22

262 17 2
                                    

There are people who come into our lives in the most unexpected way, in ways we have never foreseen they would and then we fall in love with them and feel as if life could not proceed without them.
We want to tell them how happy we are that they came into our lives during these time.

~~~~
Wanka ta fito ta zauna ta na tsara kwalliya mai sauƙi, bayan ta gama ta kalli kanta ta cikin madubin ta na murmushin kyawun da ta yiwa kan ta. Ko da ba za ta jera kanta a sawun kyawawan mata ba, za ta birge kanta a hakan ma.  Ba ta da dalilin yin kwalliyar, amman kuma ta na da nasaba da huɗubar Yaseera tun bayan da ta halarci Dinner ga bikin Umar. Da yake a cikin gidan Yaseera ita tafi kowa shiri da abokanan Nass hakan ce ya saka ma babu abin da bata je ba a bikin Umar ɗin. A ranar da aka kai amarya a ka yi dinner ne washe gari da safe ta ke bawa Fatima labari, a lokacin ta na kitchen Fatimar Yaseera ta shigo ɗaukar ruwa sai fira ta riƙe su.

"Ai wallahi Antinmu da a ce kin san yammatan da ke wajen diner nan na san ba zaki bari Yaa ya je ba, ai ban za ci ba tare za su ba. Kin ga yadda yammata ke bin shi masu aji da gayu? Lallai, wallahi sai kin dage kin dai ga ba wani fita yake ba ko Office baya zuwa, idan baki so wankin hula ya kai ki dare gara ki dage"

A lokacin dariya kawai ta yi, duk da a zuciyarta ta ji ba daɗin yammata masu ajin da taji wai suna bin shi.

"Ba maganar wasa ba wallahi kin ga Yaaya ko? Sam bashi da wahalar shawowa in dai ta hanyar gayune, ni zan shaida miki ya na son mace mai gayu da kwalliya..."

Kiran da aka ƙwala mata daga waje ya datse labarin nasu. Ya kuma zauna dam a ranta da bata san dalilin zaman ba. A yau kuma ta tashi da ganin son ta rike wuta. Ta kara kallon kayan da ta zaro za ta saka ta yi dariya. Dariya ta ke yiwa kanta, kalar wautar da ta ke yi. Ina ita ina Nass in ba abu irin na Mom ba? Ita ba cikin manyan mata ba, ba cikin masu kyau ba, babu kuɗi to ta yaya kwaryarta da ta shi zasu gamu? Duk wadan nan tunanin kuma sai ta kasa maida kayan ta saka. Wando ne ɗan karami da ya tsaya bisa cinyarta da riga mai hannun vest bata rufe cibi ba, rigar saman ce ta sauko ta wuce tsayin wandon ta baya, daga gaba kuma iyakar in da wandon ya tsaya ta ke, shara-shara sai maballai biyu a tsakar rigar da dogon hannuwa masu dan faɗi daga sama ƙasa a tsuke. Kalar rigar ta sama red mai cizawa kalar janbakin da ta shafa.

Kanta da ya daɗe rabon shi da kitso ta sharce ta raba shi gida ukku yadda zai ɗan yi mata tsawon daurewa ta saka ƙananun ribbon, sai ta ɗakko hair pin ɗin Ikky kalar ruwan hoda ta maƙalawa tukuwa ɗaya.

Ta daɗe ta na ta juye-juyenta kafin ta ɗakko wayarta ta yi selfie ta na jin dadin yadda ta yiwa kanta kyau.

Kakkaɓe ɗakin ta yi ta goge ta fesa freshner da taga yana sakawa. Filet ɗin da ta ci Doya da ƙwai na safe ta kalla ya na aje gefen kujera ta dafe goshin ta. Ba za ta iya fita a haka ba sai ta ɗaura zane, abin da bata shirya ba a yanzu. Kafin Nass ya shigo ta tsara za ta nemi dogon wando ta saka a kalla ko cinyar ta rufe. Saman madubin ta haye ta na saka earpiece a kunnenta ta na sauraren audio din girki da aka ƙara masu bayani dashi bayan video.
**
Sanye da Jersey riga da wando na kamfanin Nike ya shigo ɗakin, hannun shi ɗauke da handkerchief  ya na goge zufar da ke goshinsa sakamakon workouts din da ya yi bayan ya kai Abbu airport ya dawo. Tsaye ya yi yana kallon ta, ta na kaɗa ƙafafuwa a hankalinta gaba ɗaya yana kan wayar. Handky ɗin ya soka a aljihu ya na dai-daita tsayuwar shi idanun shi da hankalin shi duka a kanta. Tamkar wata yar diyar baby haka ya ke kallon ta cikin idanun shi, cilla kafar da ta ke lokaci zuwa lokaci ya ke bi da kallo da murmushin da bai san da zuwan shi a fuskar shi ba. Ƙarar wayar shi ta dawo da shi, har ita da hankalinta ya ɗauku kan wayar ta ɗago. Waro mashi idanun ta tayi gaba ɗaya, ta duro ƙasa ta na jan rigar ta zuwa kasa, kamar hakan zai saka ta ƙara tsawo. Takowa ya dinga yi in da ta ke a hankali har a lokacin bai janye idanun shi a kanta ba. Wani kalar tsalle kirjinta ya shiga yi, zucciyarta ta dinga bugawa kamar zata fito, kafafuwanta su kayi wani kalar sanyi ƙalau. Ya iso daf da ita har ta na jiyo hucin nunfashinsa, wani abu ya yanke daga sashin zuciyarta ya rubza a lokacin da ya saddo kansa saitin wuyanta. Ta rufe idanunta gam ta matse rigar ta da ke cikin hannunta.

HAYAR SOWhere stories live. Discover now