10

255 17 0
                                    

           ****************
Abubuwa sukan zo mana kwatsam a rayuwa da bamu tsammata ba, kamar kaddarorin da muke rayuwa da su, wasu su zo ta daɗi wasu akasin haka, a hakan kuma zamu tare su hannu bibbiyu mu godewa ubangijinmu. Hakan ce ta faru ga Fatima, tsawon rayuwarta ko ma ta ce a sati ɗaya da ya wuce ba ta tsammaci rayuwarta za ta juya har haka ba, wai Aure. Aurenta ne a cikin kwana ukku masu zuwa. Idan wani ya hasaso mata faruwar hakan a kwananikin baya, kai tsaye za ta ƙaryata hakan kanta tsaye sannan ta bigi gaba ta ce Baba ya tsaya mata, ya tsaya mata akan ra'ayinta da ya zo kala ɗaya da nashi akan karatunta. Sai dai lokaci ɗaya  kaddararta rayuwa ta iso mata, kuma ba ta barta da wani zaɓin da ya wuce ta bita sau da ƙafa ba.

Hawayen da ya ziraro mata ta saka hannu ta share ta na ƙare matse takardar da Safwan ya aiko mata da ita. Takardar da ta yi silar zubda duk wasu makaman yaƙinta na ganin cewa bata auri wanda a ke shirin ƙwakwaba mata ba, ba ta bi wata hanyar da za ta nisanta ta da ga burin makarantarta ba. Shi kan shi Safwan ɗin bai barta da wani zaɓin da ya wuce ta yi auren jeka ka dawo ɗin ba, za ta yi auren kuma za ta jira shi kamar yarda ya buƙata.

Ta ƙara warware takardar ta karanta a karo na ba adadi tun daga ranar da ya aiko da ita alokacin da ta ke fitowa daga gidan su Zainabu, zuwa yau. Bayan ta gama ne ta yi murmushi mai tafe da hawayen kewa ta ce

"Ni taka ce Safwan har abada!"

Ta linke takardai sannan ta miƙe da nufin maidata ma'ajiyar da ta tanadar mata a cikin kayan sakawarta. Faɗowar wasu takardun ya saka ta kalli ƙasa ta na binsu da ido. Sai da ta kai wasikar ta adana kafin ta dawo ta kwashi dogayen papers ɗin guda ukku ta na kallo.

Wadan nan su ne rayuwarta!
Waɗannan su ne matakan duk wasu dalilin da zai bata damar kasancewarta da Safwan.
Burikanta sun ta'allaka ne a kansu!
Su ɗin ne kuma ke riƙe da martabar danginta gaba ɗaya!  Sannan Ta ƙurawa ƙasan takarda ɗaya dake sama in da ta yi sign ido, maida biyu daga cikin takardun wurin Mum na nufin amincewa da duk waɗan nan abubuwan da ta lissafo.

Sharaɗi na farko; 'Babu gardama a duk wani abun da zai biyo baya!'

Na biyu;'Babu wanda zai gano gidan da za ki aure bare ki saka ran ganin wani na ki har lokacin da harkallarmu za ta ƙare!'

Na ukku;'........

Ta rufe idonta da karfi ta na damƙe papers ɗin gabanta na faɗuwa. Ita ɗin duk za ta iya wannan? Sharuddan da yawa. Menene matsayinta kenan a wurin baba?

'Maƙaryaciya!'

Wanis sashe na zuciyarta ya faɗa mata. Tabbas kuwa amincewa da duka wannan na nufin ta zama babbar maƙaryaciya a wurin Baba, duk da amincewar shi ce ga auren amman ai bai san manufar ba. Haka ya na nufin ta gina wata tazara ta sirri tsakaninta da Baba. Anya za ta iya duka wannan? Karyukan ma kaɗai da aka shinfida mashi a ido sun isa, yaudarar ta yi yawa. Ya na ganin abubuwa ne ba a yadda su ke ba. Tun daga manema auren Fatima har angon da ake gwada mashi duk ƙarya ce!

Ƙarar wayar da bata saba da ita ba a cikin kwanakin nan ta cika ɗakin. A razane ta dawo hayyacinta saboda rashin sabo. Ta riga ta san mai kiran, Mum ce ita ta bata wayar kuma ita kaɗai ke kiranta tun bayan kyautar. Rashin kwanciyar hankalin da ta ke ciki bai sakata zumuɗin wayar ko kwashe lambobin ƙawayenta da me cikin slum book dinta ba. Mafi lokutta ma Fa'iza ke amfani da wayar ta na games da yiwa yar tsana kwalliya kamar yadda ta ga masu wayar ajinsu na yi.

Jiki a sanyaye ta ɗaga kiran.

"Ki fito ina waje"

Abin da Mum ɗin ta faɗa kenan da kashe kiran.

Da wankanta daman duk da hakan ba zai sa idan sun je in da zasu a saka ta ƙarayin wani ba a kalolin ruwaye masu kamshi daban-daban da a yanzn har jikinta ya fara dauka. Fa'iza kan ce mata

HAYAR SOWhere stories live. Discover now