18

206 18 2
                                    

Gwangwanin maltinar ta ƙara kafawa a baki a karo na ukku ta kurɓa. Ta ɗago gwangwanin ta kalla ta na jin yan hade-haɗen da ta zuba sun mata yadda ta ke so. Ƙara kurba ta yi kafin ta aje ta aje taburin gabanta da ke manne a gefen ƙaton madubin da ya dire har ƙasa ta na mitsi-mitsi da idanuwanta cikin tunani.

Cikin yan dakikun kallon da ya ke mata ta gama kwashe surar fuskar shi tsaf a kwakwalwar ta. Ƙare matse idon ta yi sa'ilin da ta kai yatsunta cikin dumbuzezen gashinta da ya ke a kwance kuma a baje, ta sosa. Kawai bayanai ta ke so a kan shi da shi ɗin ma gaba ɗaya da take fatan ƙara jefa ƙwayar idanunta a kyakkyawar fuskarshi.

Tun bayan da suka bar wurin ta ke ba kwakwalwar ta wahalar in da za ta nemo shi, amman kowa ta tambaya a cikin abokan huɗɗarta bai san shi ba, asali ma basu ganshi ba a lokacin saboda ta kansu su ke su samu damar barin Hotel din ba tare da an kama ta ba.
Duk yadda ta ke zaton abun da sauƙi kamar yarda su ke samo bayanan su amman sam shi bai zo da sauƙi ba.

'ka cancanta' ta faɗi a fili. Sai kuma ta buga ƙafa cikin alamun gajiya da rashin madafa ta fara hautsina gashin kanta.

"Layla!"

Ta ɗago manyan idanun ta da kwalli eyeliner da mascara suka haɗu suka dame sama da ƙasan su ta jefa mashi wani kallo

"Me?"

"Zuly na ce"

Ta rufe idon ta buɗe sannan ta saka hannu ta maida gashin da ya zubo a fuska baya.

"Meye?"

"A kwai taro da Black shadow goma da rabi na dare, kin kashe wayoyinki ana ta neman ki"

Ta juyo ta ɗauki gwangwanin maltinar ta kafa baki. Sai da ta zuƙe shi tass ta matse gwangwanin ya molaƙe ta wurga mashi a fuska, sannan ta ɗaga yatsa ta nuna mashi ƙofar fita. Ba musu ya fita.

Madubi ta ke kallo yadda duk fuskarta ta damalmale gefe da gefen bakinta duk jan jambakinta ne a dame gaba ɗaya ta yi kamar aljana. Miƙewa ta yi tsaye ta yi kwallo da stool ɗin da ta tashi bisa. Ta na ganin dishi-dishi ta isa gado ta faɗa rub da ciki idanuwanta na rufewa.

        *****************

Ta kasa samun natsuwa tun da ta farka, ita dai Umma ta ɓallo mata ruwa. Jiya da ƙyar bacci ya ɗauketa shima don an mashi laƙabi da ɓarawo. Gashi Mom ba ta ce komai ba kuma ai ta san bata iya ba. Wayarta ta ɗauka ta kunna data duk da ba kowa ta aje a whatsapp ɗin ba, don Fa'iza ce ma ta saka mata shi a yan kwana biyun da ta yi da wayar a gida. Har wani group ta sa aka saka ta a cewarta na yan ajinsu ne da ita bata ga amfanin shi ba tun da kullum makarantar ta ke zuwa. Rashin abin yi yasa ta ji leƙawa group ɗin duk da ba wanda ta sani.

Tsulum ta ga wani group ɗin da sunan makarantarsu da wasu lambobin ma duk an mata magana. Shigowar sakonnin ba tsayawa ya saka ta aje wayar.

"Idan ba za ki nutsu wuri ɗaya ba ki fita falo, kin ishe ni da tsuminiya"

Ta ji maganar shi ba zato. Hararo wurin da ya ke ta yi duk da ba ganinta ya ke ba, don akwai tazara sosai tsakanin kujerar da ta zama tata da gadon shi da ya ke kwance.

"Wannan ai rigima ce"

Ta faɗi ta na turo baki.

"Kika ce?"

"Ban ce komai ba"

Bai ƙara magana ba. Har ta ɗauki wayarta ba za to ta ji ya ce

"Idan ba ki iya girkin ba dole sai kin yi? Ko an maki dole ne?"

"To ba ance in yi ba?"

Ta faɗi kamar za ta yi kuka.

"Ba ki da hankali"

HAYAR SOWhere stories live. Discover now