25th May, 2021
~~~~~
GGSS MANIGaba ɗaya makarantar a harmutse ta ke da hada-hadar ɗalibai kowace area da cikin hostels a yamutse su ke a dalilin shirye-shiryen tafiya gida a gobe da ta kama ranar candy. Kowacce ka gani fuskarta washe cike da murna yayinda mafi yawan yaran kuma(juniors) ke cike da alhinin rabuwa da su,musamman masu yayyai a ciki.
"Ba fa haka aka ce a yi ba a wurin!"
Muryar Fatima ta fito cikin tsiwa da gundira ga yadda ƙawarta Maryam ke cike slum book ɗinta da ta sha zama ta tsara duk abubuwan da za a cike mata. Su dukansu suna zaune ne a tudunkar gaban ɗakinsu, hannun Fatima da ƙunshi ta na jiran ya sha iska. Maryam ta saki dariyar shakiyanci duk da yadda ta ga Fatima ta haɗe rai kuwa. Ta ce
"Me zan rubuta wuri?"
"Maryam a je mini abuna"
Kawai ta faɗi ta kauda kanta gefe.
"Haba sorry mana ƙawata, Allah da gaske ban kula ba ne, ke ce kika ce dole ni zan cike a ƙarshe fa ni kuma wahalar komawa baya na ke ji in gano yadda kika tsara abunki. Yi hakuri yau ai babu faɗa bari na kece papper na sake"
Ta yage sannan ta buɗe sabuwa ta fara.
'Nan Jokes za ki rubuta,kar ya wuce layi shidda'
'Nan waƙar da ki ka fi so'
'yawwa saura well wishes'
Haka Fatima ta dinga leƙa kanta ta na faɗa mata har ta gama cikewa. A lokacin kuma ƙunshinta ya bushe ta wanke sannan ta kai slum book ɗin cikin tsohuwar ghana must go ɗinta da ta yi parking kayanta, ta adana.
Ƙagare ta ke gobe ta yi su rubuta jarabawar ƙarshe su ta fi gida. Za ta ga Baba ta ga Fa'iza da Inna. Babban abin da ke mata daɗi yadda za ta koma ta haɗu da Safwan, wata ƙila yanzu ne zai faɗi mata yadda ya ke sonta kamar yadda suka tsammata da kawarta Hauwa.
Safwan saurayi ne ɗan gayu ga tsabta da iya kwalliya. A gidan yayanshi da ke nan unguwarsu ya ke zaune ya na karatu a FCE. Tun wani hutun da suka je na ƙarshe ta haɗu dashi su ke mutunci sama-sama ya ke matukar birgeta har a ke zaton ko soyayya suke, abin da ya ɗaga fatanta kenan. Shi kuma bai taɓa cewa ya na sonta ba shine da Hauwar ta biyo Inna visiting ta ke bata labarin yadda kullum ta ga safwan sai ya tambayi kwanakin da suka ragewa Fatimar ta dawo. Wannan ya sa su duka su ke zaton lokacin ne zai ce ya na sonta.
"Wai tunanin me ki ke ne? Ki yi sauri gashi cen an fara kiɗi area blue house"
Cewar Maryam da ta saka Fatima saurin zuge jikkar ta miƙe.
Haka su ka wuni gararamba da rawa tsakar makaranta har dare, daren da sai da ya tsaga su ka kwanta a gajiye duk da hakan sun bar wasu ɗaliban na kujiba-kujibarsu da koke-koken bankwana.
******. *****Wani dogon lumfashi ta ja ta dire ta na shaƙar iskar wajen makarantar. Duk da kewar da ta ke ji ta rabuwa da ƙawaye bai hanata jin kamar ta fito da ga keji bane tsabar daɗewar da su kayi ba tare da hutu ba saboda zaman camping da na extension. Sai da ta gama shaƙe shaƙen iskan ta ga ana ta zuwa ɗaukar kowa a na watsewa a nan ta fara baza idon neman baba, domin kuwa alƙawari ne yai mata na zuwa ɗaukarta ranar candy.
Karo su kayi da Maryam da ta ke neman nasu yan gidan.
"Ah ashe ki na nan ina ta nemanki kin shige mini. Mu je da ga cen mu zauna ta yadda duk wan da ya taho za mu hangeshi"
Hakan kuwa su ka ɗanyi nasa ga gate ɗin su ka tsaya gefen titi. Shiru-shiru a na ta watsewa su duk biyun basu ga ƴan gidansu ba.
"Ina mamakin ko dai baba ya mance da ranar candy dinne?" Fatima ta faɗi ta na leƙen titin.
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!