33

303 18 3
                                    

A ruɗe ta yanki titi ta fara tafiya tayi nan tayi cen ta rasa in da zata dosa. Hasken mota ya dallare mata fuska ba shiri ta saka hannu ta kare tana yin baya zata faɗi tayi karo da mutum. Ruƙota ta ji anyi ta buɗe baki zata fasa ihu ya ɗaura hannun shi a bakin.

"Shhhh! Ina za ki je haka?"

Da sauri ta juyo ta na kallon fuskarshi cikin hasken motar, ba tare da tunani sau biyu ba ta rungume shi ta na fashewa da wani kalar kuka cike da shessheka. Ya saka hannu ya ɗagota ya na kallon fuskarta da tayi sharkaf da hawaye.ya goge mata hawayen sannan ya ce

"Me ya fito dake?"

"Ban ganka ba ai"

"Sai akayi yaya?"

"Na fito in dubo ka, kuma sai naƙi ganin ka sai agogonka"

Ta faɗi ta na ɗago agogon. Hannun shi ya fara kalla ya ga babu agogon ba zai ce ga lokacin da ta faɗi ba. Ya karɓi agogon ya kamo hannunta ya ɗaura mata ita sannan ya tallabo fuskarta ya na kallon cikin idanunta da suka rine da kuka.

"Waye ya ce ki fito don baki ganni ba?"

Ta kyafta idanu ta na turo labbanta.

"Ki na zaton za a sace ni ne?"

Kamar ta ce saboda Zuly ne, sai ta tuna yadda suka kwashe don haka kawai ta kuma turo labba ta yi shiru sabbin ƙwalla na cika idanunta.

Janye hannunwanshi yayi daga fuskarta ya zagaye jikinta dahannunshi ɗaya ya rungumota,ta damƙe gefen rigarshi ta na sakin sabon kuka.

"Na gode. Na gode Zahra kuma kiyi haƙuri"

"Babu abinda ya same ka? Ina kaje?"

"Duk ni kaɗai zan ansa?"

Ta gyaɗa kai.

"Babu abin da ya same ni, na je dai-daita wani abu ne da kika so in yi na kasa fahimtar ki"

Ta ɗago ta kalle shi.

"Kiyi haƙuri"

Ya ce mata.

"Ta yaya ka sani?"

"Ta tsoron da ta dinga baki."

Ya kama hannunta yace

"Mu tafi gida"

Ta juya ta kalla baya

"Su Mufida fa.."

"Suna da mazaje"

Ya katseta. Shiru ta yi har suka isa ga motar ya buɗe mata,ta shiga. A hanya yai mata bayanin hoton kungiyar Black shadow da ta gani a gidan Umar.
**

Akan idanun Umma suka shigo, haka Mom ma. Kowaccen su da kalar tunaninta na cimma manufa.
  Suna shiga ɗaki ya kalleta fuskarshi ɗauke da murmushi ya ce

"Ga dakin ki nan anbar miki"

"Ɗakina?" Maganar ta kubce mata.

"Ba dakinki bane?"

Wani haske taji ya gilma ta cikin idanunta ta gimtse dariyar farincikin da tazo mata. Ya girgiza kai yana ganin zallar yarintarta.

"Barin ɗakko Ikram"

Ya gyaɗa mata kai. Fita tayi ta je dakin Hajja, zaune ta iske su suna fira da Amina.

"Auntyn mu ce, bamu taɓa haɗuwa ba"

Aminar ta faɗi ta na kallin Fatima. Ta yi murmushi ta gaishe ta. Zama ta yi suka ɗan yi fira duk su ukun, ta fahimci Amina nada kirki sosai.

"Ikram ta yi bacci ne?"

HAYAR SOWhere stories live. Discover now