Seoul,Korea
Motar Abbu ta gangara wajen aje motoci na cikin gidan, ta tsaya. Bai jira an buɗe mashi ba ya fito. Kallo ɗaya za aga ramarshi kiri-kiri da rashin kwanciyar hankalin da ya bayyana kwance a fuskarshi. Wayoyin shi aka miko mashi ya karɓa ya shige cikin gidan. Tsaye yayi yana kallon kofar falon da take a buɗe cikin tsananin mamaki don ya san ya kulleta ba don wani zai shiga ba. Wata zuciyar ta shaida mashi kilan mancewa yayi bai kullen ba. Ta falon da zai kaishi dakin shi yabi in da suke zama suyi fira da Yaseer ya tsaya yana kare mashi kallo ya na tuno duk wasu firarrakin har yana hango kamar Yasser din na zaune a wajen. Kwallar da take saka idon shi rawa ya saka hannu ya mirtsike ya na samun daya daga cikin kujerun ya zauna. A yanzu kuma bai san abin yi game da Yaseer ba, yadda suke binciken su da kwakkwafi shi kanshi ya yaba hakan ya kuma san sun yi mashi aiki ba na wasa ba akan neman shi, amman abu ya faskara ko dishi-dishin shi ba a samu ba kuma an tabbatar mashi bai bar ko garin ba bare ƙasar. Ga Hajja da duk sadda ta samu sarari kiranshi take ba dare ba rana akan cases ɗin cen gidan da har ya gaji da jinsu. Labule yaga ya kaɗa kamar da mutum a baya ya dade yana kallon labulen kafin ya tashi ya nufi wajen, mutum yaga ya zura da gudu har yana tuntuɓe ya nufi bathroom da gudun tsiya. Cikin sauri Abbu ya bishi. Yana shiga yaga baiga mutunen ba, kalle kalle ya fara yi yana neman in da ya shige. Yafi minti biyar a tsaye yana neman mutunen da ido baiga ko wa ba. Fitowa yayi ya kulle bathroom din da makulli. Ya zagaya ya saka wani security tsayuwa bayan bathroom din wajen window koda zai diro, sannan ya koma ya dakko wayar shi ya kira Detective Park yace yazo gidan shi.
Basu jima ba sai gasu su biyu, ya fada masu tun kofar da ya tarar bude har mutunen da ya gani. Ciki suka koma ya bude bathroom din suka shiga dubawa har saman water heater da saman windows. Cen bayan bathtub ya hango shi daga cikin glass din tagar. Ya kudundune ya cure waje guda ya na kyarma. Damko shi akai ya juyo jikin shi na rawa yana sussune kai."Yaseer!"
Abbu ya fadi cike da mamaki da shakku. Kayan jikin shi ba zai manta ba tun na ranar ne da zasu tafi gida, gashin kanshi da yake tarawa yayi cuku-cuku haka fuskar shi ma duk tayi muni cikin gashi ba gyara duk yabi ya firgice.
Abbu ya matsa gaban shi na faduwa ya taba kafadar shi
"Yaseer"
Ya kuma kiran shi muryarshi na karyewa. Yaseer ya janye kafadar shi da sauri ya matsa cikin tsoro. Abbu ya juyo ya kalli Detective Park.
"Bari mu kira asibiti azo a tafi dashi, bashi da lafiya"
Kai Abbu ya jinjina jikin shi a sanyaye da wani kalar tsoro a cikin ranshi. Yaron shi ne a haka? Suna tsaye a kanshi har aka zo tafiya dashi dashi yaki yarda Abbu ya kama shi sai dai likitocin.
"Yaskid...Yasss!"
Suka jiyo muryar wani yana kwalla ma Yasir ɗin kira yana shigowa cikin falo, a lokacin suma sun fito falon. Ido huɗu Abbu yayi da Junaid(JMan) ya murtsika ido ya buɗe yaga dai Junaid ne. Junaid sirikinshi yayan Zahra. Yayi wata shiga da ganin shi kasan ya isa cikakken tantiri ko a saka wandon shi wanda kafan ya hana ya faɗo kasa. Gaban JMan yai wata kalar faduwa, bai tsaya shawarar komai ba ya juya a guje zai bar dakin.
Detective Park suka damko shi, ko ba a fada ba sun san laifi ya saka shi guduwar. Bakin Abbu ya kasa furta komai don mamaki, bai san ma ta ina zai faro tunanin shi ba, mai ya kawo Junaid a nan, ko meye hadin shi da Yasser ko kuma yadda ya ganshi a haka sabanin yadda ya saba ganin shi?
"Ya za ai dashi?"
"A aje shi tukunna, za muyi magana da shi idan na natsu"
Da JMan aka fito su Abbu suka tafi Asibiti asibiti shi kuma su Park suka tafi dashi.
***************
"Wai Don Ubanki za kiyi man shiru in ji da abin da ya ishe ni ko da wannan kukan naki zan ji?"
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!