"Fatima"
Ya kira ta a karo na biyu. Firgigi ta juyo tana kallon shi kafin ta saki ajiyar zuciya.
"Menene?"
Ta yi guntun murmushi. Ta faɗa mashi? Ta yaya ma? Yusuf kanen shi ne ta ina zata fara fada mashi abin da ta gani, idan ya zo ba daidai ba kuma ya kalleta makaryaciya? Duk mutuncin da Yusuf din ke mata da mutuncint da ya ke gani kuma ya zube.
Zama yayi yana fuskantar ta.
"Yanzu fada mani. Kiyi haƙuri kiran gaggawa ne akai min, yarinyar ce wadan da suke tare suke son kashe"
Ta fiddo ido waje cikin tashin hankali.
"Me..meyasa?"
Ta tambaya muryarta na rawa. Ya kama hannuwanta ya matse.
"Ki nutsu. Bata mutu ba, amman ta na asibiti, ina tsammanin don kar ta tona masu asiri ne ya sa suke son kashe ta"
Ta yi shiru tana tunanin har sun kai haka? Kashe junansu don rufin asirin su? Kenan idan ta fadawa Naseer abin da ta gani daga ita har shi suna cikin haɗari tun da zasu iya komai don rufin asirin su.
"Ki kwanta haka nan ki huta da safe sai muyi magana"
Ta kalle shi.
"Ina jin tsoro"
"Babu abin da zai same ki"
Ya faɗi ya na miƙewa. Riga da wandon baccin da ya fara hada ido dasu ya ciro mata ya bata. Sannan ya juya ya shiga washroom ya watso ruwa ya saka kayan bacci. Zaune ya iske ta bisa gado ta saka kayan amman bata kwanta ba, kwata-kwata tunaninta baya tare da ita. Ya iso gabanta ya saka mata hular da ke rike a hannunta. Ya ce
"Ki kwanta"
Kwanciyar ta yi, ya lulluba mata blanket sannan yai mata addu'a ya tofa mata. Kamar jaririya haka ya ke shafa bayanta yana jiran tayi bacci. Bai dade zaune sosai ba ta yi baccin sai ajiyar zuciya ta ke saukewa. Ya miƙe kamar zai tafi kuma ya juyo yana kallon ta. Zagayowa yayi ya kwanta gefenta ya ja blanket din ya rufa ya tada kanshi da hannun shi ya zuba mata idanu. Kallon ta yayi har ya gaji kafin yayi addu'a shi a ya kwanta.
A cen cikin bacci ya ji ta rirriƙe shi ta na surutai, ya buɗe ido da kyar tare da kunna fitila.
"Kace ba zaka barni ba.."
"Kace ba zaka barni ba.."
"Ni ba zan tafi ba"
Ta dinga maimaitawa ta na rike shi. Bai san sadda murmushin daɗi ya kubce mashi ba. Ita ma tasan so? Ya kuma yin dariya ya na goge bakinshi da tafukan hannuwan shi. Wani kalar feeling ya ke ji da ya dade bai ji kalar shi ba, bai taɓa sanin da sauran so da ya rage sai a yanzu ba. Baccin da bai koma ba kenan ya cigaba da zuba mata ido ya na shafa kan ta iya lokacin da ba zai ce ga yawan shi ba.
****South Korea**
Agogo ya ke kallo yana kara kallon ƙofar ɗakin Yaseer 4:30pm sauran su minti talatin jirgin su ya tashi amman har yanzu bai fito ɗakin ba. Kayansu tun jiya ya saka aka saka su mota duk don kar ya bata mashi lokaci tun da ya ga bawai son tafiyar ya ke ba. A yanzu haka ma har sun fito yayi hanzarin shiga daki bai san mai zai dakko ba yafi karfin mintu sha biyar shiru. Matsawa yayi bakin kofar ya kwankwasa
"Kar ka bata mana lokaci Yaseer ka fito mu tafi"
Ya saurara. Ya kuma bugawa da karfi sannan ya buɗo kofar ya fito idon shi da alamun bacci. Kallon mamaki ya ke mashi
"Bacci?"
"Wallahi Abbu kawai bacci na ji yana daukata"
Takaici ya hana Abbu magana kawai ya juya ya ce
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!