SHINFIƊA

594 31 0
                                    

Alhaji Ahmed Dikko shine yaro na farko kuma na ƙarshe a wurin marigayi Alhaji Muhammad Dikko da Hajiya Sa'adatu da su ke kira Hajja. Asalinsu ƴan asalin karamar hukumar Dutsamma ta jihar Katsina ne, ciraninshi ya maido su cikin garin Katsina da zama.

Ya tashi da gatan dangi da na mahaifa kasancewar shi ɗaya tilo. Mahaifinshi shahararren ɗan kasuwa ne da ya rike mukaman gwamnati kala kala. Tun da Alhaji Ahmed ya gama karatunshi ya ke siyen filaye ya siyar da taimakon babanshi wani lokacin har ya gina ma ya siyar ko ya saka haya har Allah yayi wa mahaifinshi Alhaji muhammadu Dikko rasuwa. Bayan ƙara zurfin karatu a yanzu ya zama cikakken hamshaki ta fannin saye da sayarwa, ginawar filaye, gida je da sauran kadarori 'Real Estate Developer'
  Ya gina ƙaton kamfaninshin da yai mashi suna da DIKKO REAL ESTATE SOLUTION bai tsaya a nan ba sai da yai nasarar gina shahararren Hotel DIKKO ROYALE INN a nan gida nigeria da SouthKorea inda a cen ne kasuwancinshi ya fi yawa a duk cikin kasashen ketare.

Alhaji Ahmed Dikko mutum ne da ya san darajar kuɗi ƙwarai da gaske ya ke kuma ganin darajar masu kuɗin. Ba shi da rowa amma ya na gudun alaƙa da talaka wanda ya san babu abin da hakan zai ƙara mashi ban da ciwon kai. Kafin mahaifinshi ya rasu shi ya yi mashi auren fari da diyar abokinshi wanda sam shi bai so auren ba ya kuma yi duk yadda zai yi ya gujewa auren amman bai fasu ba. Dalilin ƙin auren bai wuce yadda shi abokin baban nashi ba kowa bane bai san kowa ba, ba wanda ya sanshi a ƙasa. Sun tashi ne da babanshi tun yarinta. Da jan idon da babanshi ya mashi ya sa shi haƙurin zama da ita amman a zucciyarshi da kudirin dallo wata matar yar manyan gida, a haka ne ya tashi da matayenshi ukku.

1. Hajiya Zinatu suna kiranta Umma, ta na da yara huɗu mata ukku namiji daya
•Amina: 28 years.
•Aysha:25  II
•Aseeya23 II
•Adam 16 II

Hajiya Zinatu ƙwarai ta nunawa Alhaji Ahmed ita ɗin fa talakkar ce, ta hanyar zalamar son kudinta a fili. Kishiyar da akai mata ya sa ta koyi dannewa duk da hakan ta na iya ƙokarinta wurin ganin ya ɗaura ɗanta a kan ragamar dukiyarshi. Amina da Aysha sun yi aure kuma Alhaji Ahmed 'Abbu' shi ne ya zaɓa masu mazaje don bai yadda zuri'arshi ta fada hannun wanda bai da ko sisi ba.

2. Hajiya Fatima ita ce mata ta biyu su na kiranta da 'Mami' Auren so su kayi. Lokacin da ya aure ta babanta ministan kudi ne. Mace mai tsananin kirki da kauda kai, sai dai ta na da fada ba laifi idan an shiga sabgarta da bai kamata ba. Yaron ta ɗaya Naseer wanda su ke kira da Nass shekarshi ashirin da bakwai 27. sosai Abbu ya daura burinshi a kan Nass saboda shine namijin farko da ya fara samu, tun ya na service Abbu ya nemo mashi mata daga babban gida a ka sha biki. Bai yi jayayya ba saboda komai na ta ya mashi ƴar gayuce ta ƙarshe kamarshi 'Nadra' ya na kammala bautar ƙasa a ka sha bikin kece raini ta tare a nan cikin gidansu DIKKO MANSION

3. Hajiya Rahama, su na kiranta Mom. Kusan babu tazarar shekaru tsakaninta da Maryam. Abbu ya samo ta a wani meeting da ita ce aka ba kwangilar abincin da za suci kasancewarta ƙwararrar wurin dafa abinci musamman na kwangilar manyan mutane da takan samu daga babanta. babanta kuma abokin kasuwancin Abbun ne wanda a yanzu ya dade da rasuwa tun bayan bikin, hakannkuma bai saka Abbu canza mata ba don ya na son ta kuma ya ci moriyar mahaifin nata sadda ya ke da rai. Mom mata ce mai mugun son kanta da son yin kane-kane da lamurran gida duk kuwa da kasancewarta ƙaramarsu. Ta na da mugun wayon da duk bala'in mutum bai isa sanin gabanta ko bayanta ba saboda tsabar kissa. Yaranta biyar

•Yaseer 25years
•Yusuf   23  II
•Yaseera 20 II
•Yusrah 16 II
•Yumna 8   II
••••••         •••••••      •••••••

Malam Suleiman da aka fi sani da Sule, Ɗane na biyu a wurin Mahaifinshi Mal Nura da Asabe. Yayanshi ɗaya Isa da a yanzu ya koma kano da iyalanshi ya na kasuwancinshi. Sai  ƙanenshi Umar da  shi kadai ne ya samu yin NCE ya na zaune a katsina shima, ya ke koyawa a wata primary. Shi kuma Malam Sule Shagon cikin unguwa ya ke saida yan provision ɗin da za a iya buƙata a unguwa kafin bukatun yau da gobe su cinye jarin tsaf ya koma kame-kame da yan buge-bugen neman na abinci. Matarshi ɗaya Mariya da yara biyu mata
•Fatima 16 Years
•Fa'iza   13  II
Mariya mace ce da ta matuƙar raina samun mijinta, ta kwashi laifin talaucinsu ta rataya a wuyanshi.





Kun shirya? to ku gyara zama😍

HAYAR SOWhere stories live. Discover now