Ta buɗe kumburarrun idanuwanta da ta ci kuka ta gaji har ta yi bacci ba ta sani ba, a kan Fa'iza da ke tsaye a kanta. Kallo daya ta yi mata ta ga tashin hankali a fuskarta ban da sauya kalar da idon ta itama su kayi. Don abu ne mai wuya ke saka Fa'iza ta yi kuka duk tsurin shi.
"Yaushe ki ka dawo?"
Fatima ta tambaye ta ganin yadda lokacin tashinsu makaranta yai saurin yi mata. Ba ta bata amsar tambayarta ba sai cewa ta yi
"Fatima Baba..."
Da sauri ta tashi zaune
"Ina Baban? Me ya faru?"
Ta runtse ido ta ƙarfi ta na rasa ta yadda za ta korowa Fatima jawabin abin da ya faru ta ke.
Tashin su daga makaranta kenan suna tsaye bakin titi suna jiran napep din da za su cika su dawo gida, kamar da wasa motar yansanda ta gifta ta gabansu ga mutane sai wata motar ma da ta bi bayansu bata san mi ya ja hankalinta ga motar ba ta hango Baba zaune da hawaye su na bin fuskarsa. Da sauri ta shige napep ɗin da tsayawar ta kenan ta ce ya bi bayansu ba tare da ta ji kiran da sauran kawayenta ke mata ba.
Kafin ta isa har an fito da Baba an ingiza shi cell.
"Me yayi ku ka kawo shi anan? Ku bari in ga Babana"
Ta dinga maimatawa a lokacin da su ka hanata shiga.
"Babanki ne?"
Cewar wani ɗan sanda ya na mata kallo ta ƙasan ido.
"Eh me yayi maku?"
"Ai ba za ki iya ganinshi a yanzu ba gaskiya.."
Kin ga matar cen?
Ya nuna mata wata dakekiyar mata ɓaka ƙirin da ita, ta ci uban ado ta yaɓa jan janbakin da ko a lama bai yi mata kyau ba sai girgiza ƙafa ta ke.
"...ta bada umarnin babu wanda zai ganshi har na tsawon kwana ukku kafin a tafi kotu"
Ta zaro ido a tsorace gabanta na faɗuwa.
"Kotu kuma? Duk a kan menene wai?"
Ta yi saurin zuwa gaban matar ta na mata wani kallin tsana.
"Me Baba yai maki ki ka kawo shi nan?"
Matar ta juyo ta kalleta a yamutse.
"Ohh dangin ɓarawon ne sun fara zuwa? Kar ma ki wahalar da kanki ba za ku ganshi ba har sai ya fiddo mini sauran sarkoƙi na wallahi..."
Kalmar ta yi mata girma sosai a kai. A nan matar ta fara mata bala'i wai ubanta ya je har gida daga ya shigar masu da kaya daga napep zuwa cikin gida shi ne ya sace mata sarƙar gwal a bisa madubi yanzu an ga ɗaya a aljihunshi ba'a ga ɗayar ba.
Fa'iza duk ta ruɗe gashi ita ba mai magana ba, a sanin ta ma baba bashi da Napep to duk me ya kawo haka? Da ta rasa yadda za ta yi da su ga mutane sai nuna ta a ke yi sai ta hawo Napep ta dawo gida don ta faɗawa Inna. Ta iske Innar bata san sai Fatima da ke bacci.
"Ki faɗa mini me ya samu Baba?"
Fatima ta fadi a ruɗe. Sai kawai ta jawo hijab ɗin Fatimar ta mika mata ta jawo hannunta. Su na fitowa Inna ta shigo gidan da jikkar gari yai zafi a hannunta bakinta a washe. Daga kasuwa ta ke, ta yo siyayya da wasu kuɗin da Mum ta bata don ma rana ta yi da wurin Rabi'u kafinta za ta leƙa ta ji yadda za ayi da batun gado da kujerun Fatima. So ta ke ta fidda ta da kyau tun da gidan masu kudi za ta, kar su raina ta. Ta mance da daga wurinsu kuɗin ya fito.
Turus ta yi ta na kallonsu
"Lafiya na ganku a yamutse haka? Ku mu shiga ciki ga ɗan balangu nan na tafo da shi a motsa komaɗa"
![](https://img.wattpad.com/cover/270528964-288-k829669.jpg)
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!