Da waɗan nan kalamar dukkan kuzarinta ya dawo, da su duk wani abun da ta rasa na ɗabi'unta tun daga maganar auren har shigowarta gidan, su ka dawo. Ta ji ita ce Fatima! Fatimar da bata da tsoro, mai ƙwarin guiwar da ba a cutarta ta fatar baki.Kayan da ta cire ta linke ta maida su sannan ta zaro rigar da ta fara shiga hannunta. Kowacce iri ce za ta saka, za kuma ta ci gaba da saka su iya zamanta a gidan ta kuma zagaya in da ta so. Rigar yellow ce mai ɗige digen fari a jiki tsawon ta bai wuce guiwa ba sai aka bita da tsaga a baya. Saka kayan ta yi ta na kallon yadda kafafuwanta ke shawagi a waje buɗe.
'kai' ta faɗa ta na fiddo ido. Gara dai ta samu masu wando. Ta cire ta linke rigar ta kuma zaro wani dogon jeans blue da baƙar riga mai guntun hannu ta saka. Ta jujjuya ta ga haka ya fi sauƙi.
Gaban madubi ta yi simple makeup da ya hau da sanyin safiya. Gashin ta ba dogo ba ne balle ta sake shi yadda ta so shiyasa ta samu bakar hula ta saka. Da saurinta ta koma wurin kulolin abincin da ta bari. Dukkanninsu ta buɗa a ciki dankali da kwai kawai ne abin da idon ta ya sani. Sauran a ido ma basu bata sha'awa ba bale ta iya kaiwa bakinta. Dankalin ta zuba da kwai ta hada tea ta ci ta koshi. Ta maida sauran da bata taba a Basket ɗin ta kai gaban gado ta ajewa Nass.
Fa'iza ta zo mata a rai. Da sauri ta ɗakko wayarta ta kira Inna. Sai dai har ta tsinke ba a ɗaga ba. Haka ta dinga jera kira ya kai biyar ta gaji ta hakura. Sai a lokacin ta tuna yau Litinin ma Fa'iza na makaranta. Don ita Inna wayarta ita da babu duk ɗaya a na iya kiranta hamsin ma ba a samu ba. Idan ta dawo an jima sai ta kira kila idan Fa'iza na kusa sai ta ɗaga.
Rashin abin yi ya saka ta lalubo game ɗin da Fa'iza ke yi da wayar ta kama yi duk da tun cen ba iyawa ta yi ba amman ta lura zaman sai da game kafin sadda za ta shiga makaranta.
*******
Rana ta fara hasko shi da ga kishin giɗen da ya ke. Cikin gidan ke bai son komawa zamanta a ɗakin takura shi ya ke. Miƙewa ya yi ya shiga kai tsaye kitchen ya zarce. Ya na shiga masu aikin su ka bashi wuri kamar ko yaushe don yin girkin shi.
Noodles ya dafa da kwai ya fito. Yaseera da Aseeyah ne kawai a falon suna kallo sai Yusuf cen kusa da dining da handouts a baje ƙasa ya na rubutu rubuce.
"Yaa"
Aysha ta kira shi ya na gab da hayewa sama.
"Mom ta ce ba ka son Kamun da za ayi..."
Hararar da ya banka mata ya saka yin shiru ya juya ya tafi. Ya na bude dakin ƙarar ƙwal kwal ta game ta fara shigar mashi kunnuwa. Bai kalli in da ta ke ba ya wuce ya aje plate ɗin shi a ƙasan gado ya dakko prayer mat ya shinfiɗa a kan kafet ya zauna.
Da wutsiyar ido ta kallo shi. Ta ce
"Ga abincin ka nan in ji Mom"
Yai kamar bai ji ta ba.
"Kaji. Abincin k..."
"Ɗauki ki cinye"
Ya faɗi mata a takaice. Buɗe baki ta yi ta na kallon shi. Bai damu ba ya cigaba da cin abincin shi jin kallon ya yi yawa ya saka kallonta
Saurin ɗauke idon ta ta yi tana cigaba da game gabanta na faduwa. A duk sadda zai kalle ta sai ta ga kamar zai taso ne ya shake ta ya ce ya gane ta. Jin shiru bai taso ba ta saki ajiyar zuciya.
"Ki kashe ƙarar ko ki aje wayar"
Ya faɗi ya na jin kamar ya taso ya rufe ta da bugu. Duk dai Mom ta jawo mashi wannan jidalin ai ya na zaman zaman shi.
Ya na gamawa ya shiga toilet, sai gashi ya fito yai tsaye a kanta.
Innalillahi ta fara karantowa a ranta hannuwanta na kyarma. Shike nan watan cin ubanta ya tsaya.
![](https://img.wattpad.com/cover/270528964-288-k829669.jpg)
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!