39

293 21 6
                                    


         Seoul, Korea.

Da wani kalar bayyanannen mamaki Abbu ya ke kallon JMan da ke gurfane a gaban shi yaci bugu.

"Rahamar ce ta saka ka duk abinda kayi?"

"Eh wallahi tallahi, na san zata musa muje gani gata a warware magana"

Ya faɗi don ya san idan har Abbu ya barshi kasar nan hannun 'yan sanda to ya mutu, har igiyarshi tayi rara babu mai fito dashi. Kan Abbu ya kulle, shi Rahma zataiwa haka? Shi zata yaudara? Duk a kan dukiyar shi da bata san ta yadda ya tara ta ba?

Booking flight ya saka aka yi mashi na ranar, duk rintsi baya son ya kuma kwana a kasar nan idan ba Nigeria ba, idon shi idon Rahma da shegiyar yarinyar da aka kawo tana cinye mashi arziki sai ya saka sun biya. Fatan shi ya samu a dauki Yaseer hankali kwance har su isa gida. Don duk wani gwaje-gwaje anyi an kuma tabbatar da babu abin da ke damun shi ciki da wajen shi hakan ya saka Abbu tunanin ko dai makiyan ne suka tuso shi gaba ta hanyar yaron shi? Shi yasa ya yanke shawarar maida shi gida, ya nema mashi magani shine za a yi mashi allurar da har su je gida ba zai tashi ba don ba zai taba bari a tafi dashi ba ko kusa da Abbun bai iya tsayawa.

Hakan kuwa Abbun yayi ya saka aka tarkato mashi JMan ya haɗo dashi suka yo Nigeria.
      ******************

"Sis"

Munjanatu ta kira ta a karo na biyu ta na dafa kafaɗarta. Fatima ta ɗago idanun ta da suka koma kalar kuka.

"Ba dai kukan kika kuma yi ba?"

Ta yi murmushi ta girgiza kai.

"Mami tace mu dafa abincin rana ta fita. Me zamu dafa ne wai?"

Ta yi tambayar tana cire hijab din islamiyyarta ta fara linkewa. Sauko kafafuwanta daga gadon tayi bata bata amsa ba. Ita ma tafi son tati duk wani abin da zai janye mata hankalin tunanin Naseer. Duk da a fuska damuwarta bata boyuwa, kawai saukin ta da Baba na kusa da ita.

Sai da Murjanatu ta fiddo masu awarar da ta siya a kofar islamiyya mai zafi suka ci kafin su tafi kicin din.

"Yau Daddy zai dawo fa, idan bamu dafa dafa abu mai dadi ba Mami za ta yi faɗa yanzu ma fitar ta dole ce na san da babu in da zata sai ta gama"

"To me za muyi?"

Fatima ta tambaya suna taruwa sukai zuru a cikin kicin. Ganin Fatima ta kuma yin shiru ya saka Murjanatu fara fiddo kayan girkin tana mata surutu. Suna yi suna fira har suka gama. Sai da suka gama zubawa kowa Daddy da Baba sannan suka hada nasu sukayi ɗaki. Fatima na gama wanka suka yi sallah suka ci abinci ta zo wajen Baba a lokacin ya gama cin abinci ta zauna suna fira yana kara kwantar mata da hankali da bata hakurin da bakin shi bai gajiya.

Bayan ta koma ne ta kunna wayarta tayi wa Fa'iza message ta fada mata in da take, da gargaɗin kar ta fadawa Inna kamar yadda Baba ya gargaɗeta shima. Ko barin gidan nan yayi bashi da niyyar zama inuwa ɗaya da ita sam bai son ganinta ma bayan abin da tayi mai girma na rashin hankali ga diyarta da rayuwarsu gabaɗaya.
          *****

Umma da ke zaune bida hannun kujera tana kaɗa kafa cikin jin daɗin shirin da ake gabanta, tayi saurin hantsukawa ta faɗa cikin kujerar, kafin ta tashi zaune ta kuma miƙe tsaye tana kallon Yusuf da rabin fuskar shi take a kumbure tayi jan duka. Ta kuma kallon Fearless da Bobo suma sun ci bugu da ganin su hannuwansu sarkafe da ankwa.
Ji tayi kamar an tattaro duk wasu abubuwan da ke cikinta an tsuke waje ɗaya, kafarta ma kyarma take idanun ta waje ta ke kallon su, su da 'yansandan.

Mom ma tsayawa tayi da kuka da magiyar ta na son tantance ɗanta ne wai take gani a haka kuma tare da wasu da suka fi karfin a kira su da kauraye tsabar lalacewa. Kuma daure da ankwa a hannun 'yansanda? Ta girgiza kanta

HAYAR SOWhere stories live. Discover now