20

220 16 2
                                    

In life we all have an unspeakable secret, an irreversible regret, an unreachable dream and an unforgettable love.

~~~~~
Cikin sauri-sauri ta gama taimakawa Ikram ta cinye abincin ta sannan itama ta yi breakfast, ta yi mata wanka, kayan ta daman da ɗan yawan su ta ɗakko daga ɗakin Hajja sai ta yi mata wanka ta saka mata, ta barta ta na wasa ita kuma ta shiga wanka.
Bata san haɗe ran me ya ke ba tun da safen nan, shi yasa da yace idan ta daɗe bata shirya ba ta nemi wani ba shi ba, ta zage ta na zuba sauri. Idan ma wata tijarar ya ke ji bata fatan ya sauke ta a kanta. Koma don Abbu ya saka ya kaita ganin fili da yo fassport ɗin da bata san ko na meye ba ya ke haɗe ran, oho dai. Ai ba ita ta saka shi ba.

Doguwar riga umbrella ta saka ta buɗe sosai, ta yi mata kyau musamman da atamfar take ja da baƙi, sai ta ɗaura kallabin ta mai kyau ta yafa baƙin gyale da takalma ta ɗauki Ikram a kafaɗa ta saɓi handbag ɗin ta ta fito falon. Zaune ta ganshi ya kunna tashar labarai ya ma tv ɗin zuru, kallo ɗaya zai shaida baya fahimtar ma me ake a labaran.

'Ko me yake damun shi?' ta furta a ranta.

"Mun shirya" ta faɗi ta na tsayuwa gaban shi. Ya ɗago ya kalle su, har ya kauda kai ya kara ɗaga kai ya kalle su. Yadda ta ke riƙe da Ikram yai mashi kama da uwa da ƴa. Girgiza kan shi yai da sauri ya na runtse idanuwan shi da ƙarfi har suna sauya kala.

Ya miƙe yai gaba. Adam ne ya fito daga ɗakin Umma ya gaishe da Nass ya kalli Fatima
"Antinmu unguwa za a ?"

"Eh, Adam"

Ta bashi amsa da murmushinta.

"Za ka fita ne, ana ta baza kamshi?"

Ya yi dariya.

"Aunty ki na gani na wujiga wujiga hankali a tashe ki ce baza kamshi? Duk na kare yawa ne"

Suka sa dariya gaba ɗaya

"Jarabawa ta zan dubo fa ta waec da ta fito"

Gaban ta taji ya faɗi ta zaro ido

"Har ta fito? Nima ina son na duba"

"To shikenan sai in gano mana tare, Allah ya sa muga alkairi"

Ta ce "Ameen" sai da ta rubuta mashi exam card da number sannan ta fita.

Can ta iske Naseer tsaye a gaban mota ya na waya.

"Auntinmu"

Ta ji muryar Yusuf a bayan ta.

"Wannan kwalliya duk ta fitar ce?"

Ta yi dariya.

"Allah ko kun yi kyau irin sosai, gaskiya sai na maku hoto"

Ya faɗi ya na zaro wayarshi

Ta na dariya yai masu hoton, Ikram ma haka. Ta ɗaga ta sama ta na mata wasa ta na kyalkyala dariya akai masu. Ya yi masu kusan kala biyar kafin ta ji karar hon na shirin huda kunnuwan ta ta juya ta tafi ta na wa Yusuf godia.

Bai ce mata komai ba ya tafa motar su ka tafi.
**

A hanyar su ta dawowa ta kowa yayi shiru kamar lokacin zuwan na su. Ta ce

"Ka ji.."

Ya kalleta

"Mu kai Ikram ko shillo ta yi?"

"Ba ki san hanyar ba?"

"Please?"

Yai banza ya kyaleta. Ta na ta gungunai bai ce mata komai ba sai taga ya yi U-turn ya canza hanya. Bata tsammaci zai kai sun ba sai da ta gansu a kofar park din. Da murnar na ta kama murfin kofar ta bude tun bai daidaita parking ba. Ji ta yi an ruko hannun ta, ta waigo suka haɗa ido.

HAYAR SOWhere stories live. Discover now