17
Cikin tashin hankali dukkan su suka maida hankulansu wurin. A lokacin Nass ya ji an damko kafaɗunsa ta baya a na raba idanuwansa da nata. Fizge wa ya ke ana jan shi da ƙarfi har zuwa bayan motarsa da ya aje kafin a sake shi.
Da wani kalar kallo ya ke bin su.
"Ka yi hakuri yallaɓai ne ya ce mu maida ka gida cikin salama"
Su ka faɗi su na dan russunawa. Juyawa ya yi wurin da ta ke amman wayam! Babu ko alamaun ta.
Zuly ya ji an kirata da shi. 'Zuly' ya maimaita sunan a kanshi ya na sakin ajiyar zuciya tare da matse idanuwansa. Ya na kallon yadda sauran securities ɗin ke ta zagaye wurin suna dube duben yarinyar. Motar kawai ya shige ya na tunanin abin da ke faruwa da Abbu ya zaɓi boye mashi.
A bakin gate ya iske Abbu bayan sun iso gida. Tamkar ɗan yaro haka Abbu ya damƙi hannunsa har cikin ɗakin shi.
"Me ka ke tunanin ka na yi Naseer?"
Ya faɗi sa'ilin da ya ke sakin hannun shi ya na duban shi ran shi a bace. Ya ci gaba da faɗin
"Ka san hatsarin da za ka iya jefa kanka haka kawai gaba gaɗi ana zancen mutuwa ka kai kanka? Hankali na ke baka son dai ya kwanta kai a rayuwarka ko?"
"Ba haka bane. Kawai ina son sanin me ke faruwa ne?"
Ya faɗi muryarshi cen kasa.
"Zauna"
Abbu ya fada mashi. Ya zauna ba musu. Shima Abbun zaman ya yi.
"Ka ga ɗaya daga cikin dalillan da ya sa na ke son ka tsaya da kafarka a kamfani ko? Duk waɗan nan abubuwan ba za ka fahimce su ba ko da na faɗa maka, ka na dai zaune haka a gida"
"Me yasa za ayi kisa a can?"
Ya tsallake dukkan bayanan Abbun. Shi kawai ya na son jin dalilin ne.
"Ni ma ban san dalili ba Nass, a ko ina za a iya yin kisa in dai wanda ake hari na wurin. Ka sani Hotel wuri ne na jama'a kowa zai iya zuwa don haka ne kuma komai zai iya faruwa"
"Me yasa ba za a kira yansanda ba Abbu? Meyasa?"
"Hakan ba zai taɓa faruwa ba Naseer, sunan mu ne zai baci..."
Da mamaki Ya ke kallon shi. Abbu ya girgiza kai.
"Eh kwarai sunan mu zai ɓaci, ba mu muka yi kisan ba, a takaice ma ba a gama tantance victim ɗin ba amman ai a Hotel ɗin mu ne. Idan labarin nan ya fita ƙofar wurin ta wa yan jaridar garin nan kaɗan, ga makiya da ke son ganin mun durkushe. Shi yasa ko da wasa ba zan taɓa bari hakan ta faru ba."
Shiru ya yi kanshi ƙasa na wani lokaci kafin ya ce
"Yanzu Abbu saboda sunanka kar ya ɓaci shine dalilin da za ka ɗauki fitar ran wani da wasa haka? Rai fa Abbu? Shike nan shi an kashe banza kenan maganar ta mutu har abada kai kuma darajar ka na nan?"
"Naseer!"
Ya kira shi cikin tsawa. Ya dade ya na kallon shi kafin ya yi ajiyar zuciya ya sassauta murya
"Shi yasa na ce ba za ka gane ba ai, ba zamu bari yan sanda su san meke faruwa ba domin bamu da amsoshin ba su da sauran yan jarida. Shisa zamu gama namu binciken mu gano makashin tun da ga shigowar shi har zuwa fita. A lokacin ne mu ke da dukkan baya nai, ka fahimce ni?"
Ya gyada kai a ranshi dai ya na tunanin anya wannan shawarar ta Abbu za ta ba da kyau?
"Shi ke nan Abbu zan je in kwanta"
"Yawwa to ko kai fa, ka yanke shawarar lokacin fara aikinka ina son in ga ka fara zuwa office kafin in bar kasar nan in san waye na barwa dukiyata"
Ya gyada kai kawai ya buda kofar ya fita.
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!