11

196 17 0
                                    

A madubin gabanta ta ke duban kanta ta na kasa janye idanuwanta daga furkar da ta zama bakuwa a gareta. Light make-up ne akai mata amman  zanen fuskarta ya fito tar, an fito da komai da ya saka ta yi wani kyau na ban mamaki. Don za ta iya rantsewa ko hodar ɗari biyar ba ta taɓa shafawa fuskarta ba a tsawon rayuwarta. Kayan jikinta ta ke kallo straight gown ce ta atamfa green mai manyan bakaken patterns da aka bi da stones suka ƙara kawata atamfar da dinkin, akai mata daurin zara buhari. Aka bata bakin gyale dan ƙarami da bakin takalma masu tsini sosai da su kai bala'in kyau da dinkin jikinta.

"Ki saka wadannan"

Matar da ta yi mata kwalliya ta ce ta na miƙa mata zobuna guda biyu na gold. Ta ansa ta saka.

"Ko za kiyi mini hoto don Allah?"

Fatima ta tambayeta. Ta na son idan ta koma gida ta gwadawa Fa'iza kwalliyart ta san zata burgeta sosai don wadan da aka yi mata kwanaki da za a kaiwa Abbu ita bata gansu ba ma.

"To amman da wayarki don Hajiya ta ce kar muyi maki hoto"

Wayarta ta mika mata sannan ta dinga gyara zama ana bata style ana hoton. Ta ansa ta na gani har sai da Mom ta kira ta ce idan an gama su fito. Kamar yadda aka koya mata tafiya haka Mom ta bata umarnin ta dingayi a ko yaushe daga yanzu har zuwa ranar bikin don ta saba ta bi jikinta.
  Suna fitowa Mom ta wata mota ta ce

"Ki je Yayanki Junaid ya na ciki ya na jiranki. Kin hardace duk abin da na rubuta miki ko"

Ta gyada kai.

Daga nesa Junaid ke hango su idonsa akan Fatima. Bai ankara ba ya ji ta dan buga glass din motar. Ya juyo ya buɗe mata gidan gaba ta shiga. Idanuwanshi ya lumshe ya na shakar kamshin turarenta da ya gauraye motar.

"Sannu"

Ta ce mishi ta na kallonshi.

"Sannu?"

Ya maimaita ya na kare mata kallo. 'lalai yarinyar nan' ya faɗa a ranshi. Yayi murmushi ya ce

"Kin manta yayanki ne ni kike ce mini sannu?"

"Bamu shiga filin wasan ba tukunna"

Ta faɗi mashi kanta tsaye.

Ya jinjina kai ya na mamakin tsaurin idon yarinyar.

Ya ɗan dage kafaɗa ya ce

"Haka ne"

Ya tada motar. Kallon shi ta karayi ta ce

"Me yasa na ke jin kamar mun taɓa haɗuwa?"

Dariya ya saki ya ce

"Ni?"

Ta ce "Eh" ta na tunanin tasan muryar koma a ina ne. Shi kuma aranshi mamakin yadda ta ke kokarin gane muryarsa ta ke a zuwa biyu kacal da yayi gidan su cikin duhu a matsayin Nass.

"Yammata da dama sun sha faɗa mun haka, ban sani ba ko salon ku ne a kan gayu iri na idan kun ɗasa?

Wani kallo ta yi mashi mai kama da harara kafin ta juya kanta gefe.

"Kin ji"

"Kar ka mance matsayinka Yayana kake"

Ta faɗi ba tare da ta juyo ba.

"Ba mu isa filin wasan ba ai. Haka ki ka faɗa ba?"

Ta kalle shi ya kashe mata ido. Ta juya haushin shi kamar ya kasheta.  Dariya kawai ya yi, ya yanki titin da kai tsaye zai kai shi 'Dikko real estate solution' in da za su haɗu da Abbu.
            *****************

"Ikram!"

Ya buga mata tsawar da ta ruɗata ta saki littafin da ta ɗakko ta na e shirin yagawa. Ta saki wani kalar razanannen kuka.

HAYAR SOTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon