Eyes,
Which used to dream together,
Eyes,
Are now crying relentlessly on being separated.
~~~~~
"Assalamu alaikum"Mamman wanda yafi kowa rashin mutunci a duk cikin securities din Abbu ya buga sallama ya na buga kyauren gidan su Fatima. Baba da shigowar shi kenan gida ya shiga ya kama ruwa zai ci abinci ya ji tashin sallama ya fito.
Mamman bai bi takan gaisuwar da Baba ke mashi ba, kai tsaye ya ce
"Kai ne Malam Sule?"
"Ni ne"
Baba ya amsa
"Uban Fati wacce tayi aure?"
"Ƙwarai kuwa"
"Toh!toh!! Kai ne kayi wa yarka auren ha'inci domin kudi ko? Kai ne ka lailaya karya a rayuwar bayin Allah ka yaudare su da auren 'yarka ba tare da su din sun san ko wacece ba ko?"
"Ban gane kan maganar..."
Mamman ya damƙi wuyan rigar Baba ya ida fito dashi cikin lungun.
"Ai ba zaka gane ba, amman yanzu zaka gane sai ka fara koro bayani dalla-dallah"
Ya na kwacewa Mamman na janshi ƙii! Kamar sabuwar Akuya. Inna ta fito da sauri habar zanenta a hannu.
"Kai Innalillahi me zan gani haka? Don Allah ku sake shi, me yayi maku?"
Kallon sama saura aka watsa mata dayan su yace
"Hukuncin auren yaudarar da yayi me zai karɓo"
Daga haka suka tusa ƙeyar baba gaba, kan shi ya kulle sam ya kasa fahimtar in da abin ya dosa. Duk da ya dauki hakan a matsayin rashin fahimta aka samu, duk ma in da zasu kai shi idan sun ga bashi bane ai zasu maido shi ne.
***********
"Madam lokacin da kuka diba ya kare tun dazun"Muryar wata inyamura ta ratso mata kai.
Wayarshi da ke yashe a ƙasa ta jawo ta riƙe sannan ta miƙe dakyar idanunta a kimbure ta fara takawa a hankali tana barin wajen. Tafiya kawai take hankalinta sam baya jikinta tunaninta kaf ya bace mata. Sai da wani mai mota ya kusan bigeta ne ya fito yana hargagi kafin ta dago ta kalle shi."Ka kai ni gidan Dikko"
Kawai ta fada mishi. Yadda tayi maganar tana kauda kanta gefe ta cigaba da tafiya ya sakashi fahimtar bata ma cikin hankalinta. Shi ya fita ya shigo da ita motar ya tambayeta unguwar da zata.
"Nace maka Gidan Dikko,GRA"
Ta fadi a tsawace kamar zata hade shi.
Sai a lokacin ya fahimci Dikko Mansion zata. Bai kuma tambayarta ba ya kaita har kofar gidan ya aje ta ya tafi. Shiga tayi, kamar yadda Nass ya wuce su hakan ita ma ta wuce su ba tare da ta fahimci akwai wani a dakin ba. Umma ta bude baki zatai magana Hajja ta girgiza mata kai.
"Ki barta tukun"
Dakin ta bude ta shiga. Ya na zaune kasa kanshi sadde bisa gado. Har ta iso in da yake bai dago ba. Ta duƙa ta na taɓa kafadar shi. Wani kalar juyowa yayi ya zuba mata idon shi da sukayi jazur.
"Tashi ki bar nan tun kafin raina ya ɓaci"
Ta kalli hannun shi da ke fidda jini duk ya daskare. Ta jawo hannun ya fizge.
"Za kaji ciwo ka bari in gyara ma"
Yai mata wani kallin baki da hankali.
"Ciwo? Har wane kalar ciwo kike magana kuma?"
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!