23

252 17 2
                                    

Tsaye ya ke cikin ɗakin ya juya baya yana fuskantar mutanen waje daga cikin tagar ɗakin, hannuwansa biyu duka a jikin ƙarafunan tagar. A yanzu kuma bai san kalar binciken da zai yi ba ko ta ina zai koma. Dr. Ya riga ya tabbatar mashi da a awon da a kayi Thallium poison ne daga cikin plate ɗin, wanda bashi da kala kuma bashi da ɗandano don haka ne ita ba zata gane an saka mata wani abu ba. Tutsiyen da ya dinga yi wa masu girkin ne duk wata shigowar da zai yi ya nemi ɗaya daga cikin su da suka kira Samantha, ya rasa. Hakan kuma ya bashi tabbacin koma meye ta na da masaniya a kai, koma ita ce aka saka. Ta wurinta ne kawai zai gano gaskiya, babu ita. Kwana uku kenan duk wani binciken in da zai same ta yayi bai samu ba, har guardian ɗin ta ya sa aka nemo ya bincike shi har a wurin yan sanda amman babu labarin ta. Fatima ko yatsanta bata motsa a cikin kwana na ukkun nan ba. Ga Abbu baya ƙasar. Hannun shi na hagu ya banbaro daga karfen tagar ya daki tagar da karfi ya na sace iskar bakin shi dake haɗe da huci. Juyowa yayi ya kalle ta, kamar dai ko yaushe idanun ta manne da juna a rufe. Ya taka ƙafafuwanshi ya isa gaban gadon ya na zama a kujerar da ke fuskantar ta. Wani kalar tausayin yarinyar ya ke ji, a yan shekarun nan nata da yarintar nan har wani yake tunanin cutar da ita. Sam-sam mutane basu da hankali, idan ma don shi ne basu kula ba ta kanta ya ke ba? Ba suyi tunanin ta yi mashi kankantar da zai kalle ta da sunan mata ba? Meyasa? Mayasa sai ita? Hannun shi ya ƙara ɗagawa ya buga da ƙarfen gadon cikin zafin rasa ta in da tambayoyin shi za su ɓullo.

"Za ka ƙarasani ne?"

Ya jiyo muryar ta can ciki dakyar. Da sauri ya kalle ta, tana ƙokarin bude ido suna lumshewa da kansu.

"Are you okay?" Ya faɗi ya na taɓa goshinta.

"Ru...wa"

Ta faɗi a rarrabe ta na maida numfashi. Da sauri ya juya ya dauki ruwa ya balle murfin robar, ya tallabota a hankali ta yarda ba za ta kware ba ya bata ruwan. Da kaɗan kaɗan ta dinga sha har ta janye kanta, ya rufe robar ya aje. Da sauri ya juya don ya kira likita.

Bai daɗe da fita ba su ka shigo da likitan, ya dudduba ta da yan tambayoyi. Ya juyo ya kalli Nass

"Mu je sai in rubuta maka magungunan ka anso, ta fara cin abinci sai ta sha maganin"

Ya gyaɗa kai. Shigowar Hajja da Yaseerah ya saka shi tsayawa yiwa Hajjar bayani a takaice ya fice. Da sauri Yaseerah ta karasa ta na mata sannu da jiki.

"Sannu. Sannu Fatimah, kin sha wahala. Allah ya yi miki sakayya akan ko waye ke son ganin karahen rayuwarki"

"Ameen Hajja"

Yaseerah ta amsawa Hajjah. Ta cigaba

"Ni wannan lamari na gidan nan na bani tsoro, ai na waje dai takanas ba zai zo ya cutar da wani a cikin gidan su ba. To kuwa idan hakane a cikin gidan za a samo mai laifi. Allah ya kaimu Dikkon ya dawo to, sai ya san matakin da zai ɗauka wannan magana i ba ta yin shiru bace."

Ta dubi Yaseerah

"Har yanzu bai kira ba?"

"Eh Hajjah, ban sani ba ko ya kira Mom. Amman da wuya gaskiya don da ta yi maganar."

"Shi kenan, ina nan ina jiran kiran na shi ma. Gara ya dawo a yi mai yiwuwa sai ya koma idan da hali tun da idan ya tafi ba nan kusa ya ke dawowa ba."

"Gaskiya dai"

Yaseerah ta amsa.

Naseer ne ya shigo da ledoji a hannun shi ya a za a bedside.

"Ka samo mata abin da za ta ci ko? Ai Allah abin godia ban zaci ta tashi ba da ban taho haka ba, sai in shiga in dafa mata wani abun da kaina ma tun da gidan ya zama abin tsoro"

Gyaɗa kan shi kawai ya yi sa'ilin da ya gama ware ledar maganin daban.  Alokacin aka ƙwankwasa ɗakin ya je ya buɗe tare da ansar flakes ɗin hannun yaron. Ruwan zafi ne ya sa aka zuba mashi a wani gidan cin abinci da bashi da nisa a asibitin. Ya san wurin da mutanen su sosai tun ma alokacin da Nadrah na da rai suna zuwa, musamman idan ya kawo ta awo sai ta ce a tsaya a siya Fizza ko wani abu. Sun sha zama a cen su ci wani lokacin suyi takeaway. Tun bayan rasuwarta bai kara taka kafarshi wurin ba sai yau.

HAYAR SOTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang