I hate the distance between us. I want to touch you, but I cannot. It’s killing me. I loveyou and miss you terribly. I hope soon we’ll be together.
~~~~
Dukkan fuskokin su cike suke data alhinin hukuncin da aka yanke a zaman kotun farko kuma na karshe, bayan share sati dayan Umma da Yusuf police station zuwa mikasu koto. Amina, Aysha da Adam kuka suke kamar ran su zai fita. Sun sani ta cancanci duk wani hukunci, ta kashe rayuwa ta kuma salwantar da rayuka amman uwar su ce. Hukuncin kisan da aka yanke mata ta hanyar rataya yayi tsaurin da zuciyoyin su ba zasu iya dauka ba. Duniyarsu ta harmutse ta riki ce ga Abbu tun ranar da abun ya faru yana Asibiti bai san in da kanshi ya ke ba har yau. Yusuf hukuncin daurin shekara goma a gidan kaso aka bashi. Mommy kallon kowa kawai take da ido sam ko magana bata iyawa zaman kotun ma bayan an yankewa Yusuf hukunci hawaye kawai ke zubo mata da babu sauti, tana ji tana gani aka wuce dashi idanuwan shi cikin nata. Bata baro wajen ba sai da aka kamo taSuna nan tsaye suna kua aka fito da Umma da Yusuf za a tafi dasu, tun da ita Umma kwana biyu a ka saka yanke hukuncin nata, Yusuf din ne za a wuce dashi kai tsaye. Da gudu suka ruga suna rirriketa a na janye su, duk wanda ya gansu sai ya matukar tausaya masu ba kadan ba. Da kyar take taka kafarta sakamakon ciwonta da yai mugun tsami ya ke fitar da ruwa saboda rashin kula da ya samu. Da kyar yansanda suka banbare su suka iza keyarta mota aka tafi da ita. Mom kuma da bata kara sanin me take ciki ba aka jata aka koma gida da ita duk ta rame ta zuge kamar mai cutar amai da gudawa.
Wani ɗansandan da ke tsare da JMan ya ƙaraso wajen Naseer.
"Ranka ya dade ya batun yaron wajan mu fa?"
"Wane ke nan?"
"Wan da Alhaji ya zo dashi."
Ya sa hannu ya goge bakin shi ya jiya ya kalli Mom zuru sai raba ido take. To mai wacce ta saka shi aikin ma bata san me take yi ba, wane hukunci ya rage mata?shi an dakko shi ne tun daga kasa zuwa kasa yayi abin da aka saka shi an biya shi ya tafi, me ya rage?
"Ku bar shi ya tafi"
Ya fadi ya na juyawa ya tafi.
Inna da Fa'iza dake gefe ma suka tari napep sukai gida. Daman ta zo ko Allah zai saka Fatima ko Baba su bayyana a wajen.
***"Inna don Allah ki yi haƙuri ki ƙara ko loma biyar ce, kar yunwa ta kama ki. Ga rana kin shawo"
Cewar Fa'iza tana dauke da plate ɗin shinkafa da miya har da salad da ta san inna na so, ta na faman rarrashi kan taƙi cin abinci tun jiya.
"Aa Fa'iza halin da muke ciki ya fi karfin aci abinci. Ni dai kawai in ga Babanku in ga Fatima. Allah ya sa ba hannun mugun suka faɗa ba.."
"Inna ai ba sace su ko bacewa su kayi ba.."
"Kin san in da suke?
Ta katse ta. Ta girgiza mata kai.
"Aa Inna"
"To kawai addu'a ce mafita, amman ai an sa ce su..."
Sai ta fashe da kuka. A yanzu duk wani kwakwazon ta aje shi gefe tun da ta fahimci ba zai saka ta ganin su Fatima ba. Duk ta rame ta tsotse, dan kuzarin da ta farayi yanzu ya koma. Abinci kuma ta yanke cin shi tun jiya da rana. A cewarta bata san halin da suke ciki ba, ba zata saki ciki ita tana ci ba. Kuma har a zahirin idan ma zata cin ba zata iya ba, sam bata ji n yunwar cikinta kamar yadda take jin bacewar su.
A yanzu zata iya bada duk wani abun da ta mallaka don a dawo mata da su. Ta tsinewa Mom ya fi lissafin cikin kanta. Wani abu da ya ƙara firgitata da taga Mom ita ya babu duk ɗaya, ba zata iya cewa ta haukace ba tun da tana ganin yadda take kuka da aka tafi da ɗanta.
![](https://img.wattpad.com/cover/270528964-288-k829669.jpg)
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!