~~~~~
Shesshekar kukan ta ya ji cikin kunnuwan shi, shi ya ƙara karya zuciyar shi. Kenan dai duk tunanin shi hakan ne har ta ke tausaya mashi haka."Kuka kuma? Tawu ƙaddarai kenan. Ki kwanta sai da safe." Ya faɗi ya na rufe idanuwan shi ba don ya na jin baccin ba, yin maganar ta kara tado mashi tabon zuciyar shi, duk da a wani fannin nauyin da ke kirjin shi ya ragu saboda faɗin da ya yi. Bai taɓa zama yayi maganar da kowa ba, a ciki har da Mom da ya aje ta a matsayi na Uwa! Duk da ya sha samun tamabayoyi na rashin kula Ikram babu wanda ya taɓa tanka mawa duk da tambayar na mashi zafi sosai. Sai a yau da bai san maganaɗisun da ya jashi furtawa Fatima, bai san dalilin ba. 'wata ƙila don ka hangi wani ɓangare na kulawa' sashen tunanin ya fada. A wurin Mom ya san ta na kula dashi da nuna mashi duk soyayya haka Abbu ma, amman akwai wata kulawar da bai san ta yadda zai musaltata ba bai ma san da zaman ta ba tun bayan babu ran Mamin shi sai a fuskar Fatima, sai a kalaman Fatima. Yar yarinyar da bai zaci za ta iya kula da ko kanta ba ma, yarinyar da idan za a shakare shi ba zai iya cewa ga sunan ta ko ya zana cikakkar fuskarta ba.
*
Kuka ta ke marar sauti, kuka mai cike da wani kalar tausayi da bata san yaushe ta fara sanin damuwar wani ba bale tausayi, ita a rayuwarta kawai ta na yin abin da duk ya ke gabanta, duk baki da tsiwar da ta tashi da shi ba zata ce akwai wani abu tausai da ta sani ba, bayan na Babanta da ta tabbatar da shi ta fara wayau. Bayan haka babu wani abu na cikin rayuwar mutum da ke ɗaɗa ta a kasa. Ta tausayawa Naseer, namiji har namiji mai cikar haiba da kamala cike da kwarjini shi ne yake rayuwar ba yadda na iya, shi ne yake rayuwar da sam sam bata kamace shi ba, wata rayuwa da babu gata a ciki. Ƙwarai babu gata a dai kalar wannan gidan nasu da babu wanda sabgar ɗan uwanshi ta dama. Hajja ta tsufa duk da jikin ta bai nuna yawan shekarun ta ba amman sun ja da yawa, a halin da ya ke ciki sam ba Hajjar ma ta cancanci bashi baki da nuna mashi hanyar da zai bi ba. Za ta yi karya idan ta ce a ɗan zaman ta gidan ba ta fahimci Abbu ya fi son shi fiye da kowa ba, amman duk wannan son ba ta hango kulawa a cikin shi ba, asali ma son ya dawo da- dai ɗin, duk dan ya ja ragamar gidan ne a yarda aƙidar Abbun take na dole sai shi da ya ke babban namijin farko a gidan. Kulawa ya ke so mai cike da nasiha da nusarwa akan kaddarar shi. Mom ta riga ta fidda ta layi tun da ya zo gabar cewar ba ita ce asalin mahaifiyar shi ba. Ta fahimci dole ta na da manufa.Ta yaya zata fara taimaka mashi, ba za ta taɓa barin shi a halin nan ta tafi a haka ba. Ko dan Hajja, ko dan Ikram, ko domin tausayin da ta ke jin ba zai kafa a zuciyarta ba har sai ta ga ya zama mutum kamar kowa, kamar rayuwar shi ta baya. To ta ina? Da ƙaryar? Koko da yaudarar? Wasu hawayen masu zafi suka sake zubo mata. Tabbas Mom da abin da take nufi da duk wannan shirin, to ya zata iya taimakon shi idan ba ta san manufar Mom ba? Ta ya za ta taimake shi a cikin ƙarya da yaudara? Idan ya gano gaskiyar lamarinta wane kallo zai mata? 'Macuciya!' sautin ya amsa cikin kanta. Ta runtse idonta da sauri ta na fatan kar Allah ya gwada mata ranar. Koma ta wace hanya ce za ta taimaka mashi, sannan ta bar rayuwar shi ba tare da ya sake jin ɗuriyarta ba, bare ya furta mata kalmar 'Makaryaciya!, Mayaudariya! Kuma macuciya!'
"Ya Allah!"
Ta faɗi cikin sarƙewar numfashi. Miƙewa ta yi zaune kafin ta tashi ta fara takawa a hankali har zuwa bakin gadon shi.
Motsin da ya ji ya saka shi buɗe ido. Ta na tsaye a gaban shi, hannuwan ta sarƙe da juna.
"Mene?"
Ba ta ce komai ba ta raɓa filin da ya bari ta zauna.
"Kamar yadda ka ce ba don kana so kake share Ikky ba, haka kaddara ma bamu da zaɓin wacce za ta zo mana mai kyau ko marar kyau. Hakan kuma baya nufin mun karaya da lamurran rayuwa. Duk kokarin ka na ganin ka karesu ba wayo ko dabarar taka za ta kare su ba sai abin da Allah ya kaddara, in haka ne kuwa kaba baka isa kaja da hukuncin Allah ba. Kenan ba zaka kalubanci kan ka akan kaddarar wani ba, ko da kai ne da kan ka.
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!