You may be apart of my thoughts someday, while sometime you might be lost.
Arjit Singh
~~~~~
"Ba za ki yi bacci ba?"Ya faɗa cikin rashin sanin abin da zai faɗa, da kuma shirun da yai yawa a tsakanin su tun da su ka dakko hanya. su na gama a suba suka taho so ya ke su isa sa wuri duk da dai nisan da ke akwai, a ranshi ya gama yanke hukuncin tafiya mai nisa ta karshe ce zai yi. Yadda ya ga tayi shirun nan ke bai mashi daɗi, tun daga ranar da tayi kuka ya san akwai abin da ke damun ta kuma duk idan ta zauna shiru haka sai ya ga damuwar ce. Bai mata magana bane don baya son takurata ko tsallake iyakarshi, idan ta bukatar taimakon shi zata faɗa mashi da kanta.
Ta gyara zaman ta da yar mikar gajiya."Na yi bacci sosai, yanzu ban ji"
"Za ki sha sweet?"
Ta gyada kai.
Gangara motar yayi daidai wani shago da ke kan hanya. Ya ce
"Mu shiga"
Fitowa su kayi su ka shiga shagon. Wata yar kwana ta bayan kanta ya samu ya tsaya ya na harde hannayen shi,ita kuma ta wuce ta na abubuwan da suka birgeta a ido.
"Sannu yammata"
Ta ji an faɗa a bayanta. Ta juyo har ta na firgita da tsayuwar shi wurin. Saurayi ne da ba zai wuce ashirin da biyar zuwa da shida ba. Ya washe mata baki ya na taba sumar kansa
"Sannu" ta fada mashi ta na juyawa.
"Emm...mu ɗan yi magana mana"
"Ina da miji"
Ta faɗa mashi a takaice ba tare da ta juyo ba. Ta na jin sautin dariyar shi a bayanta.
"Ku yan matan nan haka kuke, daga an yi magana sai ku ce kuna da miji ko ansa maku biki. Duk na saba ji"
Ba ta ce mashi komai ba, ba ta kuma juya ba. Nass ta gani tsaye a in da ta barshi.
"Na gama ta faɗa mashi"
Ya miƙa mata atm idanuwanshi na kan saurayin da har lokacin ya kasa rufe bakin shi.
"Yayanmu ina wuni"
Ya faɗi ganin ta tsaye wurin shi, ya na dan russunawa. Bai kula da rashin ansawar da Nass ya yi ba ya dubeta
"Kalar ja tayi miki kyau sosai..."
Maganar shi ta koma ciki ya bi Nass da abin da ya ke yi da kallo.
Juyawar da za ta yi cikin sakanni biyu ta ji hannuwanshi a kafaɗun ta ya na juyo da ita ta fuskance shi. Ya ɗan ya mutsa fuska ya na daura yatsun shi biyu saman idonta yana yin kamar ya na cire mata a bu.
"Yanzu kin yi kyau"
Ya faɗi har saurayin na jiyowa fuskar shi da dukkan murmushin da zai iya fita. Kafin ta gama tunanin murmushin na miye ta maida martani zuciyarta ta tsaya cak! Jin dumin labban shi a goshinta. Ta damƙe yan yatsun kafarta bugun zucciyarta na ƙaruwa ya na bugawa da sauri.
Ya janye bakin har lokacin da murmushin a fuskarshi. Ya karkata kan shi a hankali ya na kallon yadda saurayin ke barin wurin. Ya sake ta ya na fizgar atm din ya je ya biya. Har lokacin ta na tsaye a wurin da ya barta ta kasa koda motsa yatsanta. Hannunta ta ji ya ja suka bar shagon.
Shi ya bude mata motar ta shiga, ya zagaya ya shige shima ya ja ta da karfi. Kwana ta ga sun yi, sauyin zuciyarta ya fi karfin tsayawa mamakin komawa bayan. Sai da su kayi tafiya ta kusan minti sha biyar kafin suka tsaya wani wurin. Da kallo daya tayi mashi ta gane na siyar da kaya ne da su ke wa kirari da _shiga da wanka_ .(Readymade)

YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!