A lokacin da dukkan dangi da ma duk wanda aka gayyata suke tsakar gida su na hada-hada da shinkafa da tuwon biki fuskarsu washe an cika gidan da shewa da surutai na mata, a lokacin ita take ƙumshe a ɗaki da zungureriyar takardar da ake kira da cardboard paper. Zanen gida ne ciki da wajenshi da abinda ya ƙunsa.
'Wannan shi ne gidan Dikko. Idan ki ka bi komai a tsanake za ki fahimci dalilin baki zanen idan kin shiga gidan. Komai da za ki gani a kwaishi a cen ba sai kin tambayi kowa ba'
Haka Mom ta faɗa lokacin da ta bata zanen. Tun daga ranar kuma ta ke bin ta da kallo ta na karanta sunayen duk wani abu da ta gani ta na hardacewa har zuwa yau da ya zamana ranar aurenta.
'Aure'
Ta maimaita kalmar wata yar guntuwar dariya na zo mata da ita kanta bata san ma'anar ta ba. Ba za ta ce ta na farinciki ba tun da ba masoyinta za ta aura ba, haka kuma ba za ta ce ta na baƙin ciki ba idan ta tuna ta yi ne don ɗaukewa Baba ɗawainiyar katatunta. Haka ya sa ta ke karahan kadahan ba ta jin komai a ranta game da auren.
Agogon hannunta ta kalla ƙarfe sha biyu da rabi na rana. Hakan na nufin saura mintuna talatin a ɗaura aurenta...A cikin mintunan ne kuma akalar rayuwarta za ta canza gaba ɗaya!
*
Shigowar Fa'iza ya saka ta naɗe takardar ta cusa a cikin jikkarta."Innalillahi wai duk abin nan ki na cikin ɗaki?"
Fa'iza ta faɗi cike da mamakin sauyawar Fatima lokaci ɗaya.
"Bikin ki fa ake. Ki fito ni dai za muyi hotuna da kawayena a gidan Maman Hafsat nan bayan layi"
"Don Allah Fa'iza ba za ki bar ni in huta ba? Ni ban san duk lokacin da ki ka hada wannan gayyar ta ki ba"
"In ke baki gayyato na ki kawayen ba ni ga nawu sun isheki, daman ina amarya ta ga hutu?"
Haka ta ja hannunta su ka kutsa cikin mutanen da ke ta tsokanarta har suka fice.
*******************"Ni na rasa wane kalar aiki ne haka tsakar rana da za a tare hanya"
Cewar Baba cikin damuwa ƙwarai ya na kallon agogon da aka haɗo mashi a kayan shi na ɗaurin aure daga wurin Mom. Kafin Baba Isa wanda shi ne madaurin auren ya yi magana wayar Baba ta dauki ƙara da ta saka duk su ka zura mashi ido cikin jimami.
"Ya zo direban tun ɗazu ma ya ɗakko mu wallahi hanyar ce a ka rufe wai ana aiki, mun zo komawa ma mu sake hanya yan sanda ne ke rikici da wasu an tare hanyar ba wurin wucewa"
Ya kai karshen maganar cikin rashin madafa ko sanin abin yi. Ɗaurin aure dai a yanzu haka mintuna goma suka rage uban amarya da madaurin aure kawai ake jira amman babu su. Shi uban ango da ango tashin jirginsu nan da minti arba'in ne. Haka aka fada wa Baba tun farko, shi yasa ma aka saka daurin auren karfe daya ta yadda ana gamawa za su wuce amarya kuma bayan kwana ukku akai ta wurin mijinta.
Baba duk ya damu ya na ganin rashin kyautawar da yai masu na jira duk da ba laifin shi bane, amman jira irin wannan ba shi da daɗi tun da ga shi har direba aka turo ya dauke su duk dan kawai a saukaka abun.
Alokacin da aka zo mashi da shawarar wurin ɗaurin auren shi da kanshi ya basu zaɓi da su zaɓa in da zai fi yi masu kusa da uzurinsu. Don shi mutum ne mai girmama duk wani uzuri na wasu.
"Za ku iya wakiltar amarya a madadinmu?"
Cewar Baba da yasa su Baba Umar kallon shi da sauri. Ya gyada masu kai ya na ci gaba da magana da na cikin wayar
"Idan ba matsala ayi hakan kar a katse masu tafiya irin wannan in ya so idan mun iso sai a gaggaisa da juna.
To shikenan ni ke da godia, Allah ya saka da alkairi"

YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!