32

276 14 1
                                    

Hawaye masu zafi suka zubo mata hannuwanta na kyarma ta duƙa cikin rashin sanin abinyi ta fara tattare takardun, ta na kwaaowa su na zubewa ƙasa. Hannuwanta ta ji an riƙe ta ɗago ta kalle shi yai murmushi ya karɓi takardar hannunta ya ɗago ta ta miƙe.

"Me ya faru?"

Ya faɗa ya na share hawayenta. Ta gyaɗa mashi kai

"Ba komai"

Murya a sarƙe. Hannunta ya saki ya bude kayanta ya ciro mata Abaya ya mika mata.

"Saka"

Ganin yadda hannuwanta ke kyarma ya taimaka mata ta zura, ya miko mata takalmanta ta saka. Ya kalli Zuly da ta daskare gabanta na faduwa sosai ko ya ji maganar da su ke. Murmushin da yayi mata ya saka ta saki ajiyar zuciya har su na ji.

"Ina dawowa yanzun"

Ya faɗa mata ya na kama hannun Fatima su ka bar ɗakin. Ta ɗage ƙwayar idon ta ta na bin su da kallo. Ta juyo ta halba jikkarta da har lokacin ke kasa sannan ta zauna daɓas ta na warware gashin kanta ta na ja.

A kan idon Safwan suka wuce hannunta cikin nashi. Idanun shi suka sauya kala ya shige dakin shi daman daga makaranta ya dawo.
  
Shi ya buɗe mata mota ta shiga sannan ya zagayo ta ɗayan ɓarin  ya zauna kusa da ita.

"In ɗakko Ikram?"

Ta ce ta na kallon shi.

"Ta na wajen Umma ta yi bacci"

Gyaɗa kai kawai ta yi. Aka buɗe masu gate su ka fice. Unguwar su Umar ya faɗawa direban, da suka shiga unguwar ya dinga gwada mashi hanya har su ka isa. Ya cewa direban ya tafi kawai. Su ka shiga.

"Oyoyo ga Amarya, yau ranar ta mu ce kenan"

Mufida matar Umar ɗin ta faɗi. Wuri ta gwada masu suka zauna duk da Naseer ba bakon gidan ba ne, su ka gaisa ta kawo masu ruwa da lemo sai snacks.

"Yanzun nan na ga ya fita ba kuyi waya ba?"

"Mun yi"

Ta gyaɗa kai ba ta kuma cewa komai ba. Ta riga ta saba da halin Naseer din a cikinsu shi ba mai tsawaita magana bane. Basu dade ba Umar din ya shigo ya na ta tsokanar Fatima su ka gaisa. Mufida ta ja Fatima suka shiga bedroom ɗinta a cen ta dinga janta da fira, acikin firar ne ta ke jin wai wani biki gare su na abokinsu da su kayi karatu tare a yau cocktail party ake yi bayan isha'i shi yasa ma aka kawo ta don su haɗu da matar Yusuf su shirya su duka.

"Na cika ki da surutu barin kawo miki abinci"

"Bana jin yunwa fa"

Ta faɗi. Har yanzu ita hankalinta ba duka ya ke jikinta ba tunanin yadda za ta kare Nass daga Zuly ta ke.

"To ki ci ko cake ɗin barin ɗakko miki, nan fa gidanku ne kema ki saki jijinki don Allah amarya"

Ta dan yi murmushi kawai, ita ai ba a binta bashin magana in banda halin da ta ke ciki da yanzu ta tabbatar ta fara gundurar Mufida da surutunta.

Paper da ke aje bisa gadon ta ɗauka ta na wasa da ita har Mufida ta dawo da cake ɗin ta aje mata.

"Wannan zane ai bala'i ne"

Ta faɗi ta na kallon paper hannun Fatima. Lura da hakan ya saka ta juyo da ita, zanen shahon da ya buɗe baki ne mai jela.

"Dabba ce ai"

Cewar Fatima ta na kallon zanen.

"Ta Black shadow ba"

Fuskar da Fatima ta yamutsa cikin rashin gane zancen Mufida ta fahimci ba ta san komai a kai ba. Cikin mamaki ta ce

HAYAR SOМесто, где живут истории. Откройте их для себя