41

311 18 2
                                    

Ƙafar da ke takawa  ta tsaya cak! Ta na mata wani kalar sanyin da in ba don Murjanatu ta tare ta ba tsab zata faɗi.

"Subhanallahi! Bata lafiya ne?"

Cewar Hajja ta na miƙewa tsaye. Da ƙyar ta ida jan kafarta ta isa wajen su ta sunkuya ta na gaishe su da harshen ta mai nauyin da take jin kamar an aza mata dutse, haka ma zuciyarta. Gabanta na tsananin faduwa ta ke fatan ace kunnuwanta ba daidai suka jiyo mata ba.

"Sannu Zahra"

Hajja ta sake faɗi ta na kamata ta zauna. Ita ma zaman tayi, sannan ta kuma maida hankalinta wajen Baba.

"Ka fahimci wani abu, kamar yadda ka ji abun nan daga sama muma hakan ne daga gare mu..Yaron nan wallahi ya sha wuyar da a ko yaushe zuciyarshi zata iya bugawa, ka faɗa min idan laifi nayi don ina son binciken lamarin, ka fada min idan kai ne ba zaka bi duk hanyar da kake ganin zaka bi ba don sanin in da lamarin ya fara?"

Ta ɗaga kai ta kalli Fatima da ke duke gabanta na wata kalar faduwa ba na wasa ba, ta ce

"Kalli diyar nan"

Baba ya juya ya kalle ta.

"Ita ta haɗa auren? Ita ta kai kanta? Aa ko? To kamar yadda akai mata dole, ni da kai da shi mijin babu wanda ya san ta kan maganar ma gaba ɗaya. Shin ta yaya zaka cara hukuntashi da laifin wasu?"

"Ba ina nufin hukunta shi bane, kamar yadda kika ce anyi auren nan ba tare da sanin mijin ba, a yanzu zan tafi da ita ne don sawwaka ma su dukan su.."

Hajja ta yi saurin katse shi.

"Kana tunanin shi suka fi so bu biyun? Ka tambaye ta shima hakan idan sun musa to bani da hau ka raba auren."

Kallon Fatima Baba ya yi. Ya mira sunan ta.

"Fatima"

Ta ɗago ta kalle shi.

"Ki ma son Mijin ki?"

Da sauri ta maida kanta ta sadda.

"Ni ba zan yanke maki hukunci ba kin sani, wahalar da kika sha nake hango maki karshenta, idan har kin san baki son shi ki fada min in tafi dake"

Ta na jin yadda kowa ke kallon ta a wajen.  Bakinta yai wani kalar nauyin da ta dinga motsa shi kawai.

"Ke muke saurare Zahra"

Cewar Mami ta na taɓa kafadarta.

"Baba duk yadda ka yi ni yayi min"

Ta faɗi dakyar cikin wani kalar kaffin hali. Ta yaya zata furta son wani agaban idanu haka? Ba zata iya ba, hukuncin kuma ta barwa Baba idan ya ce ta bishi zata bishi gidan.

"Zahra"

"Na'am"

Ta fadi tana kallon saitin da aka kira sunanta. Baban su Murjanatu ne.

"Ki tashi ki tafi, duk hukuncin da aka yanke za a sanar da ke"

Mikewa tayi har tana haɗawa ta bar wajen. Wane kalar hukunci zasu yanke mata? Zuciyarta ba zata taba natsuwa ba ta sani idan har bata ji makomar ta ba.

'Ban son kara ganinki Zahra'

Maganar Nass ta ratso cikin kanta. Ta runtse idonta. Ta san babu wani hope akan komawarta, shi da kanshi ya kore ta daga kusa dashi.

Sai da ta goge kwallan da suka zubo mata sannan ta shiga dakin.
**

Shiru shiru bata ji wani ya kara kiranta ba har bayan isha'i, har lallabowa tayi ta je kicin ta sha ruwa kowa ya watse ma. A sanyaye ta dawo daki ta zauna. Suna fira sama-sama da bata gane rabin abin da Murjanatu ke cewa aka kira wayar murja ta tashi ta fita.

HAYAR SOWhere stories live. Discover now