Page 26

1.7K 120 14
                                    

BWA

{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
     {the love saga}

#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and more

  SIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim

  26

  Ɗaga ƙafar sa yayi cikin ɗar ɗar da tsantsar faɗuwar gaba na fara takawa cikin halin komai ma na iya faruwa da su su biyun dan abin da ke yunƙurowa yana taso mai ba abin da kowa zai iya fassara mai bane sai shi kan sa,each step nasa na ƙara mata babban tambarin sa cikin zuciyar ta ba kaɗan ba wani maganaɗisun son sa ne ke tunzira zuciyar ta tana jin kamar ko garwashin wuta aka ajiye a gaban ta akan ta taka dan nuna son da take mai tana iya aiwatar da hakan..

  Ko da ya kawo tsakiyar ɗakin sai ya koma da baya ya kashe hasken ɗakin hakan ya janyo hankalin ta ta mayar da duban ta gare sa har da dai duhu ya mamaye ɗakin amma hasken dake penetrating labulen ɗakin daga harabar hotel ɗin sai ya sa take iya ganin sa sama sama ba sosai ba,..

  Hankalin sa a tashe yake jin kansa yake kamar wani dokin da aka shayar wa maganin dawakai sannan aka tsikara ma allurar doki dan ƙara mai ƙarfi,bai san abin da ke faruwa da body system ɗin sa ba bai gane ba hala rashin lafiyar da yayi ne ke saka sa yin abubuwa haka kamar marar cikakkiyar lafiya,within him inside him a zuciyar sa yana jin wani sashe na danne sa daga aikata abin da yake shirin aikatawa gare ta amma wani sashen da ya fi ƙarfin ɗaya sashen na nuna mai a'a kar ya bi shawarar wannan sashen dan abin da shi wannan sashen yake nuna mai shi zai kawo mai sauƙin damuwar da yake ciki..
   Wannan musun da ya kaure tsakanin sashi biyu na zuciyar sa ya haifar mai da wani sabuwar damuwar dan kan sa kamar zai buga tsabar ciwo da sara mai da yake yi,,shi kam anya hankalin sa na jikin sa kuwa?..
  Ganin ya tsaya ya kasa yin gaba ko baya gashi ya kashe mata hasken ɗakin ta ya hana ta yin saƙata kuma ba gama shirye shiryen ta tayi ba kwanciya tayi dan ta ɗan huta saboda ta sami ƙarin ƙarfin jikin ta kafin ta cigaba da aiki amma shigowar sa ya sa bata iya taɓuka komai ba sai ma sanyin jiki da ya rinƙa sauko mata ita kaɗai abin ta ta rinƙa saƙe saƙen ta akan manufar sa na shigo mata ɗaki sannan bai ce mata komai ba ya kashe mata fitilar ɗaki kai tsaye..
  Daga kwancen da take ne ta ga kamar yana da damuwa amma bai san yadda zai faɗa ba hakan ne ya sa ta laluɓo falmarar rigar baccin nata wanda yake dogo ne har ƙasa sai dai shara shara yake duk a huhhuje yake kamar rariya dan ana iya ganin jikin mutum sak ta cikin rigar baccin,gyara mahaɗar rigar tayi haɗe da mai da sumar ta gefe ɗaya sannan ta miƙe tsaye cikin takun ɗai ɗai mai rikitarwa ta nufe sa.
  Tsab yake kallon ta tun daga yadda ta laluɓo rigar ta saka har yadda ta gyara suman nata kawo ga tashin ta daga kan gadon da irin yadda take takun ta tana nufo sa abin ya shige sa ba kaɗan ba sai dai ya daure ya tsaya yana jiran ta ya ga abin da zata yi..
  Tsinkewa da lamarin ta yayi a lokacin da ya ji saukar hannayen ta masu daɗin taɓawa saman fuskar sa,duka hannayen nata biyu tayi amfani da su wun riƙo fuskar sa tana kallon fuskar nasa,babu wadataccen haske a ɗakin amma kaɗan dake reflecting ya taimaka mata wun hango damuwar da ke tattare da shi,saukar hannun ta saman fuskar sa ya saka sa lumshe idanun sa dole yana kuma jin abin da ya addabe sa game da ita na ƙara asassa mai...

  Cikin daddaɗan kalamai da son sanyaya mai rai haɗe da nuna mai muhimmancin sa ta fara yi mai magana a hankali kamar dai bata son yi
"Ka sanar da ni damuwar ka wata ƙil in baka shawarwarin da zai amfane ka dan matsalar da ka faɗawa wani har ya baka shawarar da ka sami sauƙi shine matsala mafi sauƙi a gare amma in kayi shiru sai dai damuwar ta cigaba da takura maka so did you need my comfort"?sauke mata sanyayyun idanun sa yayi yana son ganin abin da ya bambantata da wasu matan dan dai bata kasance wata ɗaya daga cikin masu jin kan duniya ba haka bata cikin matan da zaka kalla ka ce da su suna da muni but menene wannan banbancin da take da shi a tattare da ita da har take iya saka sa jin wani irin matuƙar yana tare da ita..

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now