Ta zagaye tsakar gidan yafi sai goma sha ɗaya da wayarta a hannu tana faman kiran Mom amman bata ɗaga ba. Ga tijara na cin ta amman tana tsoron abinda zai biyo baya idan taje Dikko Mansion musamman da ta kwana ta tashi da sanin muhaimmancin kudi da abin da zasu iya yi, ita kuma yan canjin da ake bata tana lamushewa basu isa sakawa ko hanawa ba a cikin garin Katsina. Fa'iza ta zo ta faɗa mata sakon Fatima da sauri ta ja hijabin ta dake saman kyauren daki ta zura habar zane a hannu tacewa Fa'izar muje. Gaban Dikko Mansion aka sauke su ta fito tai tsaye tana wasi-wasi a ranta. So take tsotsai ya fito mata da Mom amman har ta karaci zaman ta ga marece na karayi ga kuma Baba da ke cen police tsugunne. Da dai taga zaman ba zai kaita ba ga Fa'iza ba abokiyar fira ba balle suyi ta sababin tare, sai ta jata suka koma cen bayan gidan suka zauna tace ta latso mata Fatimah. Ta kira bata daga ba, Innar ta kwace wayar ta cigaba da danna kira amman shiru.
"Yo wai ita to mi take nufi da ba zata dauki wayar ba muyi magana? Idan ita wannan bakar matar taki dauka ita kuma ai diya tace ko"
Fa'iza tai mata shiru dai.
"Aiko dole ma ki ɗauka ki saka mijin ki ya zo ya fiddo Ubanki wallahi"
Ta cigaba da kiran amman shiru. Wasa-wasa har akayi magriba suna wajen. Fa'iza da duk abin duniya ya isheta abu goma da ashirin, bata san halin da Fatima take ciki ba bare Baba ga Inna ta ishe ta da mita da maganganun da basu da madafa.
"Inna Baba fa bai ci komai ba, ki tashi muje mugan shi don Allah"
"Eh kuma haka ne, yau na shiga uku ni Mariya"
Ta mike fuu! Fa'iza na biye da ita suka samu Napep. Suna shiga gida suka yi sallar magriba da sauri Fa'iza ta dafa mashi Shinkafa jallof don ta san ba son taliya ya ke ba. Sai cen wajen tara na dare dai a takaice suka fito suka isa police din da Fatima ta fadi. Sai da aka gama ja masu rai kafin ace su shiga amman dakin da aka ce yana cimi sai wayam! Ba kowa a ciki.
"Yo wai yana ina kuma"
"Malama ni dai na san yana nan har mintuna biyar da suka wuce don nine ma nake da makullan dakin, to daga nan kuma ban san ya akai ba. Wai bai ciki?"
Ya kara da tamabayar da ta hayaka Inna matuka.
"Yana ciki bango ya tsaga ya shiga"
Ta fadi tana huci.
"Allah baki hakuri kila an fidda shi ma ai"
Ya fadi yana tafiyarshi. Duk wanda suka tambaya ba wata cikakkiyar amsar in da Baba ya ke. Nan fa hankalin Inna ya miƙe ta dinga zarya kowane daki da tambaye-tambaye amman babu shi ba labarin shi. An dai ce an sake shi amman wanda ya fitar dashi ne babu amsa.
*********
Tana tafiya tana kuka har ta fita gate din gidan. Karo suka ci da Murjanatu ta tsaya tana kallon ta cikin mamaki"Zahra lafiya?"
Ta kamo ta. Zamewa Fatima tayi zata wuce Murjanatu ta kuma riketa.
"Rasuwa akai? Waye ba lafiya? Mu koma ciki don Allah"
Ta girgiza mata kai.
"Ba zan kuma shiga ba"
"Shiga ina? Cikin gidan wai?"
Ta gyada mata kai.
"Okay muje gida."
Wayarta tafiddo ta kira direban gidan su da baiyi nisa ba tace ya dawo. Daman zuwa tayi taji yaushe za suyi registration din Nursing school din da suka samu tun da Fatimar ta faɗa mata an bata Admission ita ma. Gidan su Murjanatun suka koma. Mamy na kitchen taji sallamar Murjanatu ta leƙo zatai magana ta ganta da Fatima tana kuka.
![](https://img.wattpad.com/cover/270528964-288-k829669.jpg)
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!