"Ba zan iya tuna komai ba daga hadarin mu ban kuma san farkawata ba sai bayan watanni biyar kamar yadda baban da nake wajen shi ya faɗa mani. Ba muyi wani dogon zama da shi ba ya na ta shirin da zai maido ni gida kwatsam aka dira kauyen aka kashe mutanen su aka kwashe masu dukiyoyin su, sai suka tafi dani.."
"A takaice dai duk kina wajen su?"
Umma ta tambaya ta na katse dogon sharhin Nadra. Ta gyada mata kai.
"Ki share hawayen ki koma meye dawowar ki ita ce mai muhimmancin, yan gidan naku kuma sai mu jira dawowar su"
Ta gyaɗa kai. Mom juyawa ta yi kawai ta bar wurin ita sam labarin bai shige ta ba. Kwata-kwata ma ba ta hango yuwuwar labarin ba. 'wani kauye?' ta saki murmushin takaici. Koma meye ita zata gano gaskiyar. Shi yasa ta so a ace an samu iyayen Nadra din amman babu kowa a gidan sai masu gadin da ke shaida masu wai sun yi tafiya basa kasar ma kuma ba su san wace kasar suka tafi ba takamaimai. Sun dai fada masu tafiyar ta sati biyu ce zasu dawo. To tana nan ta na jiran dawowar tasun.
Bayan duk sun tafi ne sai Fatima kawai da ke tsaye cikin rashin masaniyar matsayinta ko abin da ya kamata ta yi. Don idan matsayin ta ne ai ta san bata da shi tuni. Abin da ya kamatan kuma bai wuce a tattara ta a maida gida ba tun da ga matar shi ta dawo. Ta dade ta na jiran ranar da za ta samu yancin fita daga harkallar Mom amman a yanzu zuciyarta cike ta ke da tsoron hukuncin da zai biyo baya.
"Baby"
Nadra ta kira sunan shi. Ya kalle ta. Fatima ta kalla
"Ban san ta ba"
Ta fadi da murmushi a fuskarta. Ya kalli Fatima ya ga ta kalle shi, ya juya ya kalli Nadra din ta tsare shi da ido ta na jiran amsar da zai bata.
"Zahra ce. Bamu jima sosai a tare ba"
"Ba ku jima ba a ina?"
Kafafuwan Fatima su kai wani kalar sanyi, a hankali ta dinga cira su ta na neman hanyar kofa. To ita a wa? Wacece ta shi? Zuciyarta ma ba ta shirya jin ansar da zai bayar ba. Sai dai cak! Kafarta ta tsaya a lokacin da ta ke shirin ida ficewa
"Matata ce."
"Mata Baby?"
Yadda ta ji sautin muryar Nadra kadai ta shaida tsabar kishin ta. Ta yi saurin ficewa hawaye na sauko mata.
"Antinmu"
Yusuf ya kira ta. Ta share hawayen da sauri.
"Ki yi hakuri. Komai zai wuce kin ji?"
Ta gyada mashi kai. Ya wuce.
*
Ta tashi zaune idon ta na kawo ruwa"Aure kayi? Matar ka ce ka ce?"
Ya kamo hannuwanta ya na girgiza mata kai.
"Ban san ki da wannan kishin ba Noor kar ki fara. Kar ki fara don Allah."
Ta zame hannuwan ta hawayen na saukowa.
"Shekara ukku fa? Ko biyar ba a yi ba bale goma har ka yi aure Baby? Ba za kayi tunanin kewata har ta wani lokacin ba kafin ka yanke hukuncin aure?"
"Ba zaki so ganin diyarki ba"
"Diyata?"
Ya kalleta da sauri cikin mamaki
"Ya Rabbi! Ta na ina? A kawo man ita in ganta don Allah"
Ta faɗi cikin sauri. Gyada kan shi yayi ya na barin dakin. Ya na fita ta saki ajiyar zuciya ta na dafe kirji. Bai jima ba ya shigo ya na rike da Ikky, ta taso da sauri ta rungumeta tsam ta na kuka.
"Ashe zan ganki?"
Ta faɗi ta na shafa kitson kanta. Ta dago ta kalla Naseer
"Wane suna ka saka mata?"
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!