13

192 16 0
                                    

Motsin shigowar da ta ji ya saka ta buɗe idanuwanta da sauri ta na ƙara cukuikuyewa cikin lafayar ta rufe fuska.

Duk da ya san zai ganta a ɗakin hakan bai hana zuciyarsa zafi ba. Bai kalla in da ya ke tsammanin ta ke ba ya aje babbar rigar da ya dinga fama da ita tun da rana, akan kujera. Wayoyinsa ya zube a ƙaramin table ɗin da ya ke gefen kujerar tare da zama ya kishingiɗa ya na lumshe ido cike da gajiya. Ya fi mintuna goma a haka wayarsa ta yi ƙara. Hango sunan mai kiran kawai ya saka zura hannu ya dakko

"Fito ina jiranka yanzu"

Ta faɗa ma shi. Da wayar a hannu ya buɗe ɗakin. Ta na tsaye da leda a hannu.

"Mom"

Ya faɗi ya na shafa kai. Ta miƙa mashi ledar da harara a fuskarta

"Idan hannunka ciwo ya ke gashi na kawo ma. Kar ka bar yarinyar mutane da yunwa"

Ya na amsa, ta juya ta tafi. Fuskarshi da ta ke a yamutse ya shafa ya na kallon ledar. Tun a kan hanyar su ta dawowa da su Saifullah,Umar ya fita ya siyo abin da bai san ko meye ba a ledar ya miƙo mishi.

"Na amaryarmu ne"

Ya faɗa a lokacin da ya aje ledar. Da ledar da Umar din babu wanda ya kalla. Bayan sun iso ma fita yayi ya barsu bai saurari sauran maganar da su ke faɗa mashi ba wanda ya ke duk akan amarya ne.

'Amarya'

Ya faɗa a fili da shakku a cikin muryar. Komawa ya yi cikin ɗakin ya nufi in da ta ke. Tsayuwa ya yi ya na kare mata kallo a yadda ta cure wuri ɗaya.

Wannan abun su ka kira da amaryarsa? Ba zai iya Danganta Mom da marar hankali ba shiyasa ya kauda tunanin a ransa. A mman ko makaho ya laluba daga kallo ɗaya ma ansan ba zai taɓa ansar wannan figigiyar yarinyar a matsayin mata ba. Naseer ko a da cen ya na da taste ba kowacce kalar mace ta ke birgeshi ba. Ko da Abbu ya aura mashi Nadrah Babbace a lokacin har service ta gama kuma cikakkar mace ce marar makusa. Ya kan yiwa su Saifullah tsiya a duk lokacin da su ka yi yammata kanana, ko zance baya rakasu ma don ya na ganin babban raini ne tiƙa tiƙa da su suna zuwa wurin yan yara ana ja masu aji ayofi.

Shi ne yanzu aka kawowa wannan figigiyar?ko da babbar ce ma bai shirya zaman aure da ita ba bare wannan abun. Ledar kawai ya aje a gefen gadon ya juya.

"Zan yi sallah"

Yar muryarta da ta kara shaida mashi yarintarta ta ratsa kunnuwan shi.

"Na hana ki ne?"

Ya fadi can kasan maƙoshi.

"Ina kewayen?"

Ta faɗi ta na ɗan ɗago kanta. Hannu ya miƙe saitin hagu kawai ya nuna kofar ya juya. Idan ban da ɗagowar da ta yi ma da ba za ta san me yayi ba. Mamaki ya kamata.

Wanda ke zuwa ya na surutun ne a gidansu yanzu zai wani dinga sha mata ƙamshi? Lalai ma wannan ɗan rainin wayau ne. Ban da har yanzu zuciyarta ta kasa sakewa ai da ba za ta zauna a haka ba tun dazun. Miƙewa ta yi, ta nufi in da ya nuna mata ta murda kofar ta shige.

Buɗe baki ta yi ta na kallon kewayen kato dashi. Aajiyar zuciya ta yi ta na godewa hikimar Mom na zayyana mata abubuwan amfanin gidan, da a yau kuwa ba sai gobe ba zai fahimci kalar matar da ya aura. Jikinta na ɗari ɗari ta kunna famfo ta yi alwala ta fito.  Ba ta ganshi a dakin ba ta gyara zaman gyalenta ta yanki wuri ta fara sallarta.

"A garinku nan ake kallo?"

Ta jiyo shi a lokacin da ta kai raka'a ta biyu. Muryarsa da yadda yai maganar ta saka ta daburce ta juyo ta kalle shi. Ya wuce ba tare da ya kalle ta ba ya shiga toilet din.

Bin shi ta yi da idanu ta na jin muryar shi bambanta da wacce ta sani a wurin wanda ke zuwa wurinta. Lokaci ɗaya tunanin ba shi bane ya zo mata. Tabbas biri yayi kama da mutum yadda ta ga wannan ya ke ai ba ma zai zo ɗin ba. "Ko ya za mu zauna ɗin ma?" Ta taɓe baki ta samu kujera ta zauna jiran ya fito ya nuna mata gabas.

HAYAR SOWhere stories live. Discover now