09"Ke ban ga ta zama ba ai, a satin nan za ayi komai a gama. Shi ma yaron ɗan banza ne bai son ake bashi umarni na lura,amman fa ya iya acting fiye da yadda mu ka tsara mashi"
Cewar Mum ga aminiyarta Haj. Hauwa ta na kare da waya a kunnai.
"To idan haka ne ai ba wani abu, yanzu sai kin je gidansu yarinyar mu ji da me baban nata zai zo"
"Yanzu kuwa. Ban ma faɗa mashi zan fita ba kin ga...ina zuwa"
Ta katse wayar ta aje. A gurguje ta shirya tsaf ta feshe jikinta da turare ta yafa gyale ta fito. A falo ta tarar da Hajja suna kallo da su Ayshaa.
"Yawwa Rahama zo ɗauke Ikram ki kaita ɗaki ta mani bacci a ƙafafu har sun fara dayi"
Mum ta kalli falon duk ga yammatan gidan nan wai Hajja ta rasa wa za ta aika sai ita uwarsu. Abubuwan Hajja na baƙanta ranta,dole sai ta nuna masu iko da iyakarsu ita.
"Rahama..."
Hajja ta ciro idonta daga tv din ta kallo Mum da ke tsaye.
"To Hajja. Kallo a ke tatayi haka?"
"Gashi dai kin gani ai, idan za kiyi ki zauna ke da ƙafafuwanki basu gajiya da shegen yawo baki gidan ango ba ki gidan amarya,Allah sa ba wani abu ki ke kitsawa a ranki ba"
"Kai Hajja to ni me zan kitsa kuma?"
Ta ɗauki Ikram ta wuce. Hajja ta rakata da
"Ke dai ki ka sani ai" Ta maida hankalinta ga kallonta.
"Innalillahi ya akai ta fito ramin kuma..ku maido mani in gani"
"Kai Hajja don Allah ki yi shiru mu je me zai ce mata..."
Cewar Yusrah ta na turo baki.
"To duk ba uwarki ta janye hankalina ba bangani ba?"
"Hajja ba fa kaset bane Startime ne ba za a iya maidowa baya ba"
Ayshaa ta ce.
"To auho..ai mantawa na yi ko"
Babu dai wanda ya ce mata komai. Mum ta fito ba ta ƙara bi ta kansu ba ta na Allah Allah kar Hajja ta juyo ta samu ta shige corridor da zai sada ta da ɗakin Abbu. Tsayawa ta yi ta ƙwanƙwasa ƙofar aka bata umarnin shiga.
Umma da ke zaune ta na jin ƙwanƙwasa daman ranta ya bata Mum ce don haka ta haɗe rai tamau zuciyarta na zafi, daman ba tun yau ta saba shigo mata ba a duk lokacin da ta ke da aiki.
"Yaya dai Rahama? Fitar ce halan?"
Ta yi fari da ido ta na ida shigowa.
"Barka ce zan je yau kusan kwana biyar kenan"
"To ke ba zaki je ba?"
Ya tambayi Umma.
"Bata shafeni ba ai"
"To a dawo lafiya"
Ya faɗa ya na miƙo mata kuɗi. Ta karɓa ta fice.
**********************Duk yinin yau ta zura idon ganin Safwan amman shiru babu shi ba alamunshi. Tsoro ta ke kar ace a jiya bankwanan ne ta yi, shikenan sai sadda ya dawo kuma? Gashi ita ba waya ba bale su rika yi. Duk a sukuku ta wuni.
"Wai Fatima kwanciyar me ki ke a ɗaki duk yau haka?"
Ta jiyo muryar Inna. Ta shi tayi kawai ta zura hijabin ta ta fito
"Ina kuma za ki je"
"Gidansu Zainabu, sun dawo jiya bamu haɗu ba"
"To kince ina gaida Innar tasu"
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!