busy kin kuma kira na saka ki a on hold wai menene"?
Gauron numfashi ta sauke kafin ta ce
"Baha ina tsoron tafiyar nan"ɗan shiru suka yi kafin ta ce da ita"Me ya sa zaki ji tsoro Beelove bayan kin saba zuwa outreach ɗin nan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba toh nervousness ɗin na meye"?
"Ban sani ba Baha amma ina da atrong feelings akan cewa babu alkhairi a outreach ɗin nan i don't know maybe is because of your brother am not just comfortable Baha"!! ta ida kamar zata yi kuka dan haka Bahajjatu n ta ɗan saurara mata kafin ta ce
"Beelove calm down please you are being over reactive na ke ganin kamar ki yi magana da yaya Zaid kafin goben saboda ki sami relief ko me kika ce"?Bahajjatu is always putting a bilnd eyes ma duka abubuwan da ke wakana a tsakanin su haka take da halin ban san kuna da misunderstanding ba which hurts baby doctor ba kaɗan ba..
"Alright fine tunda haka kika ce nagode good night take care".. Tana kaiwa nan ta datse kiransau uku Bahajjatu na kiran ta ta ƙi ɗagawa dan ta san ta mata sallamar da ɓacin rai shi yasa ta rinƙa calling back amma ta ƙi ɗagawa haka ta haƙura ta tura mata saƙon safe journey akan washegari zasu yi goodbye proper ignoring message ɗin ta yi ta tashi ta saka slippers ɗin ta ta nufi ɗakin Bilal wanda ke ta faman rarrashin apple ɗin sa dan ta ƙi magana da shi laifin Bilkisu ya shafe shi,bata wani tsaya buga kofar ba da yin sallama ta turo ƙofar luckily yana buɗe,Da sauri ya leƙo daga cikin comforter ɗin dan bai yi tsammanin ganin kowa ba..haɗa ido suka yi ya ga yanayin ta ya chanza sai ya bama Bahajjatu haƙuri akan zai kira anjima ya katse wayar yayin da ita kuma ta ƙarasa shigowa ɗakin tana taku a hankali kasa haƙura yayi har sai da ya tambaye ta me ke damin ta. zama ta yi a saman hannun kujerar ɗakin tana ƙoƙarin danne hawayen ta
"Apple me ke damin ki har kike ƙoƙarin zubar da hawayen ki"? ai kuwa sai ga hawaye sun gangaro ta yi saurin goge su
"SubhanaAllah apple wai menene"?Juyar da kan ta gefe tayi ta ce
"Bilal bana jin akwai alkhairi a tafiyar nan da za'a yi amma babu wanda ya fahimce ni nayi nayi in fahimtar da Abba amma baigane ba ya yarda da Zaid Maher sama da misali umma ma ba'a magana dan bata son jin laifin sa Bahajjatu ma bouncing ɗi na take yi saboda yayan ta ne tauraron ta bata ganin illar abubuwan da yake aikatawa kai kuma tun farin maganar nan na sanar da kai yadda nake ji amma baka taya ni jimami ba toh duka waɗanda na amince da su basu yarda da ni ba wa kuma zai yarda da ni"? ta ƙarashe tana sakin silent cry wanda ya karya zuciyar ɗanuwan nata har shima ya ga rashin kyautawar sa out of all peoplr he should understand sama da kowa but bai bata wannan chance ɗin ba ya biye ma halin ta na sanyi ya ƙi fahimtar damuwar ta."Bilkisu am so sorry please forgive me ban san abin ya dame ki da yawa har haka ba ni duk a tunani na maybe kun sami masalaha ne a tsakanin ku but believe me apple wallahi wallahi ban san har yanzu akwai matsala a tsakanin ku ba but since it turns out to be this way ki zo mu je wun Abba a san na yi dan shi kan shi ba zai yarda ki tafi outreach ɗin da hankalin ki bai kwanta da shi,lets go"! ya miƙe tsaya yana ƙoƙarin jan hannun ta su tafi dan abin ya ƙona mai rai.

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...