01

660 23 0
                                    

2018

La'asar sakaliya gari ya yi luf-luf sai iskar damina  ke kaɗawa da ke nuna alamun ruwa bai daɗe da ɗaukewa ba. A cikin jerin gidajen da ke tsukakken lungun da katuwar kwata ta cinye rabin hanyar, dan haka gidajen suke cen mak'ure a jikin bango sun yunƙuro kamar zasu faɗo cikin kwatar da ruwan da aka gama ya cikata taf-taf ya na gudu har yana shiga cikin gidajen ya na had'uwa da waɗan da ake ƙokarin korowa daga ciki.

"Fatima ki maida hankali ki sharta da kyau kokuma su dawo.. Ƙara tura ƙyauren"

Cewar wata dattijuwar mata da shekarun ta ba zasu haura talatin da takwas ba, amman kallo d'aya za ai mata a zaci ta ba hamsin baya saboda wahalar rayuwa. Ta na rik'e da wani tsohon kwano ta na kwalho ruwa ta na watso shi waje. Yarinyar da aka kira da Fatima  kuma ta na duk'e da tsintsiya ta na faman sharce ruwan.

"Innarmu ruwan yau yafi koyaushe yawa gaskiya."

Fatima ta faɗi sa'ilin da ta ke tura ƙyauren ji kake ƙiiii! saboda tsabar ruɓewa da danƙarewar da ya ke yi kamar bai son wucewa a duk sadda za'a bude ko a rufe gidan.

"Ai da an cigaba da ruwan nan inaga mu kanmu sai mun yi iyo a ciki. Ko ina ubanki ya tsaya har yanzu, yadda aka tsula ruwan nan mai makon ya dawo sai ya samu wuri ya shantake"

Fatima ta had'e rai. Bata son irin kalaman nan na innarta akan Babanta ko yaushe, ta na yi kamar bata san duk ma inda ya je domin su bane, miye laifin shi idan ya je fafutuka dan samowa iyalinsa abinci?
Su talakawa ne fitik da idan aka ci na yau sai an nemo na gobe, sannan basu cika samu su ci abinci sau ukku a rana ba. Babanta bai da wata tsayayyar sana'a sai 'yan bige bige sannan ya na dagewa iyakar yin shi dan ganin ya saka farinciki a zukatansu, amman dai-dai da rana d'aya Inna bata tab'a yabawa k'wazon shi ba. Mace ce marar godiya da tsanar yanayin da suke ciki. Babu ranar da zata zo ta fad'i bata goranta ma Baba halin da suke ciki ba, takan ce

"kai dai baka da buri Sale,Shekara da shekaru ka kasa samar mana rayuwa mai kyau. Nidai na yi zab'en tumin dare!"

A duk sadda tai wannan maganar Fatima yini take k'unci da fushi ga mahaifiyarta. Hakan kuma bai shalli Inna ba.

A yanzun ma da Fatima ta ji Inna na k'okarin fara yankar bakaken maganganu ga Baba sai cewa ta yi

"Innarmu ki koma cikin gida zan ida kore ruwan tun da sauran kad'an."

Ganin sauran kaɗan ɗin ta yadda kwanon hannun ta ta koma ciki dan ta kimtsa tsakar gidan da ruwa yai watsi da kayakin su.

Ta sauke ajiyar zuciya ganin ta tafi, ta ci gaba da aikinta. Sai da ta tabbatar ta kore ruwan tsaf ta share kafin ta mik'e zata shige gida.

"Fati.."

Kallon da ta watsa ma yarinyar da ta leƙo ita ma da tsintsiya hannunta, ya saka tai shiru ba tare da fad'in abin da ta yi niyya ba.

"Ba dai na hana a ce mani haka ba ko baki bari, to na rantse da Allah yau muka je makarantar dare sai na bi kaf k'awayenmu na ce Zainabu Abuu sunan ki kuma har Abulle ma ana ce miki a gida"

Ta fad'i ta na riƙe ƙugu. Da sauri Zainabun ta saki tsintsiyar hannunta ta raɓo ta ƴar hanyarsu ta iso gaban Fatima.

"Don Allah ki yi hak'uri suɓutar baki ne, daga yanzun nan nayi maki Alƙawarin ban ƙarawa"

Idan a kwai abin da ta tsana duniya to a datse mata sunan ta a ce fati, ko waye zai ga fushinta. Shiyasa a bokon su har islamiyya babu mai kiran ta da Fati, hatta su Innar ta ma kowa ya kwanada sanin hakan. Kasancewar su Aminnan juna ita da Zainabu tun yarinta har zuwa yanzu da suka zana JSCE a boko da shekarunsu sha shidda, sai Zainabu ta dauki darasin Fatima ita ma bata son Abulle da aka fi yawan kiranta da shi gidansu Ko ace Zainabu Abuu. Dakyar da sid'in goshi da kuma taimakon Fatima aka bar fad'in Abulle sai dai Zainabu ya kama bakinsu maimakon zainab kawai da tafi so.

HAYAR SOWhere stories live. Discover now