Ya kama murfin motar hannunsa na rawa ya buɗe. Fitowar shi ta yi daidai da tsayuwar wata katuwar mota, a cikin ƙasa da yan sakanni motar ta wuce tare da ita da mutanen cikin motar da suka damƙeta suna rirriketa. Ta na miƙo mashi hannuwa da hawaye motar ta wuce.
"Aa...Aaa Nadrah"
Ya dinga maimaitawa da wani kalar tashin hankalin da bai taɓa kawo a kwai wanzuwarshi duniya ba. Da wani kalar sauri ya shiga motar ya na tadawa ya bi bayan babbar motar da gudu. Fatima duk ta rirrike duk in da hannunta zai iya kaiwa a cikin motar ta rike cikin tashin hankali ta ke kallon shi.
"Ina zaka? Ina za ka kaimu? Wacece? Suwaye wai"?
Bai ma san me ta ke faɗi ba kawai gudu yawa iyakar iyawarshi na tsawon lokacin da bai san iyakar shi ba, da ya kasa fahimtar motar ta daɗe da ɓace mashi.
Da kyar da taimakon motocin da ke gaban shi ya fahimci ma motar da ya ke bin ba ta nan yai parking bakin titin. Fitowa yayi ya na takawa da hanga ko ina duk ya fita hayyacin shi. Fatima ma fitowar ta yi ta zo ta dafa shi.
"Papa"
Ta kira shi a tsorace da yadda ta ganshi. Juyowa yayi ya na kallonta.
"Nadrah ce Zahra, ita na gani. Kin ganta kema ko?"
"Nadrah" ta nanata sunan mai sunan ta dawo mata cikin kai. Gabanta yai wata kalar faɗuwa. Ai ance mata ta rasu ko? Meke faruwa?
"Mu je gida to..."
"Gida? Zan je gida in kyale ta? Baki ganta da jini ba? Aa..zan nemo ta"
Bata ga alamun zai saurare ta ba ga rana ma tayi sosai yunwar da ta fara ji ma duk ta ɓace don ma akwai sanyin ruwan da aka gama. Komawa ta yi cikin motar ta kira Mom. Komai ta faɗa mata ta samu wani symbol na kusa da su ta faɗa mata in da suke. Haka ta yi mashi zuru ta na bin shi duk in da ya jefa kafarshi suje su dawo. Ta rasa me za ta ce mashi ya hakura su tafi.
Ba karamar wahala suka sha ba kafin securities ɗin Abbu da Mom ta aiko su iso in da suke. Haka suka tisa shi gaba babu yadda zai yi da su, don in dai Abbu ya bada order to koma waye babu ruwansu sai in da karfin su ya kare in yaso daga baya su bada hakuri.
************************Duk wasu kwanakin da suka biyo bayan dawowarsu gida basu zamo mata masu daɗi ba. Yau kwanan su huɗu kenan amman kullum ranar Allah da duk wasu dakikun da ke wucewa bakin shi dauke da sunan Nadrah ya ke tafiya. Da aka yi waya da Abbu ne ya ce kar a saki a bar shi ya fita gidan kwata-kwata zai yi kokarin hada komai ya dawo a sati mai zuwa. Yanzu haka ƙokarin fitan ya ke da zummar duk abin da zai faru sai dai ya faru amman zai fita ya nemo ta. Ta gaji. Ta gaji da duk wannan abubuwan, ba ta son ganin shi a halin da ya ke ciki ko baccin kirki baya yi. Shiyasa ta mike ta biyo shi da sauri. Har ya sauka ƙasa ya kai tsakiyar falon ta sha gabanshi ta na haki.
"Ka natsu don Allah, idan har ka cigaba da sakawa ran ka ita ɗin ce ba zaka taɓa wuce wurin nan ba. Wanda ya mutu ya mutu baya dawowa!"
Ta faɗi da ƙarfi ta na jijjigashi da fatan zai dawo hayyacinshi.
"Ni na gani da ido na, ita ce! Zan rantse miki in kara rantsewar ta dawo, ko ba'a dawowa ita ta dawo.."
"Ƙarya ce! Yaudara ce! Ba gaskiya bane..duk hasashen zuciyarka ne don Allah ka saurare ni..."
Ya tunkuɗata da ƙarfi ta faɗi kanta ya daki Centre table ta faɗi a wurin cikin jini babu numfashi.
"Ya kashe ta!"
Wata murya da bai tantance mai ita ba ta ratsa kunnuwan shi.
"Jama'a kashe ta yayi ko? Ku fito ni Zinatu na ga ta kaina"
![](https://img.wattpad.com/cover/270528964-288-k829669.jpg)
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!