Inna ce tsaye riƙe da roba mai faɗi shaƙe da abincin ƙasan tukunya da aka jujjuye a kuloli ta kankaro tukunyar, ta na miƙawa Fa'iza
"Za ki ansa ki juye a ledar ne kokuwa sai na gaura miki mari? Kin taɓa cin irin shi a gidan ubanki ne iye? Na ce kim taɓa ci? Wannan tsinannen faɗin ran naki babu in da zai kai ki in gaya miki, idan ki na son canza rayuwarki ne to sai ki samo miji mai lasisi ki aura ki huta mu ma din mu huta. Ki juye shi ki kulle ki hada da sauran idan mun koma gida duk bazasu za'a yi su bushe mun kwashi sati ai muna ci har uban naku mai matacciyar zuciya"
Fatima ta miƙa hannu don ta amshi robar abincin tun kafin Inna ta gama tara masu jama'a, don babu abin da ya shalleta da a sirinsu da take yadawa a bainar jama'a ita ba ruwanta.
"Ban ce ki ansa ba ita ɗin da ke kunyar aga ta na tara abinci ita ce zata juye shi ta tara aikin ai ya ƙare yanzun zuwa zan yi in anso kason mu wanda aka ware mana mu raba."
Fatima ta kalli Fa'iza da ke shirin fashewa ta kalli Inna ma ga mutane sun fara giftasu ana kallonsu ta yi hanzarin amsar robar ta ɗaura a saman kanta.
"Ni dai ban ga abin tashin hankali a nan ba, idan akwai wanda na ke zaman shi to sai yai mani dariyar na tattara abinci a leda, ni dai nan bani kunyar kowa"
Ta kalli Fa'iza da ke kallonta a mamakance duk da dai ta san halin Fatimar da idanun jama'a bai shalleta ba ta kuma san duk saboda ita ne ta yi hakan, bata dai ce komai ba ta kyale su daga ita har Innar. Ah to babu mai sakawa a rainata haka kawai don ta zo a talaka, ta ma fi ganin laifin Fatimar da ke yin wasu abubuwan kawai saboda Innar, Inna kuma ba wai za ta canza bane.
Mom da ke tsaye da ga bayan tagar kitchen ɗin ta na bada umarni tamkar a gidanta ne bikin, duk ta yi ruwa ta yi tsaki, ta gama ƙarewa Fatima kallon tsaf sannan ta kalli Fa'iza ma da Inna ta yi murmushi. Murmushin da ke gaya mata anzo wurin, yadda su ka tattauna kalar yarinyar da suke son samun kuma su kai na'am da hakan tuni wannan plan ɗin ya ruguje a cikin kan Mom wani sabo ya zo mata kallo ɗaya da ta yiwa idanun Inna tun bayan tsayuwarta a wurin, ba ta tabbatar da ta sake shawara mai kyau ba sai da ta saurari kaf maganganunsu tukun. Tabbas za ta bibiye su daga nan har zuwa lokacin da mafarkinta zai zama gaskiya!
Inna ta ciro wayarta da ke faman ruri ta cika wurin da ƙara ta miƙawa Fa'iza duba nan na san ba zai wuce ƙawayenku ba ne. Fa'iza ta karɓi wayar ta na bin lambar da kallon rashin sani kafin ta ɗaga kiran ta gi sallama.
"Au! Safwan ina wuni.." ta ɗan jinkirta kafin ta juya ta na kallon in da Fatima ke ɗuke ta na ɗaure baƙar ledar da ta juye abincin.
"To ga ta"
Fatima ta amshi wayar gabanta na faɗuwa. A karo na farko kenan da Safwan ya taɓa kiranta duk da ya dade da ansar lambar Inna.
"Ki na ina ne? Ina ƙofar gidanku yanzu haka" ya faɗa bayan sun gaisa.
"Laa mun fita fa tun safe ma..muna GRA za ka zo?"
Ya ɗan yi shiru kafin ya ce
"Bari kawai in jiraki bana son shiga unguwar"
Ba ta tambayeshi dalili ba ta ce "To sai mun dawo ɗin" ta kashe wayar.
Alokacin idanunta suka sauka cikin na matar. matar da ta yi silar canja rayuwarta gaba ɗaya!
********** ************
"Ka sawa ranka salama don Allah ka saki ranka haka nan.."
"Wannan kucakar!" Yakatse umar. Ya juya ya kalli Saifullah a harzuƙe ya ce
"Ni ne zata faɗawa shaye-shaye na yo? Ni? Ka kuwa ganta Saif? Idan na rantse ba zan yi kaffara ba idan ta tsaya gabanka za kayi amai"
DU LIEST GERADE
HAYAR SO
Aktuelle LiteraturBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!