19

198 17 3
                                    

Hankalinta a rarrabe ya ke da fuskar dukkan su da ke zaune bayan abincin da Aysha ta gama zubawa kowa. Lumfashin ta a riƙe a lokacin da Abbu ya ɗauki cokali ya debo har zuwa taunawa ya haɗiye murmushi ya bayyana afuskar shi, sannan ta saki ajiyar zuciya.

"Babu laifi, ban tsammaci har haka ba"

Ya faɗi fuskarsa a washe kafin ya ci gaba da cin abincin shi. Babu wanda yai magana har aka gama. Abbu ne ya kula da Nass baya Wurin ya kalli Fatima

"Ina mijin naki"

"Tun dazun da ya fita bai dawo ba"

Ta bashi amsa. Wayar shi ya ɗauka ya kira shi

"Ka shigo ciki yanzun nan"

Ya fada ya na kashe wayar. Ba a yi minti biyar ba sai gashi ya shigo din ya samu wuri ya zauna.

"Idan ka shiga ɗaki fa jikkar da na shigo da ita ta na nan saman kujera ka dakko mini ita"

Abbu ya faɗi ya na kallon Adam. Bayan ya kawo jikkar Abbu ya zage ya dakko wata takarda ya aje sannan ya sulalata gaban Fatima ya aje biro ya ce

"Ki yi sign, akwai wata a kasa ita ma kiyi"

Kowa zura mata ido ya yi har biron na faɗuwa daga hannunta. Yusuf ne ya miƙo mata ta gyaɗa kai da murmushi alamun godiya sannan ta yi sign a dukkan su ta taso zata bawa Abbu.

"Aa rike. Wannan tukuicin girki ne daga ahalin Dikko gabadaya"

Ya kalli Nass ya na daurawa da faɗin.

"Filin bayan government house, ka san shi ai sai ka kaita ta gano shi ko zuwa gobe daga cen ku wuce a yo mata passport, ba sai ya ɗauki lokaci ba na ke son ya kammala"

Idanuwa ta bude cikin mamakin wannan kyauta haka rana tsaka. Ta buɗe baki da shirin godiya Abbu ya miƙe

"Kar mu fara haka, ke sirika kuma diya kike a garemu ko ba haka ba"

Ya karashe ya na kallon Mom da Umma.

"Kwarai kuwa"

Cewar Mom. Umma kuma murmushin yaƙe ta yi tana nadamar kawo shawarar girkin tun a fari. Nass ya fara barin wurin bayan Abbu kafin duk su watse. Yusuf ya ɗaga mata yatsu

"Congratulations Antinmu"

Ya fice waje.

Ɗakin Hajja ta wuce ta nuna mata takardun,Hajja ta tayata murna da kashedin dagewa da addu'a a lamurranta. A wurin Hajjar ta barsu bayan ta ɗauki Ikram ta fita.

Ta na tura ɗakin su ya na fitowa bathroom da towel iyakar ƙugu ya na tsane jikin shi da alamun wanka ya yo. Buɗe idanuwa ta yi tana kallon shi kafin kamar an tsira mata allura ta juya mashi baya, a hankali ta ja kofar ta rufe.

Girgiza kan shi kawai ya yi yana ida tsane jikin shi, bai san meke damun yarinyar ba

"Crazy" ya faɗa sa'ilin da ya ke jawo rigar da zai saka. Har ya gama shiryawa bata shigo ba yana bude kofar ya ganta tsaye ta na fuskantar falo. Jin motsin shi ya saka ta juyowa ta na ganin shi ta juya da sauri. Ya wuce ta ya sauka kasa kafin ta juyo ta shige ɗakin. Jikkarta ta gani da Murjanatu ta kawo mata ɗazun sai a lokacin ta tuna basu dawo ba aiken da Mom ta yi masu. Ikram ta aje bisa kafet ta fiddo mata kayan wasan da ta siyo mata jiya a gabanta sannan ta dakko jikkar ta buɗe.

Teddy da Safwan ya kawo mata lokacin da tayi candy ce ta fado ƙasan ƙafafuwanta
Lokaci ɗaya yanayin fuskarta ya sauya ta sunkuya ta dakko teddy ɗin hawaye na cika idanunta. Tun da ta zo gidan a matsayin matar wani ba Safwan ba take iyakar kokarin ta na tura dukkan wasu memories nasu a wani sako na zuciyarta ta kumle har zuwa ranar da zata komawa farincikinta, wanda ta ke so yake son ta so na gaskiya. Ganin Tedy ɗin ya saka dukkan abin da ta ke faman tattarawa ta boyen ya fara warwarewa tare da hawayen da ke bin fuskatara.

HAYAR SOWhere stories live. Discover now