Babu wani abu da ta shirya ƙara faruwar shi don yanzu, musamman yadda Nass ya ki barin neman Samantha har yau. Kullum sai ya tara yan kitchen da sabbin tambayoyinshi. A gefe ɗaya ga Hajja da ta zuba idon ganin dawowar Abbu. Shi yasa ma ta yanke shawar lafawa da kudirinta, sai dai tafiyar da ta ji za suyi Abuja ta kwaɗaitu ga aikin ta na gaba.
Samantha kuwa a yanzu ta tabbatar ta yi nisan da Nass duk ƙwakwar shi sai dai ya hakura. Sam ba ta tsammaci zai yi wani bincike har haka ba, a yarda ta ke ganin shi bai damu da komai ba a yanzu, har da kuwa wacce aka kira da matar shi. Shi yasa ta damka mata kudade masu yawa tace ta bar garin kafin ta neme ta, Samantha bata bi ta kan kowa ba ta ware da yan kudadenta.
Da sannu za ta kawar da duk wani wanda ya shiga hanyarta, har zuwa sadda Adam zai yi girman rike kamfani. Shi yasa ta so Nass ya mutu tun a shekarun baya tare da matar shi. Mutuwar da har gobe Mom ta ke ɗaukar alhakinta a kanta ba tare da sanin aikin na Umma bane. Mom ƙwarai ta shirya tsab don ganin cewar Nass bai halarci taron ba, hakan bai yiwu ba kasancewar Yaseer ya je America wanda shi ne jagaban shirin, don haka ne ta canza shirin duk wani abu da zai hana shi isa akan lokaci har Abbu yai zucciya kasancewar shi mutum mai girmama lokaci. A lokacin, sakawa ta yi aka zuƙe man motar ta yadda dole sai sun tsaya shan mai in da a nan ne za a sace tayar motar kuma. A haka ta jejjera duk wani abu da zai riƙe su Nass a hanya. Umma kuma ta sani, ta ji firar su da Haj Hauwa.
Murmushi ta yi jin ta girmi wannan plan ɗin na su. Ita ta na komai sululu ne, har rainin da Mom ke mata kallon ta kawai ta ke don ta yarda ta fita iya magana da kissa amman sam muguntar Umma ta musammance.
Kai tsaye ta sa aka lalata birkin motar da ta san ita Nass za su shiga, wanda shi ne silar haɗarin su har rasuwar. Duk da bata so kashe Mami ba, tsotsai ya saka Mom tura ta cikin su.
Ita kuma Mom har gobe bata san aikin Umma bane ba nata ba. Ko da abun ya faru ta shiga ruɗani matuƙa, kuma har yau ta ke jigila da wannan baƙin sirrin.
*********Kallon ta ya ke sai faman sharce kai ta ke ta na runtse ido da alamun zafi ya ke mata, ga kan ma ya cunkushe. Tsawon zaman ta a gidan bai taɓa ganin kanta da kitso ba, bai sani ba ko bata so ne. Amman a ganin shi kitson zai fiye mata sauki da salama akan tsigar kan a haka cike da zafi.
A cikin satikan da suka wuce yar ramar rashin lafiyar da ta yi duk ta cike duk da ba wai kibar kirki gareta ba amman ta maida jikinta. A cikin kwanakin bayan ne kuma ya yi tunanin da ya ke ganin shi ne maslaha a gareshi da ita baki ɗaya. Yana ganin idan har ta bar gidan shi ne kawai sauƙinta, shi ne kwanciyar hankalin ta. Ya tsorata, ƙwarai ya tsorata da gubar da aka bata, bai za ci abun cikin gidan ya kai har haka ba, lallai ya ƙara jaddada kalaman Mami akan bai san sirrikan gidan Dikko ba. A yanzu ya ga wani ɓantalen duk da bai san daga ina ya faɗo ba, amman ba zai bari ya ruguza yar mutane ba. Shi yasa zai fi idan har ta tafi. Ba zai so a kashe mata ƙuruciya da ciwon zuciyata a gidan su, wanda in hakan ta faru ba zai yafewa kan shi ba tun da zaman shi ta ke.
Ya so ya zaunar da ita suyi magana ta fahimta, tunanin Abbu da ya zo nashi arai ya sakashi tuntuɓar Mom da maganar. Ita ce kawai za ta bashi goyon baya tare da nusar da Abbu manufar shi. Duk da a yanzu har a ranshi bashi da matsala da zamanta gidan, da dakin shi ɗin ma. Amman ya sani Abbu zai ɗauki hakan a wata fuskar neman dalilin rabuwa da ita ne.
"Mommy..."
Ya ce bayan ya zauna a doguwar kujerar da ke gefen gadon ta.
"Ina sauraron ka. Ka faɗi mani duk damuwar"
"Ina tunanin ba tsaro bane zaman yarinyar nan a cikin gidan nan, duba da abin da ya faru. A kwai cutarwa. Ta yi ƙarama da jalar rayuwar nan"
"Naseer"
Ya kalleta. A cikin idanuwan shi ta ke karantar kulawa, kular da ta ke fatan gani da za ta iya bada koma meye don taga hakan. 'Anzo wajen' ta faɗi a ranta. A dai-dai wannan gaɓar ce duk wata damar ta take, doke su tafi Abuja, kafin su dawo ta ke son ta ji labarin da take son ji, idan sun dawo kuma taga zahiri. A lokacin ne contract ɗin ta da Abbu zai ƙare, zai ga shedar ta tsaya tsayin daka wajen ganin haɗa kansu da kulla soyayyar su, a lokacin ne ta ke da 50% na Royale Inn, sauran kason ba zai mata wahala wajen mallakewa ba ya zamana na ta gaba ɗaya. Daga nan...sai ta juya kowa!
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!