Tun ya na wanka ya ke jiyo ringin ɗin wayarsa, ba wai don karar wayar ba sai don sawa rai da zullumin kiran Abbu a koyaushe, don yadda ƙofar washroom ɗin ya ke ba lallai ma aji ko magana daga ciki ba. Da ya fiton kuwa ya iske missed call ɗin Abbun. Gabanshi ya faɗi ya shafi kansa ya na jin wani sabon tashin hankalin na zuwar mishi.
A cikin shekarun nan ukku da su ka gabata shi kadai ya san irin fama da zuciyar da yayi, kalar wahalar da ya sha ba dare ba rana. Bacci ba ya iya yi, ba ma bacci ba babu abin da ya ke yi ban da sallah da kwanciya. Ko yaushe tunanin yadda su ka fita cikin so da nishaɗi zuwa 2nd anniversary ɗin Dikko royale ya ke. Yadda motarsu ta ƙwace mishi ba shiri birki ya ƙi yi da yadda su ka faɗa cikin gada akan idon shi Nadra ta rasu bayan samun ceton Ikram da akai dakyar ta hanyar operation ba ta ko san halin da take ciki ba, ba ta san me ta haifa ba rai yayi halinshi.
Ya tuno lokacin da Mami ta ruko kannunshi da duka hannuwanta idon ta cikin nashi ta ke fada mashi
"Kar ka yarda da kowa Naseer, akwai abubuwan da baka sani ba acikin gidanku akwai boyayyun sirrikan da baka da masaniya a kansu Naseer.
Na san ka iya girki tun da dashi ka taso tun yarinta.."
Sai ya dinga tuno lokutta dayawa da ya ke taya ta aiki, da ya ke yi mata girki kuma duk idan bata lafiya. Bai ta ba ganin taci ko tabashi abincin da bata girka ba a cikin Dikko mansion. Ya ji ta ƙara matse hannunshi.
"...ka ci abin da kai ka girka. Ban ce ka nunawa ƴanuwanka Bambanci ba amman ka bi sannu da kowa. kar ka ce za ka zauna ba aure."
"Mami don Allah.. ki bari, ki bar magana irin haka"
"Naseer Allah yayi maka albarka ka kula da Yarinyarka ka saka mata sunan Nadra sannan ka sama mata uwa tagari.."
Daga haka bai kuma jin muryar Mami ba. Ita ma ta tafi kamar yadda Nadra ta tafi..a lokacin sai ya duƙe a ƙasan wurin kanshi bisa tantagaryar tiles ya na wani kalar kuka, kukan da ya dauke shi watanni ya na yi kafin ya dangana. Ya riga ya a za dukkan laifin rasuwarsu a kanshi hakan ya dinga damunshi ya na addabarshi har zuwa yanzu da ya ke jin babban zunibi ne ya kalli wata macen da sunan so bare Aure bayan shi ne sanadin rasuwar tashi matar. Wata kila da bai ja motarsu ba da ba haka ba, su na da direbobin da bai san adadinsu ba amman ya zaɓi tuka motar duk da ma kusan lokutta da yawa hakan ya ke yi in dai da Nadra zai fita.
Ya na son Ikram ƙwarai, sosai ya ke son ta akusa dashi ko yaushe amman ganinta a lokutta da yawa na saka ya dinga jin bai kyauta mata ba, ya ke jin ya kashe mata uwa da hannayenshi, ya ke jin kuma shi bai cancanci soyayyar da Ikram ke mashi ba. Wannan dalilin ne ya saka Hajja ke ɗauke ta ko yaushe ta na ɗakinta har kayanta. Ya dubi in da ya aje hotunan da Abbu ya bashi da har yau bai duba su ba, ya kauda kai. Shin wai ya zai yi ne? Ya ji an ƙwanƙwasa ɗakinshi. Da mamaki ya kalli ƙofar sannan ya mike ya zura doguwar jallabiyar da ya ke ta riko a hannu.
"Shi go"
Ya faɗi ya na jan hular rigar ya rufe kusan fuskarsa saboda sauyawar da ta yi.
"Yaro na"
Ya ji muryar Mom. Ya ɗan juya kaɗan ya kalleta ya maida kanshi ga hotunan.
"Na ga baka fito ba duk yau, tun jiya ma dai baka sauko ba"
"Kawai ina hutawa ne"
"Na san dai tatsuniyar gizo ba ta wuce ta koki, ni dai ban son shirun nan na ka don Allah ka mance da komai..."
"Mom please"
Ya katse ta. Ta harari bayanshi sannan ta kai dubanta ga hotunan in da ya ke kallo. Ta mika kannu ta dakkosu ta buda ta na gani.
"Kai kai me waɗan nan fitsararrun su ke a dakinka yarona?"
"Da sauri ya kalleta"
"Eh mana, waɗan nan yaran yo waye bai san su a gari ba saboda tambaɗa. Don Allah idan ka na da hadi da su ka janye. Su ba wasu hadadduba ba wani aji amman sai tsabar..."
![](https://img.wattpad.com/cover/270528964-288-k829669.jpg)
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!