Ƙafafunta su ka sage da gajiya ta dinga buga ɗakin da karfin gaskenta.
"Me ya faru ne?"
Ta ji an fada a bayanta. Ta juyo ta kalle shi da murmushin yaƙe. Yusuf ya girgiza kansa kawai ya san a rina ai in dai Naseer ne. Fitowar shi kenan daga ɗakinsa zai sauka ƙasa ya ganta ta na ta faman buga ɗakin."Ina zuwa" Ya faɗa ya na daddana wayarshi ya kara a kunnai
"Yaaya mana ka buɗe ƙofar in ji Mom"
"Ga ta nan tsaye tun ɗazun"
Ya kashe wayar. Ba ayi minti ɗaya ba kofar ta buɗe Nass ya leƙo. Lellekawa yayi bai ga Mom ba ya kalla Yusuf
Da sauri ya riƙe kunnuwansa yai saurin barin wurin. Ya na dafa ƙofar ta yi saurin bi ta cikin hannuwansa kamar yar mage ta shige ɗakin. Juyowa ya yi ya bita da kallo ya kalla ɗan saƙon da ta bi a hannun nashi kafin ya rufe kofar.
Ta na tsaye riƙe da ƙugu ya zo ya wuce ta.
"To me nayi ka rufe min kofa?
Bai juyo ba har ya isa ga bookshelf ya ɗakko wani littafi 'This is for real' na James Hadley chase ya zauna a karamar kujerar wurin.
"Za ka fita kai ma sai na rama"
Ta faɗi ƙasa-ƙasa ta na turo baki.
"Ki kwatanta"
Ta ji ya faɗi. Ta yi saurin kallon shi, littafin ya ke kallo abin shi. Ta koma ta zauna ta na rasa abin da za ta yi kuma
Da rana Yusrah aka ƙara aikowa da abinci. Ganin idon Naseer ya saka ta gaishe da Fatima ta aje basket ɗin ta ɗauki na safe ta fita. Ba ta ce mishi ya ci ba tun da ɗazu ma gwale ta ya yi, ta sauko ta buda kular. Farar shinkafa ce sai dai ba zata ce ga sunan miyar ba, tsanwa ce shar da rashin ƙamshin daddawa ya hana ta kira ta da ta kuka, ta sha carrot da yankakkun naman kaza a ciki.
'Tashin hankali' ta fadi cikin ranta ta na zuba shinkafar kaɗan, miyar ta ɗebo ta ga kamar miyar kuka ta debo saboda yauƙi. Haka nan dai ta zuba cokali ɗaya ta yi ta aje cokalin ta na raba ido. Sam ba ma za ta iya cin abincin nan ba. Da safe ma ban da Allah ya saka an hado da dankali da babu abin da za ta ci. Fridge ɗin dake gaban gadon shi ta je ta bude. Sai da ta ɗan saurara ta ji bai ce mata komai ba kafin ta yi ajiyar zuciya ta ɗakko lemon da ba ta san ko sunanshi ba a yar karamar kwalba. Har ta taso ta yi tunanin yadda za ta bude lemon ma tashin hankali ne ta yi saurin maidawa ta ɗakko ruwa ta koma ta zauna. Ba jimawa ta ga ya mike ya fita. Ya daɗe bai shigo ba don har ta gama sallah ta zo ta kara jujjuya abincin ta kasa ci ta hakura ta zauna haka nan ta na gyangyadin dole.
Cikin ɗan baccin da ya fara fizgarta ta dinga jiyo kamshi sama-sama ta buɗe ido. Nass ta gani ya na cin abinci ba kalar nata ba. Da sauri ta tashi zaune ta na mirtsika ido cikinta ya ɗau ƙara.
Ta daɗe ta na tunanin yadda za ta yi kafin ta yi karfin halin ce mashi"Kaji.."
Ya juyo ya kalleta.
"Zan ci abincin ka"
Rasa mai zai ce mata ya yi ya cigaba da cin abincin shi, to ba ga abinci nan a gabanta ba don gulma ta ce nashi za ta ci. Yadda ya ji cikinta na ƙara ya bashi mamaki.
"Plate ɗaya na girka ni"
Ta tsinto muryar shi bayan ta fidda ran zai tanka ta.
"To ka rage mini"
Abincin gabanta ya kalla ya ga an zuba ba a ci ba. Kenan bai mata ba? Yai murmushi cikin ranshi, ya riga ma ya koshi amman ba zata ci ba ko zata mutu kuwa. Haka yai ta ci, ya cinye tas ya aje plate din ya na kallon ta ta gefen ido kamar za ta fasa kuka.
*********
![](https://img.wattpad.com/cover/270528964-288-k829669.jpg)
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!