Motarsu ta gangara cikin Hotel ɗin, ta na tsayawa a wurin da aka tanada na ajiye motoci. Direban da ya kawo su a bisa umarnin Alhaji Isma'il, ya fito. Kafin ya buɗe masu Naseer ya fito itama ta fito. Sai ya zagaya ya fito masu da kayansu tare da wata katuwar jikka ta fata da basu san meye ciki ba da Hajia ta basu.
Wani mutum wanda alamu suka nuna ma'aikacin Hotel ɗin ne a dalilin kayan jikin shi da suke kala ɗaya da sauran masu giftawa, ya iso gabansu
"Naseer Dikko?"
Naseer ya gyaɗa mashi kai. Kayansu ya dauka ya na faɗin
"Nan hanyar"
Direban ya russuna ya miƙawa Nass makullin motar. Shi kuma ya saka hannu Aljihu ya dumtso kuɗin da bai san nawa bane ya miƙa mashi. Suka bi bayan mutunen.
Elevator suka shiga suka sauka a 3rd floor da shine na Vip. Room 10 ya kaisu yai masu lock security setting da fingerprint dinsu. Kallon kayan da ma'aikacin ya aje Nass ya yi
"To ba a dakko kayan duka ba"
Ya fadi ya na shirin kwalawa ma aikacin kira.
"Duka ne fa"
Ta bashi amsa.
"Ban ga akwatina ba"
"Wanne akwatin"
Ya mutse fuska yayi
"Ke kika hadashi da kan ki ko?"
"Ohh! Wai kayanka? Gasu nan ai hade da nawu"
Kallon ta yai ya kalla a kwatin, sai ya dauka kawai ya ida shigar da shi, ita kuma ta dauki dayar jikkar suka rufo dakin.
Fiddo kayan da ta san za su saka alokacin ta yi marassa nauyi ta a je a gadon, tasan wanka zai yi sai ya dauka. Bai daukan ba ya shige toilet din. Kayan da za su bukata irin su mai na shafawa da sauran tarkace duk ta kwaso ta jera a bedside. Ta na zage akwatin ya fito. Fiddo idanuwa ta yi duka akan shi sai kuma ta saka hannu ta daɗe idon gabanta na faɗuwa sosai. Ta yaya namiji zai yi mata tsaye a haka ɗaure da towel? Sai ta ga ya ƙara girma fiye da ko yaushe. Kallon ta ya yi yadda ta wani matse ido kamar ta ga dodo. Tunanin ko bata lafiya ya zo mashi a rai.
Takowa yayi har in da ta ke ya saka jikakkun hannuwan shi ya na raba hannunta da fuskar.
Gabanta ya fadi fiye da farko ta zame hannun ta ta maida a fuska
"Are you okay?
Ta girgiza kai.
"Meye to?"
"Kai ne ai"
"Na yi me?"
Yadda ya ke magana gab da ita na saka zucciyarta rawar da har a muryarta ta bayyana.
"Ka..matsa to. Ka saka riga"
Wata kalar dariya ta kubce mashi. Shi sam bai kawo ma ranshi wai don fitowar shi haka ta ke daddade ido ba. Miƙewa ya yi ya bar wurin. Kayan da ke bisa gado ya ɗauka ya zura sannan ya dakko cream ya fara shafawa.
A hankali ta dinga bude idon ta na lekowa ta cikin ramin hannu. Ganin ya saka kayan ta buɗe idon duka. Ta dauki nata kayan ta shiga wanka.
*******************"Amman ban taɓa sanin rashin hankalinki ya bunƙasa har haka ba Zinatu. Ah lallai kin nuna mini kin haifa Amina, ƙwarai na gani."
"Hajja ba haka bane wallahi, shi Khalid ɗin ya bugo yaman bayani..."
"Dallah rufe mani baki sakarya, Khalid din kanen baban ki ne iye? Na ce kane yake a wurin mahifinki da zaki sunkuci diyar da ya kusan halakawa ki miƙa mashi? Idan ke baki son ta ko kuma in ce abin duniya ne ya rufe maki ido to muna nan mu. Ba zan lamun ci iskancin ki ba wallahi. Dikkon ya dawo, ai sai da na faɗa mashi ya tattaro ya a gama bala'in nan da ke kunnowa ya wani ce sai watan nan ya kare, yanzu ga wata ɓarakar nan.

YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!