25

257 14 5
                                    

Kwance ta ke ta mimmike a gado ta na sharar bacci hankalinta a kwance luf, ta na tashi daddaɗen labari ne zata ji. Shiyasa ma ko kaɗan ba tayi nesa da wayarta ba ta ke aje gefen filo.

"Umma..Umma ki tashi"

Ta ji ana jijjiga ƙafarta cikin bacci. Rai a ɓace ta ɗago ta na kallon Aysha da hankalinta ya ke a tashe.

"Lafiya?"

Hanyar waje ta nuna mata da hannu ta na kasa magana saboda shesshekar da ta ke.

"Don Allah ki kyaleni Aysha"

Ta faɗi ta na kada kanta bisa filo.

"Aunty Am..mina ce"

Ta sake faɗi ta na taɓa ƙafarta.

Gaban Umma ya faɗi.

"Meya samu Aminar? Ta na ina?"

Hanyar waje ta nuna mata. Da sauri Umma ta wantsalo daga gadon ta bi bayan Aysha da ta riga ta fita. Aminar ta gani Mom rungume da ita ta na jijjiga ta, yan gidan duk suna tsaye a kansu cirko cirko da fuskar damuwa.

"Ki faɗa mani meke faruwa Amina kina tada mani hankali..."

Umma ta matso ta fizgo Aminar daga jikin Mom. Koma meye ba mai daɗi bane bata son ta faɗe shi a gabanta. Gaban umma bai sake faduwa ba sai da ta ga fuskar Aminar a kumbure duk jini ya kwanta kasancewar ta fara don duk ma ta fisu fari a gidan. Ga gefen bakinta a fashe, tsintsiyar hannayenta duk shatin bulala ya farfashe.

"Ki bita a sannu Ummansu, baki ga halin da ta ke ciki ba?"

Mom ta sake faɗi ganin yadda Umman ke janta da sauri jikinta sai rawa ya ke su samu su bar falon.

"Umma Khaleed ne.."

Ta faɗi cikin kuka.

"Khaleed ne Umma. Saboda mace yai mani dukan nan, mace karuw..."

"Ki nutsu na ce ko?"

Umma ta daka mata tsawa jikin ta na ɓari tare da addu'ar duk da ta zo bakin ta akan Mom bata ji ba. Sai dai babu in da addu'ar tata ta je don kuwa salatin da Mom ta rabka sai da Hajja ta fito.

"Lafiya? Me kuke yi haka?"

Sai lokacin ta lura da Umma da ke jan Amina ta kusa shigewa ɗaki.

"Ke Zinatu lafiya? Sakarta mana"

Kamar Umma za ta sa kuka ta saki Aminar.

"Innalillahi wa inna-ilairraji'un! Me zan gani haka ni Sa'ade, hatsari kika yi ne a hanyarki?"

"Hajja duka ne"

Mom ta faɗi da sauri.

"Duka? Wane irin duka ne haka kamar anyi hatsari da ita, to ubanwa ye yai mata haka?"

"Mijinta"

Mom ta kuma faɗi. Umma kamar ta fasa ihu ta ke ji. Takaicin duniya ya gama rufeta. Yadda ta ke taƙama da mijin Amina a gidan nan kowa ya sani, ga kyau ga tarin dukiya. Don ko kaɗan Abbu ba zai gwada ma uban Khakeed dukiya ba sai dai shi ya gwada mashi. Shiyasa duk wani dan ƙorafi idan Amina za ta bugo waya ta faɗa mata ko idan ta zo Ummar bata wani sauraro, ba dan bata tsananin ƙaunar ta ba a'a sai don tana tsoron abin da zai rabota da Khaleed su ji kunya.

Kamo hannuwanta Hajja ta yi tana cigaba da doka salati. Ta zaunar da ita a kujera.

"Yaseerah dakko ruwa"

Ruwan ta kawo, Hajja ta buɗa ta bata ta sha.

"Shi Khaleed ɗin ne yai miki haka?"

Ta gyaɗa kai.

HAYAR SOWhere stories live. Discover now