🖤💔🖤💔🖤💔
HAYAR SO©℘їηк¥🦋
Email:Oumarrabiatu@gmail.com
Kallon dakin ya ke yana son ya gano ina ke bai gyaru ba. Kayanta ya gyare mata su tsab ya jera. Duk wani harmutsin da ya tara a ɗakin ya share ya kwashe ya goge komai tsab. Ya canza kujerar da take kwana a da ya canza ta gaban gado da labulaye dakin ya dauki wani kalar kamshin da ya hade da sanyin AC. Ya gama shirya yadda zai tare ta tsab sannan ya kwashi kayan da zai shirya kwalliyar shi ya kashe fitilar dakin ya fito. Dakin Yaseer da har yanzu baya zama cikin shi yayi wanka ya shirya cikin farar shadda ya saka agogo ya gyara sumar kanshi ya fesa turare.
Duk bayan yan mintoci sai ya duba a gogo ya ga karfe nawa. La'asar, Magrib har isha'i shiru, sai dai yayi sallah ya dawo ya kara fesa turare. Ya zauna falo. Yaseera sai dariya take mashi. Su Amina duk suna wajen Umma da kullum sai sun je a kofar prison din suke yini.
Tara saura kwata Mami da murjanatu suka shigo don ko kofar falon a bude take bai rufe ba. Mikewa yayi tsaye yana leken bayan su a cen ya hango Fatima sai sunne kai take.
Kai tsaye wajenta ya wuce bayan ya gaida Mami bai ko jira ta amsa ba. Hannunta ya kamo tana zame wa yana jawo hannun har suka haye stairs Mami ta girgiza kai
"Marar kunya."
Sai da suka gaisa da Hajja ta faɗa mta zata tafi da Mami ita ma ya kamata a duba kwakwalwarta tun da har yanzu razanar abin da ya same ta bata sake ta ba, ko magana bata yi. Hajja bata musa ba Mami ta dauki Mom suka tafi da Yusrah.
Ya na buɗe dakin taja ta tsaya.
"Ya naga duhu?"
Ya dage kafada
"Kawai ki shiga."
Tana taka kafarta ya zura hannu ya kunna fitilar tare da kunna makyallin fanka. Kananun flower suka zubo suna watsewa a kanta. Juyowa tayi tana kallon shi da fadadden murmushi a fuskarta.
"Welcome Mon Cherie"
Ya fadi ta na buda hannuwanshi. A hankali ta taka ta isa ya rungume ta.
"Thank you. Thank you Zahra and Sorry. I'm very sorry"
Ta dago ta na girgiza mashi kai.
"Kana son nayi kuka?"
"Aa don Allah kuka ya kare Please,Okay?"
Ta yi murmushi. Ta dago idanun ta ta kalle shi ita yake kallo. Da hannu tayi maahi alamar ya duko, dukowar yayi ta kara da dage ta yi missing goshin shi.
"Wow!"
Ya faɗi ya na shafa wajen tare da lumshe idanuwan shi.
"Sai nan"
Ya nuna bakin shi. Hannunta gida daya ta saka ta rufe idanunshi tayi amfani da dayan ta tallabo keyar shi tayi kissing din shi na kusan minti ɗaya sannan ta sake shi.
"How sweet of you"
Ya faɗo ta na zagaya hannun shi ta kugunta ya jawo ta dab da shi. Zucciyarta sai tseren gudu take, ta damke yan yatsun kafafuwanta. Ya duko saitin kunnuwanta ya ce
"Ba kya jin yunwa?"
Ta saka hannu ta bugu damtsen hannun shi. Sannan ta dafe cikin ta
"Bayan ka hana ni cin abinci yau a gidan Mami?"
Yai dariya.
"Kin riƙe alkawari."
Ya faɗi ya na sakinta ya kama hannunta ya kaita kan kujera ta zauna. Gefen gado taga ya nufa sai gani tayi yana fitto kuloli da manyan bowls na abinci kala kala. Sai da yai shinfida sannan duk ya daura su.
![](https://img.wattpad.com/cover/270528964-288-k829669.jpg)
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!