07

229 19 0
                                    

Ta sha ganin halayen Inna kala-kala duk da ba za ta ce ta saba da su ba domin duk shafin da ta ɓallo sabone a garesu ga kowa ma da ya santa da halinta, don haka ne ma ba ta yanke tsammanin ganin koma meye daga Inna ba amman ba irin yau ba. Ba kamar irin mamaki da firgicin da ta tsomata cikin mintuna biyu kacal ba. Wai ma ta ji abin da Inna ta faɗa yanzun nan kuwa? Ta kalli Inna ta ga ta zuba mata idanu alamun ta na saurarenta ta ce "Eh" alamun gamsuwa da bayananta ta kalli kujerar da Baba ya ke zaune da safiyar yau ya na shan kokon da Fa'iza ce ta siyo musu babu ko haɗin kosai. Ba ta san yaushe maganar ta fara ba, amman za ta iya cewa a jiya bayan sun yi bacci ne, a yau da safe kuma aka dasa abin da kunnuwan ta su ka jiyo kafin fitar shi kawai shi ne

"Ki yi koma me ki ke ganin za ki yi Mariya ko kadan ban yarda da zan cen Auren nan ba haka rana tsaka, idan kin ga ya faru to rai na ne ya bar jikina"

Ba ta san wane auren ba, amman tun da ga lokacin gabanta ke bugawa har zuwa yanzun da Inna ta tusa ta da zancen ta mata miji ta rabu da Safwan.

"Na maki miji ne na nunawa sa a, kaf! Dangina da na babanku babu wanda ya auri kamar shi, a gaba ma ba za'a samu ba tun da sa'ar garemu ne"

Dakyar bakinta ya iya furta

"Me ki ke faɗi haka Inna? Wane irin miji kuma..?"

"Ke da Allah rufe mini baki wawuyar banza kawai, duk bayanin da na gama rattaba miki ki tambaye ni wani wane miji? To ki tsaya ki ji ma wallahi tallahi ba ki isa kawo mini cikas ba. Ki ta shi ki bani wuri ki ka tusani gaba kina kyafta mani idanu kamar ba ke za ji fi kowa jin dadin ba"

Ta rushe da wani kalar kuka ta zame a nan ƙasa ta na harba ƙafa. Inna ta saki baki galala ta na kallon ikon Allah

"Ba ki da hankali kuwa. Ni bayan ma ke a ka zaɓa ai da Fa'iza zan bada tun da ta fiki hankali da sanin abinda ya dace da ita mtww!kuma wallahi ki rufe mani baki idan Safwan ya zo ki sallame shi tun muna shaida juna"

Kukanta ta cigaba da yi ta na tuna yadda Safwan ke mata murmushi da yadda ta je jin shi a ranta amman yanzun rana tsaka a wani ce an sallame shi?  Ta tuna makaranta yadda su ke zama kowa na lissafo makarantar da ya ke son zuwa, abin da zai karanta da gayun da zasu rikayi a matsayinsu na yan jami'a. Yanzu duk sun tashi a banza?

Ba ta tashi da ga kasan ba sai da rana ta fara iskota ga zafi anayi dole ta miƙe ta na fushi da fatan Baba ya dawo ta shige ɗaki ta na jiyo Inna na fadin.

"Da kar ki tashi mana ki ga idan akwai abinda zai canza"

**
Ƙarfe huɗu da rabi na yamma yaro ya kwaɗo sallamar kiran Fatima in ni Safwan, a daidai lokacin da Inna ke ƙokarin shiga banɗaki.

"Ka je ka ce ta na zuwa"

Inna ta faɗawa yaron. Ta ɗaga baki za ta kwadowa Fatima kira sai gata ta fito fuska a koɗe da gani kasan ta sha kuka sai kwallin da ta ranbaɗa a ido da nufin ya rufawa fuskarta asiri.

"Shafaffa da mai. Idan kin je ki sallame shi minti ɗaya na baki ki dawo gidan nan wallahi, ahto kar yan sa ido ma su ɓata lamarin ace an ganki da wani"

Bata ce mata komai ba ta wuce gabanta na faɗuwa duk da ko kusa bata da alamar sallamar Safuwan ɗin. Ta na mashi kalar son nan da ke shiga rai ya zagaye ko ina da duk wata mace ki je alokacin soyayyarta ta fari, irin soyayya da za ka ji in ba shi ba sai rijiya mai kwalabe. A ranta ta ke jin ko mai zai faru ba za ta taɓa barin Safwan ba sai dai Inna ta yankata.

Kamar kullum ya jingina da bangon gidan hannuwanshi zagaye a baya ya na duban hanya. Fuskar shi ta cika da murmushi a lokacin da ya haɗa idanu da muradin ranshi. Murmushin fuskar ya ragu lura da yanayin fuskarta. Cikin kumawa ya ce

"Me ke damunki na ga kamar kin yi kuka?"

Ta yi murmushi ta na jin kamar an yaye damuwarta ne

"Kaina ne ya wuni ciwo"

HAYAR SOTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang