Kaf! Ta bi dakin da kallo tare da kasa kunnuwanta amman ba ta kuma jin maganar ba. Takalmanta ta ɗauka a hannu ta haye sama abin ta.
Ajiyar zuciya Fatima ta aje, ta na mikewa daga bayan kujerar da ta yi hanzarin laɓewa. Mamaki sosai ta ke yi na daga ina za ta dawo a tsohon daren nan. Lokaci ɗaya tsoro ya kamata ta ruga da gudu ta koma ɗakin Hajja.
Baccin da ba ta koma ba kenan tsawon daren. Sai bayan da ta yi sallar asuba ne ta kwanta bacci ya dauketa
***Karfe goma na safiyar ta tashi. Ikky ta gani kwance kusa da ita ta na bacci. Ta yi murmushi ta na son yarinyar sosai. Gyara mata kwanciyarta ta yi ta fito jin hayaniya a falon. Duk a tsaye ta gansu sun yi cirko cirko, sun zagaye Amina da ke durkushe ta na kuka.
"To kallon me za ki yi mata kuma bayan kin aikata wajen mugun ya ida kasota? Sai ki maida ta gidan uban Khaleel ɗin a yanzu da ya ida sako maki ita, tun da ke baki san abin da ya ke miki ciwo ba"
Cewar Hajja ranta a ɓace. Ta duka ta kamo Amina ta ɗago ta
"Subhanallahi jini? Kai wannan abu bana lafiya bane"
Ta kalli in da Adam ya ke
"Maza kira mani Yusuf ko Naseer"
Aysha da Yaseera su ka kamata su kayi waje da ita su ka yi mota da ita. Kafin su gama saka ta Naseer ɗin ya fito da sauri Nadra na bayan shi duk in da ya dauke kafa ta jefa tata.
Ya na shiga motar Adam ya shiga gaba suka bar gidan. Hajja ta shiga wata motar ta na shaida masu su jira har su dawo.
Ran Umma a ɓace sosai ta wuce ɗakinta, kowa ya kama gabanshi cike da jimamamin halin da yaruwarsu ke ciki. Fatima ma dai jiki a sanyaye ta wuce. Har ta nufi kitchen kuma ta ga gara ta fara dakko kayan da za ta saka idan ta yi wanka,sai ta wuce ɗakin su."Lafiya?"
Nadra ta ce mata ta na bin ta da kallo, a madadin ansa sallamar da Fatima ta yi. Ta bi hannun ta da ta ɓoye a baya da kallo, ba za ta iya ganin ko meye ba amma ta shaida baki ne.
"Lafiya?"
Ta sake maimaitawa wannan karon ta na duƙewa ta saka abin da ta ke ɓoyon a jikka.
"Kalau"
Fatima ta amsa ta na ida shiga ɗakin.
"Ƙalau?"
Nadra ta faɗi da sigar mamaki da kuma murmushin da bata gane makasudin shi ba. Ta gyaɗa mata kai.
"Ƙalau kuwa"
Ta kuma yin murmushi.
"Wan da kike nema baya nan"
"Na sani"
Ta bata amsa. Da mamaki ta ke kallon Fatima, yar karama da ita za ta dinga bata ansa haka kai tsaya. Kallon ta ji yai mata yawa ta wuce kawai in da kayanta suke ta buɗe wardrobe ɗin ta zaro duk abin da ta ke buƙata. Har ta kusa fita ta kuma jin maganar Nadra
"Na zaci duka kayan za ki kwashe"
"Me yasa hakan?"
"Saboda na dawo"
"So?"
Ta yi murmushin da ya fara bawa Fatima haushi.
"Can't you tell? Ni ce matar shi, kuma ni ya ke so, ni kaɗai"
Fatima ta yi dariya.
"Ki tabbatar da hakan don Allah"
Ta sa kai za ta fice. Fizgotan da ta yi ya saka ta juyowa ba shiri.
"Kin san wacece ni?"
"Ko ba ki faɗi ba na san tsinto ki akai a hanya, ko in ce kike jefo kanki a rayuwar da ba ta ki ba"
![](https://img.wattpad.com/cover/270528964-288-k829669.jpg)
BINABASA MO ANG
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!